Juyin juya-hali daga Allah babu hayaniya ba zubar da jini (1)
Wannan gwamnati wata rahama ce daga Allah ga duk wadanda aka zalunta, aka yi mana satar arzikin kasa har da mutane, ake ta kashe wa iyaye da iyalai ’yan uwansu. Ba ta ’yan Jari-Hujja, azzalumai, barayi, fajirai, fasikai, matsafa, ’yan kungiyar asiri ba ce. Mun yi gangamin samar da ita ne, mu, da aka zalunta […]
Wannan gwamnati wata rahama ce daga Allah ga duk wadanda aka zalunta, aka yi mana satar arzikin kasa har da mutane, ake ta kashe wa iyaye da iyalai ’yan uwansu. Ba ta ’yan Jari-Hujja, azzalumai, barayi, fajirai, fasikai, matsafa, ’yan kungiyar asiri ba ce.
Mun yi gangamin samar da ita ne, mu, da aka zalunta tare da azzaluman namu da nufin kashe gobara. Wato dai ba mu yi kyamar kowane irin ruwan da muka yi amfani da shi ba, wajan kashe gobarar, kamar yadda idan Allah Ya tashi taimakon bayinsa hatta makiyansu ma sai su kawo tasu gudunmawa. Yanzu ne za mu nemi ruwa mai tsarki, mu tsarkake komai da komai. Saboda haka nake kira ga dukkan wadanda abin ya shafa, musamman ’yan uwana talakawa na ko’ina a fadin Najeriya kowa ya tsarkake imaninsa da Allah da Ya yi mana gata, mu gode maSa, mu yi shirin yin gangamin da za mu iya kawar da duk ’yan Majalisar Dattijai da na Wakilai gurbatattu, masu yunkurin yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zagon kasa ko tsige shi, saboda sun ji Amurka da Turai sun yi masa alkawarin ba shi sunayen duk wasu barayin gwamnatin Najeriya da ’yan kungiyar asiri masu kashe mutane. Wadanda za ta yiwu akwai irinsu ko ma su ne mafiya yawa a majalisun biyu. Ga miyagun tsofaffin shugabannin da suke yin amfani da su. Tilas ne Shugaban kasa Buhari ya yi garanbawul ga dukkan jami’an tsaro da ma’aikatan shari’a (alkalai da na EFCC da ICPC da ’yan sanda…… Shugaban kasa Muhammadu Buhari gare ka!
Idan ba Allah ba wa zai yi mana wannan aiki?
Ga shi dai Allah Ya karbi addu’o’in bayinSa da aka zalunta, Ya shigo lamarin, har an sami CANJI na shugabancin kasa. Saura da me?
Ya rage ga mu mabiya, mu gode wa Allah, mu tsarkake halayenmu, mu kaurace wa zinace-zinace da tauye ma’auni da karya alkawari da kin bayar da zakka da kin yin shari’a da littafin Allah Mai girma. Mu yaki duk wasu nau’o’i na zalunci da tsafi da sata da cin rashawa da cin hanci. Kasancewar wadannan halaye sun yi katutu a cikin zukatan mafi yawan mutane, har da sarakuna da malaman addini da attajirai, musamman ’yan majalisa na tarayya da jihohi. Saboda haka a tashi tsaye wajen jawo hankulan masu hankali musamman talakawa wadanda ake yin dandazo a kansu, babban aikin da yake gabanmu shi ne tabbatar da tsaron rayuwar shugaban namu da lafiyarsa daga kowane irin makirci na makiya da munafukai.
Musamman ’yan majalisar tarayya da suka ginu a kan rashawa da cin hanci daga shugabannin baya, wadanda za a iya yin amfani da su wajen yunkurin tsige Shugaban kasar da ba zai ba su cin hanci ba, ba zai yarda su yi sata ba. A wannan gabar ne haduwar kanmu da jajircewarmu ke da matukar muhimmanci ta yadda duk wani dan majalisa da ya nemi a ba shi cin hanci kafin ya amince da wani kudiri na Shugaban kasa, ko wasu miyagun shugabanni suka nemi su yi amfani da shi, wajen yunkurin tsige Shugaban kasa, mu ga duk irin wadannan ’yan majalisa an dawo da su gida. Wato a tsige su, maimakon a bar su su tsige Shugaban kasa a koma gidan jiya.
