Juan Vicente Perez: Tsohon da ya fi kowane namiji yawan shekaru a duniya
An tabbatar masa da kambun ne a watan Janairu bayan wanda yake rike da shi ya mutu
Kundin tarihin duniya na Guinness World Records ya tabbatar da Juan Vicente Perez mai shekara 112 daga kasar Venezuela a matsayin mutum mafi yawan shekaru a tsakanin mazajen duniya.
Kundin tarihin ya ce, Perez ya taka wannan matsayi ne bayan mutuwar Spaniard Saturnino da ke rike da matsayin a baya.
An tabbatar da shi ne a matsayin a cikin Fabrairu, kamar yadda Kundin Guinness din ya wallafa a shafinsa na intanet.
Kundin ya ce, “Juan Vicente Perez na cikin koshin lafiya da kuma iya tuna abubuwa. Yana iya tuna yaruntarsa da aurensa da sunayen kannansa da na ’ya’yansa har ma da na jikokinsa.
“Mutum ne mai sha’awar ganin ’yan uwa a kewaye da shi suna hira da ba shi labarai.
An haifi Perez ne a ranar 27 ga Mayun 1909 a yammacin Tachira, inda tun yana dan shekara biyar ya soma taya iyayensa ayyukan gona wajen girbin rake da sauransu.
Bayan da ya girma, Perez ya yi aiki a matsayin mai sasanta rikicin filaye a garin da yake da zama.
Perez ya auri matarsa Ediofina del Rosario Garcia inda suka shafe shekara 60 tare, sun haifi ’ya’ya 11 sannan ta bar duniya a 1997.
Kawo yanzu, yana da jikoki 41 da tattaba kunne 18 sai mabi da su 12.
Dattijon ya fada wa Kundin Guinness cewa, “Aiki tukuru da hutawa a ranakun hutu, kwanciya da wuri da tsoron Allah” na daga cikin abubuwan da suka taimaka masa wajen samun tsawon rai.
Kafin wannan lokaci, Spaniard Saturnino de la Fuente Garcia shi ne mutum mai mafi yawan shekaru a tsakanin maza wanda ya bar duniya yana da shekara 113 a Janairun da ya gabata.
A bangaren mata kuwa, Lucile Randon daga Kasar Faransa ce ta zarce sauran matan duniya yawan shekaru, an haife ta a ranar 11 ga Fabrairun 1904, a bana tana da shekara 118 kenan.