Juyin mulki 9 cikin shekaru 3 a Afirka

A shekara guda an yi juyin mulki uku; mutum guda ya jagoranci biyu wata 9 a Mali; a Burkina Faso sojoji sun yi wa juna juyin mulki cikin a wata tara.

Juyin mulki 9 cikin shekaru 3 a Afirka

An sabunta 31 ga Agusta, 2023

Daga shekarar 2020 zuwa yanzu, karo na tara ke nan sojoji na yin juyin mulki a kasashen Afirka, inda aka yi na baya-bayan nan a kasar Gabon.

Daga cikinsu, akwai mutum guda da ya jagoranci juyin mulki sau biyu a cikin wata tara a Mali; a Burkina Faso kuma sojoji sun yi wa juna juyin mulki sau biyu a wata tara.

Juyin mulki da aka yi a baya-bayan nan ya mayar da hannun agogo baya a nahiyar, inda kafin shekarar 2020 ta yi bankwana daga matsalar da a wasu lokuta har da zubar da jina.

Kwararru na bayyana karuwar ayyukan ta’addanci da cin hanci a matsayin silar juyin mulki a kasashen na yammaci da tsakiyar Afrika, inda aka yi bankwana da hakan kafin 2020.

Jerin Juyin Mulkin Afirka (2020-2023)

Ga jerin juyin  mulki 9 da aka yi a Afirka daga 2020 zuwa yanzu:

  1. Mali – Agusta 2020: Kanar Assimi Goita ya hamabare Ibrahim Boubacar Keita ya nada Kanar Bah Ndaw.
  2. Mali – Mayu 2021: Kanar Assimi ya kifar da Kanar Bar ya nada kansa shugaban rikon kwarya.
  3. Sudan – Oktoba 2021 – Janar Abdel Fattah al-Burhan ya hambarar da gwamnati kan rikicin ’yan siyasa.
  4. Burkina Faso – Janairu 2022: Laftanar-Kanar Paul-Henri Damiba ja hambarar da Roch Kabore.
  5. Burkina Faso – Satumba 2022: Kyaftin Ibrahim Traore ya hambarar da Laftanar-Kanar Damiba.
  6. Chad – Janairu 2021: Mahamat Idriss Deby ya karbi mulki bayan rasuwar mahaifinsa.
  7. Guinea – Satumban 2021: Kanar Mamady Doumbouya ya hamabrar Alpha Conde.
  8. Nijar – Yuli 2023: Janar Chiani ya hambarar da Mohamed Bazoum.
  9. Gabon –  Agusta 2023: Har yazu ba a bayyana shugaban sojin ba.

Rainon Faransa

Daukacin kasashen da aka yi juyin mulkin rainon Faransa ne, wadda ke taimaka wa wasu daga cikinsu wajen yakar ta’adanci a yankin Sahel.

Sai dai kuma masu juyin mulki a kasashen yankin na zargin ta da hannu a ayyukan ta’addanci, da kuma mayar da shugabannin farar hula ’yan amshin shatanta.

A kan haka ne gwamnatocin sojin ke korar dakarun Faransa daga kasarsu, inda suke zargin tsohuwar uwar gijiyar kasashen nasu na mulkin mallaka na zamani, da kwashe arzikin kasashensu.

Faransa dai na daga cikin manyan masu neman ganin an dawo da mulkin farar hula a kasahen da aka yi juyin mulkin.

Kasashen Afirka da ke karkashin mulkin soji

1- Gabon

An wayi garin Laraba 30 ga watan Agusta da labarin cewa sojojin Gabon sun hambarar da Shugaba Ali Bongo Odimba, sa’o’i kadan, suka soke zaben tare da rufe iyakokin kasar, suka kuma rushe duk masu rike da mukaman siyasa.

Sojojin sun kifar da gwamnatinsa ne sa’o’i kadan ban ya lashe zabe domin fara wa’adinsa na uku a karamar kasar mai arzikin mai da koko da sauransu.

2- Nijar

Kafin nan a ranar 26 ga watan Yuli Sojojin Nijar suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki, lamarin da har zuwa yanzu da takwarorinsu an Gabon suka bi sahu ake ake ci gaba da kai ruwa rana wajen ganin sun saki Bazoum, sun mika masa kujerarsa, su koma bariki.

Masu juyin mulkin na Nijar Nijar sun yi tayin mulkin rikon kwarya na shekaru uku kafin su mika wa farar hula, amma kungiyar ECOWAS ta sa kafa ta shure tayin nasu.

3- Burkina Faso

Kafin Nijar sai da sojoji suka yi juyin mulki sau biyu a Burkina Faso inda a watan Janairun 2022 Laftanar-Kanar Paul-Henri Damiba ja jagoranci kifar da Gwamnatin Roch Kabore kan zargin gaza yakar ta’addancin da ya addabi kasar.

Bayan wata tara a watan Satumba, Kyaftin Ibrahim Traore ya yi masa juyin mulki ya kwace iko da kasar.

4- Sudan

A ranar 25 ga Octoban 2021, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ja jagoranci sojoji suka kwace gwamnati a juyin mulkin da suka yi bisa zargin rikicin ’yan siyasa da ya jefa kasar cikin rikici.

5- Guinea

A watan Satumban 2021 Kanar Mamady Doumbouya ya jagoranci sojoji suka yi wa Shugaban Alpha Code na kasar Guinea juyin mulki.

Sojojin sun hambarar da Alpha Conde ne shekara guda bayan ya sauya kundin tsarin mulkin kasar domin ba shi ikon kara wa’adin mulki.

6- Chadi

A watan Afrilun 2021 sojoji suka ci gaba da mulki a kasar Chadi bayan rasuwa Shugaba Idriss Deby Itno a fagen yaki da ’yan tawaye.

Bayan rasuwarsa ne dansa, Janar Mahamat Idriss Deby ya karbi ragamar shugabancin kasar karkashin mulkin rikon kwarya, wanda wasu ke gani a matsayin juyin mulki a cikin ruwan sanyi.

7- Mali

Juyin mulki na farko a daga shekarar 2020 shi ne wanda sojojin Mali suka yi a cikin watan Agusta, inda Kanar Assimi Goita ya kifar da da gwamnatin Shugaban Ibrahim Boubacar Keita.

Sai dai maimakon nada kansa a matsayin shugaba, sai ya mika mulkin kasar ga Kanar Bah Ndaw (mai ritaya) a matsayin shugaban rikon kwarya.

Daga baya Kanar Assimi ya kiar da shi a wani sabon juyin mulkin a watan Mayu 2021, ya nada kansa a matsayin  sabon shugaban rikon kwarya.