Kaberuka ya karbi Kambin Gwarzon Afrika na Daily Trust

Shekaranjiya Laraba kamfanin Media Trust Limited, mai mawallafa jaridun Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust da Aminiya ya karrama Shugaban Bankin Bunkasa Afirka, Donald Kaberuka, yayin da ya mika masa kambin Gwarzon Afrika na bana.Da yake bayyana dalilin da ya sanya aka zabi kwararren masanin al’amuran tsimi da tanadin a matsayin wanda ya […]

Kaberuka ya karbi Kambin Gwarzon Afrika na Daily Trust

Shekaranjiya Laraba kamfanin Media Trust Limited, mai mawallafa jaridun Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust da Aminiya ya karrama Shugaban Bankin Bunkasa Afirka, Donald Kaberuka, yayin da ya mika masa kambin Gwarzon Afrika na bana.
Da yake bayyana dalilin da ya sanya aka zabi kwararren masanin al’amuran tsimi da tanadin a matsayin wanda ya cancanci kambin na bana, Shugaban Kwamitin Karramawar, tsohon Shugaban kasar Tanzaniya, Dokta Salim Ahmed Salim ya ce an zabi Kaberuka ne saboda la’akari da kwarewarsa wajen shigo da sababbin tsare-tsaren bunkasa tattalin arzikin Nahiyar Afirka, wanda haka ya sanya har aka bullo da ‘Asusun kasashen Afrika 50’ domin bunkasawa da gina Afirka.
Kwamitin karramawar ya samu nasarar zaben Kaberuka ne bayan dubawa da tantance fitattu kuma sanannun ’yan Afirka da suka yi fice a fagegen hidimar al’umma daban-daban. Cikin masana da fitattu ’yan Afirka da aka tantance a bana, sun hada da Ridha Khadher, dan kasar Tunisiya, mazaunin kasar Faransa, wanda ya shahara a sana’ar biredi. Haka kuma akwai shahararriyar marubuciya, ’yar kasar Zimbabwe, Nobiolet Bulawayo, wacce ta rubuta littafin kirkirarren labari mai taken ‘We Need New Names’, wanda yana daya daga cikin littattafan da suka yi tashe a bara. Sannan akwai rikakken dan kasuwa kuma attajiri, Alhaji Aliko dangote, wanda ya shahara wajen kasuwanci da tafiyar da kamfanoni daban-daban a Afirka.
Shi dai wannan kambi ya kunshi har da tsabar Dala 50,000 (wanda bankin United Bank for Africa Plc. yake daukar nauyi), an mika shi ne ga gwarzon, a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar a otel din Transcorp Hilton Abuja, daren Larabar.
Shi dai Donald Kaberuka, wanda a halin yanzu shi ne Shugaban Bankin Bunkasa Afirka, an haife shi a ranar 5 ga Oktoba, 1951, a garin Byumba na kasar Ruwanda. Ya yi karatunsa na zamani a kasashen Tanzaniya da Turai, inda ya samu digirin digirgir daga Jami’ar Glasgow. Ya yi aiki a bankuna da cibiyoyin kasuwanci a sassan duniya daban-daban, har na tsawon sama da shekara goma.
A 1997 aka nada shi mukamin Ministan Kudi da Tsare-Tsare na kasar Ruwanda, inda ya kwashe shekara takwas a mukamin. A yayin da yake kan mukamin na Minista, an samu tabbacin cewa ya taimaka sosai wajen daidaita tattalin arzikin kasar Ruwanda, bayan da kasar ta yi fama da yakin basasa a 1994. A 2005 ne aka nada shi mukamin Shugaban Bankin Bunkasa Afirka (AfDB), inda ya fara aiki tun daga Satumba na shekarar har zuwa yanzu. Shi ne shugaba na bakwai da ya shugabanci bankin.
Wannan kambi da ya amsa na Gwarzon Afirka, an kirkiro shi ne tun a 2008 domin karrama shahararru kuma fitattun ’yan Afrika da suke yi wa nahiyar hidima a fannonin da suka kware. Ana zaben ne bayan al’umma ’yan Afirka sun gabatar da sunayen gwanayen nasu, wadanda a cikinsu ne ake tantacewa sannan a zabi gwarzo guda da aka ga ya fi sauran yi wa al’ummar Afirka.
Wasu gwarazan Afirka da suka taba lashe wannan kambi a baya sun hada da Dokta Denis Mukwege na kasar Jamhuriyar Kongo (2008), Dokta Tajudeen Abdul-Raheem na Najeriya (2009), Mista Danny Jordaan na Afirka ta Kudu (2010), Mai Shari’a, Uwargida Fatimata Bazaye ta Nijar (2011) da kuma Tsohon Shugaban kasar Afirka Ta Kudu, Mista Thabo Mbeki (2012).