Jus don sanyaya rai a lokacin zafi
Barkanmu da sake saduwa damu a wannan filin namu na girke-girke uwargida. A yau na kawo muku jus din markadaddun ’ya’yn itace ne don sanyaya ran maigida domin zafin da aka shiga na kwanan nan. Abubuwan da za ki bukata ba ma su yawa ba ne. Ga arha, ga kuma biyan bukata.Abubuwan da za a […]
Barkanmu da sake saduwa damu a wannan filin namu na girke-girke uwargida. A yau na kawo muku jus din markadaddun ’ya’yn itace ne don sanyaya ran maigida domin zafin da aka shiga na kwanan nan. Abubuwan da za ki bukata ba ma su yawa ba ne. Ga arha, ga kuma biyan bukata.
Abubuwan da za a bukata
•Abarba
• Lemun zaki
• Gwaba
• Flaba
• Kankana
•Blanda (na markada yayan itatuwa)
•Abin matse lemu (orange skueeze/press)
Hadi
Idan uwargida ta sayo abubuwan da na lissafo za ta ga lallai ba wani abu mai tsada ba ne duka bai fi ta kashe Naira 300 ba.
Ta bare abarba da gwaba da kuma kankana ta ajiyesu a gefe. Sannan sai ta samo lemun zakinta ta yanka shi rabi da wuka kamin ta daura a abin matse lemun zaki (orange press) idan ta samu ruwan lemu da dan dama, sai ta zuba ruwan a cikin blanda da yankakkiyar abarba da kwaba da kuma kankana duk a cikin blanda sai ta markadasu. Bayan ta markada, sai ta tace sannan ta zuba flaba, domin dada wa jus din kamshi. Idan uwargida mai son sukari ce, sai ta zuba siga. Amma babu sukari ya fi dadi. Sai a sanya a firiji domin ya yi sanyi kafin a zuba wa maigida a kofin gilashi domin sanyaya masa zuciya!