Juyin mulkin Syria: Iran ta tuntubi wadanda suka kifar da Al Assad

An kafa tutar ’yan tawayen kasar Syria a ofishin jakadancin kasar da ke Moscow, babban birnin kasar Rasha, inda Shugaba Bashar Al Assad da aka kifar ke zaman makafa

Juyin mulkin Syria: Iran ta tuntubi wadanda suka kifar da Al Assad

Sabuwar tutar kasar Syria mai tauraro uku da ‘yan adawa suka kaddamar.

An kafa tutar ’yan tawayen kasar Syria mai dauke da tauraro uku a ofishin jakadancin kasar da ke Moscow, babban birnin kasar Rasha, inda Shugaba Bashar Al Assad da aka kifar ke zaman makafa, a safiyar Litinin.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Saudiyya ta bayyana goyon bayanta ga yadda aka kare rayukar fararen hula da kawo karshen zubar da jini a Syria, a juyin mulkin da ’yan tawayen da ke samun goyon bayan kasar Turkiyya suka yi wa Bashara Al Assad.

A ranar Lahadi Shugaba Bashar Al Assad da iyalansa suka tsere daga Syria zuwa Moscow ne bayan mayakan ’yan tawayen Syria sun mamaye birnin Damascus, fadar gwamnatinsa a ranar Asabar.

Hambarar da gwamantin Al Assad ba tare da wata turjiya ba, ya kawo karshen kimanin shekara 60 da Zuri’ar Al- Assad suka yi suna mulkin kasar Syria.

Dubban daruruwan ‘yan kasar a cikin gida da kuma kasashen waje, musamman nahiyar Turai da Gabas ta Tsakiya na gudanar da bukukuwan murnar kifar da Shugaba Bashar Al Assad, wanda shi ne na karshe a jerin Zuri’ar Al Assad da suke mulkin kasar tun shekarar 1949.

A halin yanzu gwamnatin kasar Iran ta fara tattaunawa da shugabannin juyin mulkin na Syria da suka kifar da al- Assad bayan yakin basasan shekara 13.

Wani jami’in Iran ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa kasarsa na tattauanawa da masu juyin mulkin ne domin tabbatar da kyakkyawan dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Iran da Rasha sun kasance manyan magoya bayan gwamnatin kasar Syria a karkashin al- Asssad, wadda a yanzu ta koma hannun gwamnatin soji.

Jami’in na Iran ya ce rasa babban abokin kasarsa a Gabas ta Tsakiya, Bashar al Assad, da kuma dawowar Donald Trump mulki a Amurka, ya sa kasar ke ganin dacewar tattaunawa da masu juyin mulkin na Syria.

“Tattauanwar na da muhimmanci domin tabbatar da daidaituwar al’amura da kuma kaucewa zullumin a yankin.”

A halin yanzu, yan tawayen da ke goyon bayan kasar Turkiyya sun karbe ikon garin Manbij da ke Arewacin kasarsu, a cewar wani jami’in Turkiya a safiyar Litinin.

Kungiyar Mayakan Kurdawa ‘Yan Kasar Syria (SDF) da ke samun goyon bayan Amurka ne ke rike da yankin zuwa ranar Asabar inda ake fada tsakaninsu da masu goyon bayan Turkiyya, wadnda a ranar Lahadi suka sanar da kifar da Gwamnatin Al Asssad a birnin Damascus.