Ka kyale ’yan majalisa su zabi wanda suke so ya jagorance su – Dattawan Arewa ga Tinubu

Sun ce kowanne bangare gashin kansa yake ci, bai kamata a yi masa shisshigi ba

Ka kyale ’yan majalisa su zabi wanda suke so ya jagorance su – Dattawan Arewa ga Tinubu

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta bukaci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya girmama doka ya kyale ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa su zabi wadanda suke so su shugabance su.

A cewar kungiyar, bangaren majalisa waje ne mai zaman kansa, don haka ya zama wajibi bangaren zartarwa ya guji yi masa shisshigi wajen zaben shugabancinsa.

Daraktan Yada Labarai na kungiyar, Dokta Hakeem Baba-Ahmed ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Kaduna ranar Litinin.

Dokta Hakeem dai na martani ne ga kalaman Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima kan batun.

Aminiya ta rawaito yadda Shettiman ya tara Sanatoci yana cewa komai lalacewar Kirita dan Kudu ya fi cancanta ya jagoranci Majalisar Dattawa a kan Musulmi dan Arewa, komai cancantarsa, kodayake daga bisani ya ce canza masa kalaman aka yi.

To sai dai Dokta Hakeem ya soki kalaman na Shettima, inda ya ce abin takaici ne, kasancewarsa Musulmin da ake girmamawa, kuma dan siyasa.

Ya ce a lokuta da dama, kungiyar ta sha rokar Tinubu da ya kyale doka ta yi halinta kyale ’yan majalisar su zabi wanda suke so ya jagorance su, ba wai a kakaba musu wadanda ba sa so ba.

“Kungiyar Dattawan Arewa a lokuta daban-daban, ta shawarci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta girmama ra’ayoyin ’yan majalisar don tabbatar da tsari da yin abu a tsari,” in ji Dokta Hakeem.

’Yan bindiga sun sace Farfesa, sun nemi N10m kuɗin fansa

Za a ɗauke wutar lantarki na tsawon mako 2 a Abuja

Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza

Sakataren Gwamnatin Ondo ya rasu bayan yin hatsarin mota