Juventus ta dauki matakin ladabtar da Paul Pogba
An yanke shawarar yin wannan wasa ba tare da Pogba ba ne saboda dalilai na rashin da’a.
Juventus ta yi wasa ba tare da dan wasan tsakiyarta Paul Pogba ba, a nasarar da ta samu a kan Freighburg a zagayen kungiyoyi 16 na gasar Europa a daren Alhamis.
Wata majiya daga kungiyar ta ce an yanke shawarar yin wannan wasa ba tare da Pogba ba ne saboda dalilai na rashin da’a.
- Gwamnatin Kaduna za ta rabar da shagunan Kasuwar Barci
- Fitaccen dan kasuwa a Kano Sani Yakasai ya rasu
Dan wasan tsakiyar na Faransa bai buga kusan dukkannin wasannin wannan kaka ba saboda rauni da yake jinya, kuma ba a sanya shi a cikin jerin ’yan wasan da suka fafata a daren Alhamis ba.
Majiyar ta ce kocin Juventus, Massimiliano Allegri, ya dauki wannan mataki ne sakamakon makara da dan wasan mai shekaru 29 ya yi na zuwa wani taron da tawagar ta yi a Yammacin Laraba.
A makon da ya gabata ne Pogba ya buga wa Juventus wasan farko tun da ya yi mata kome daga Manchester United a kakar da ta gabata, kuma ya shigo ne bayan hutun rabin lokaci a wasan da suka yi nasara a kan Torino a ranar Lahadi.