Juyin mulki: Amurka da Faransa na kokarin hada Najeriya da Nijar fada – El-Zakzaky
Ya ce kasashen za su iya kai hari su fake da sunan Najeriya ko Nijar
Jagoran mabiya mazhabar Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya yi zargin cewa kasashen Amurka da Faransa na son yin amfani da halin da ake ciki wajen haddasa rikici tsakanin Najeriya da Nijar.
Ya ce kasashen Turawa za su iya amfani da dakarunsu wajen kai wa Nijar hari a zaci Najeriya ce, ko su kai wa Najeriya hari a yi tunanin Nijar ce.
- Nijar: Za mu dawo da Bazoum ta kowace hanya —Sojojin ECOWAS
- Trump zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara 700 a gidan yari
Tun bayan juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Mohammed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli, kasashen Amurka da Faransa suka bayyan matsayinsu a kai.
Faransa dai ta bukaci a saki hambararren Shugaban Kasar wanda yanzu haka yake hannun sojojin sannan a mayar da su kujerarsa.
Kazalika, ta nuna goyon bayanta ga yunkurin da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) take shirn dauka na matakin soja a kan gwamnatin sojin ta Nijar.
To sai dai da yake wa’azi ga dalibansa daga gidansa da ke Abuja, El-Zakzaky ya ce, “Sau nawa ana juyin mulki a Najeriya? Akwai wanda ya taba zuwa ya tilasta mu mu koma mulkin farar hula? Ban taba jin haka ba. Ta yaya zaka dauki makami ka mamaye kasa da sunan Dimokuradiyya?
“Kuma a bayyane yake wannan ba yakinmu ba ne. Yaki ne tsakanin Amurka da Faransa. Kodayake Nijar ta rufe sararin samaniyarta, amma har yanzu jiragen Faransa na shawagi a kai. Sannan suna da kungiyoyin ‘’yan ta’adda’ wadanda ake kira da Boko Haram. Daga can suke fitowa su kai wa mutane hare-hare sannan su kwashe ma’adina su raba a tsakaninsu.
“Yanzu ina fargabar akwai yiwuwar su yi amfani da irin wadancan ’yan ta’addan wajen kai hari a tsakanin kasashen biyu. Za su iya haddasa rikicin kabilanci tsakanin najeriya da Nijar, ta hanyar fakewa da Bazoum, su sa kabilu su rika yakar juna,” in ji Zakzaky.