Kowa ya san Cif Olusegun Obasanjo sai da ya aikata laifuffukan tsigewa har 125 amma aka kasa tsige shi, saboda cin hanci da rashawa, maimakon su tsige Shugaban kasar sai shi ne ya tsige shugaban majalisar wakilai da na majalisar dattijai. Haka shi ma Jonathan duk abin da ya yi ta faruwa na rashin tsaron rayuka da dukiya da lafiya da mutunci da na addini, maimakon su dauki matakin da ya kamata a kansa, sai shi ne ya rika tozarta su, har matarsa take kiran ’yan Arewa ’ya’yan shegu. Allah ne kadai ya san dubban rayukan da aka salwantar a masallatai da coci-coci da kasuwanni da makarantu da tashoshin mota, ga mata da kananan yara wadanda aka sace ba iyaka, bayan biliyoyin Dalar Amurka na man fetur da aka sace!
Kusan fiye da 70 cikin 100 na ’yan majalisar tarayya da aka kayar da su a zaben fidd-gwani maimakon tunda sun san ba za su koma ba, su dauki matakan shari’a a kan Shugaba Jonathan, sai suka fi so a yi ta dage zabe domin su yi ta zama a haramtacce lokaci a majalisar tare da Jonathan. Duk kashe-kashen da ake ta yi mana, bai dame su ba, dama satar da ake yi mana tare suke rabawa.To yanzu labari ya sha bamban.Ko duk ’yan majalisar jam’iyyarsu daya da Shugaban kasa, ba abin yarda ba ne har sai mun ga kowa ya kai bantensa. Domin mun sha ganin zababbun da suka rika canjawa daga jam’iyyar da aka zabe su zuwa wata, tun daga ’yan majalisar tarayya zuwa gwamnoni da Mataimakin Shugaban kasa. Har ta kai ga Shugaban kasa da ya yi shekara takwas yana mulki yau ya fita daga jam’iyyar da ta zabe shi. Sai mu yi hattara, a kan kudi babu abin da wasu ba za su yi ba!
Kada mu manta, kusan duk wanda aka zaba a 1999 tsarin sojoji ne; su Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdussalami Abubakar da ire-irensu. Sai yaransu da suka daddasa a jihohi a matsayin gwamnoni kamar yadda suka dauko Janar Obasanjo daga kurkuku suka kakaba mana a matsayin Shugaban kasa domin biyan bukatar kansu, wanda hatta dan uwansa Olu Falae da suka yi takara tare, sai da ya gargadi ’yan Najeriya kan kada a kuskura a rantsar da Obasanjo a matsayin Shugaban kasa, (kuma Shugaban Sojoji Najeriya), bisa zargin dan kungiyar asiri ne. Amma aka rantsar da shi a hakan, kuma su da suka kakaba mana shi bai bar su ba, bayan bukatar tasu ba ta biya ba, sai da ya kwace da yawa daga dukiyar da suka wawashe mana.
Ga kudin wutar lantarki Dala biliyan 16 da ya kwasa babu wutar, suka kyale shi, saboda tsoron kada ya daure su, a kan barnar da suka yi daga 1979 da ya ba da mulki zuwa 1999 da ya dawo mulkin. Duk abubuwan da ya bari sun kwashe har sun ciwo bashi na fiye da Dala biliyan 30. Sun rusa darajar Naira, sun kashe noma da kiwo da masana’antu da bankuna, suna fitar da gurbataccen mai ba sa shigo da kudin asusun gwamnati (CBN), ga rarar kudin mai ta yakin Tekun Fasha Dala biliyan 12.2 (Pius Okigbo Pannel) da Asusun Waje. Irina da muka fafata da su IBB da Sani Abacha aka rika tsare mu ana fesa mana tiyagas a ido, ana dukanmu da bulala tamkar mu ne barayin ba su ba. Mun zame musu alakakai, sun rasa yadda za su yi da mu, ga shi tusa ta kare wa bodari