Juventus na dab da dauko Pogba daga Man-U a kyauta
Juventus ta yi wa Pogba tayin Fam jumullar Fam 160,000 a duk mako.
Kungiyar Juventus ta yi wa Real Madrid da Paris Saint-Getmain wajen zawarcin dan wasan tsakiyar kasar Faransa, Paul Pogba, a kyauta daga Manchester United.
Juventus, ta ce tana da kwarin gwiwar dawowar dan wasan wurinta, saboda tayi mai gwabi da ta yi wa dan wasan, wanda kwantaraginsa a Manchester United ke karewa a wannan kakar.
- Wasan kawance: NFF ta bayyana ’yan wasa 30 da za su taka wa Najeriya leda
- Ministan Buhari ya ajiye mukaminsa saboda takarar Shugaban Kasa
Idan sun daidaita da kungiyar da ke kasar Italiya, karo na biyu ke nan da dan wasan mai shekara 29 zai murza mata leda.
Sai dai kuma Paris Saint-Germain ta yi wa dan wasan goron gayyata, a yayin da ita ma Real Madrid ke duba yiwuwar dauko shi.
Tuni dai Juventus ta yi wa Pogba tayin Fam miliyan takwas a shekara – wato, jumullar Fam 160,000 a kowane mako, ga kuma sauran hakkoki masu tsoka.
Hakan ne ya mayar kudaden albashi da sauran hakkoki da zai samu a Juventus zai sanya shi cikin mafiya tsoka a harkokin tamola.
Kungiyar tana hasashen tauraronsa zai kara haskawa a yayin da Paulo Dybala da kuma Giorgio Chiellini ke shirin barin ta, duk kuwa da cewa ta sanya hannu da Dušan Vlahović daga Fiorentina a kan Fam miliyan 62 daga watan Janairu.
Kungiyar na son ganin dawowar Pogba ya farfado da ’yan wasanta da shi kansa, ya zama daga cikin manyan ’yan wansan tsakiya a duniya, duk da kalubalen da ya fuskanta a shekara shida da ya shafe a Manchester United.
Pogba ya fara taka leda ne a Juventsu a shekarar 2012 kafin a 2016 ya koma Manchester United a kan Fam miliyan 89.
Yanzu kuma kungiyar ta kasar Italiya na shirin dauko shi daga Manchester United a kyauta bayan kammala kwantaraginsa a can.