Juyin Mulki: Wane ne zai zama sabon Shugaban Nijar?

A daren ranar Laraba ne wasu dakarun sojin kasar suka sanar da hambarar da gwamnatin shugaba Bazoum.

Juyin Mulki: Wane ne zai zama sabon Shugaban Nijar?

Da tsakar daren Laraba ne wasu dakarun sojin Jamhuriyar Nijar suka bayyana karbe shugabancin kasar daga hannun Mohamed Bazoum.

Kazalika dakarun sojin sun bayyana cewa sun kafa Majalisar da za ta kare kasarsu ta gado daga rushewa.

Kakakin sojojin kasar, Manjo Ahmadou Abdrahamane ne, ya yi bayanin ta kafar talabijin din kasar.

Sai dai duk da haka sojojin ba su bayyana ko wane ne shugabansu ko kuma shugaban kasar ba.

Sai dai tun bayan hambarar da gwamnatin kasar, aka shiga halin rashin tabbas kan su wane ne za su zama ‘yan gaba-gaba cikin dakarun sojin da za su ja ragamar shugabancin kasar.

Bayanai dai na cewa Janar Omar Tchani ne, jagoran sojojin da suka hambarar da gwamnatin Nijar.

Janar Tchani shi ne shugaban dakaru masu gadin fadar shugaban kasar a halin yanzu, kuma ya kasance a wannan mukami tun farkon mulki tsohon Shugaban Kasa Muhammadou Issoufou.

Sai dai yayin da ake cikin wannan halin, Ministan Harkokin Wajen Nijar, Hassoumi Massoudou ya wallafa wata sanarwa a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana cewa shi ne ke jagorantar gwamnatin kasar a yanzu.

A gefe guda kuwa, shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), Bola Ahmed Tinubu ya gargadi dakarun sojin da suka hambarar da kasar.

ECOWAS ta lashi takobin tabbatar da mulkin dimokuraddiya a kasar, inda ta fara shirye-shiryen samar da tawagar tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Tun da fari magoya bayan Bazoum sun shiga zanga-zanga da yunkurin juyin mulkin tun a ranar Laraba, lamarin da ya sa sojojin da ke tsare da fadar shugaban kasar suka tarwatsa su.

Da safiyar ranar Alhamis ne kuma masu zanga-zangar suka kone ofishin jam’iyyar PNSD mai mulki a Nijar.

Yanzu haka dai shugabannin duniya na ci gaba da yin Allah-wadai da juyin mulkin da aka yi a Nijar.

Tinubu ya yaba wa NNPCL kan fara aikin Matatar Warri

Masu son Abba ya tsaya da ƙafarsa za su cuce shi – Kwankwaso

Matatar Warri ta fara aiki bayan shekara 9

’Yan sara-suka sun yi wa tela kisan gilla a Jos