Kabeji mai nama

Barkanmu da warhaka uwargida tare da fatan ana lafiya. Yaya yara? Allah Ya bamu ikon tarbiyantar da su yadda yakamata.  A yau na kawo muku yadda ake girka kabeji mai nikakken nama a cikinsa. Akwai abubuwan karyawa da dama amma yawaita girka abinci iri daya na ginsan yara da kuma maigida. A kullum mutum yana […]

Kabeji mai nama

Barkanmu da warhaka uwargida tare da fatan ana lafiya. Yaya yara? Allah Ya bamu ikon tarbiyantar da su yadda yakamata.  A yau na kawo muku yadda ake girka kabeji mai nikakken nama a cikinsa. Akwai abubuwan karyawa da dama amma yawaita girka abinci iri daya na ginsan yara da kuma maigida. A kullum mutum yana son cin sabon abu. Don haka dole ne mata a dage wajen koyan nau’ukan girke-girke domin kayatar da abincin da ake dafawa a gida.

Abubuwan da ake bukata

Nikakken nama

Kabeji

Attarugu

Koren tattasai

Albasa

Magi

Karas

Kori

Citta

Tafarnuwa

Man gyada

Hadi

A wanke nama sannan a markada shi a na’urar nika nama a ajiye a gefe. A dora tukunya a wuta da gishiri kadan sannan a samu kabeji a bare shi manya-manya a tafasa da gishiri kadan na tsawon mintuna biyar. Sannan a tsame a ajiye a gefe.

A dora tukunya a zuba man gyada kadan sannan a zuba albasa da nikakken nama a zuba magi da kori da garin citta da tafarnuwa da jajjagen attarugu da yankakken koren tattasai ayi ta gaurayawa har sai naman ya  soyu sannan  a kwashe.

A samu kabejin da aka tafasa sannan a shimfida shi kamar tabarma sannan a debo hadin nama a zuba a ciki sannan ayi masa nadin tabarma a tottoshe gefe-gefen.

Sannan a dora tukunya a wuta a zuba man gyada kadan ba mai yawa ba, sannan a zuba wannan ninkin kabejin a cikin man a soya sama-sama sannan a kwashe.

Za a iya cin wannan hadin kabejin da shayi mai zafi da safe a matsayin abun karyawa.