Juyin mulki a Thailand: Sojoji sun kama tsohon ministan ilimi
Sojojin da suka karbe iko a kasar Thailand, sun cafke tsohon ministan ilimin kasar bayan ya yi Allah-wadai da matakin gwamnatin sojan da kuma yin kira kan su komo da mulki ga farar hula.Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ce an kama Mista Chaturon Chaseing ne jim kada bayan kammala wani taron manema labarai da […]
Sojojin da suka karbe iko a kasar Thailand, sun cafke tsohon ministan ilimin kasar bayan ya yi Allah-wadai da matakin gwamnatin sojan da kuma yin kira kan su komo da mulki ga farar hula.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ce an kama Mista Chaturon Chaseing ne jim kada bayan kammala wani taron manema labarai da ya kira a ranar Talata, a babban birnin kasar, Bangkok. AP ya kuma ruwaito ministan na cewa “juyin mulki ba dimukradiyya ba ne kuma jama’ar kasar ba za su amincewa da haka ba”. Daga nan kuma ya ce za su zuba ido su ga matakan da dimbin magoya bayan tsohuwar gwamnatin za su dauka.
A ranar Alhamis din makon jiya ne sojoji suka kwace mulki a kasar, inda suka ce za su dawo da doka da oda saboda rikicin siyasar da ya barke a kasar bayan wani hukuncin Kotun Tsarin Mulki da ya tilasta wa Firaministan kasar Yingluck Shinawatra, sauka daga mulki a ranar 7 ga watan nan, soboda laifin amfani da iko ba bisa ka’ida ba.
A ranar Litinin ne, gwamnatin sojin ta samu goyon bayan gidan sarautar kasar. Masana na ganin juyin mulkin da sojojin suka yi ba zai kawo kashen rikicin siyasar kasar ba, wanda ya jefa ta cikin halin rashin tabbas na tsawon watanni. Rikicin ya samo asali ne a shekarar 2006, a lokacin da sojoji suka habarar da gwamnatin Thaksin Shinawatra, wanda yaya ne ga Firaminista Yingluck.