kabilanci ne zai kai kasar nan kasa
Kamar yadda ba a iya raba hanta da jini, haka nan ma ba a iya raba siyasar Najeriya da kabilanci. Wanda duk ke bisa kujerar mulki zai nemi yin alfasha don ya dadada ko ya taimaki jinsinsa, haka nan su ma ‘yan kabilar wanda ke rike da wani mukami za su yi ta goyon bayansa […]
Kamar yadda ba a iya raba hanta da jini, haka nan ma ba a iya raba siyasar Najeriya da kabilanci. Wanda duk ke bisa kujerar mulki zai nemi yin alfasha don ya dadada ko ya taimaki jinsinsa, haka nan su ma ‘yan kabilar wanda ke rike da wani mukami za su yi ta goyon bayansa ido rufe. Irin halin da Uwargidar Shugaba Goodluck Jonathan, Madam, ko kuma a ce Kwari Patience (uwargida) ta yi ta nunawa ke nan a ‘yan kwanakin nan, tana kokarin kare mijinta ala-kulli-halin daga yarfen da ‘yan adawa ke yi wa gwamnatinsa cewa ya dai ji kunya tun da ya kasa tabuka katabus wajen ceto ’yan matan makarantar Chibok sama da 200 da aka sace.
Sa’ilin da kururuwar satar ‘yanmatan suka cika gida da waje, sai kungiyoyi daban-daban suka yi ta bin kwararo-kwararo da lungunan kasar nan, suna nuna rashin jin dadinsu, amma maimakon Kwari Patience ta tausaya masu, ko ta fito, ta jagorance su, sai ta nuna cewa abin da suke yi bai dace ba, domin kuwa suna kokarin shafawa mijinta kashin kaji ne. Cikin dan kankanen lokaci sai ga wasu fitattun ‘yan kabilarta ta Ibo sun fara fitowa fili suna sukar lamirin masu nuna juyayinsu game da satar ‘yanmatan. Wata tsohuwar Minista, Misis Kema Chikwe karyata batun sacewar ta yi, domin a cewarta kaharu ne kawai don a bata sunan mijin Kwari Patience. Haka nan ma wata mashahuriyar mawakiya, Onyeka Onwenu ta nemi muzanta hujjojin da shugaban makarantar ‘yanmatan ta bayar game da sace su don dai kawai ta karyata ta.
Daga karshe shi ma mijin Kwarin Najeriya ya amince cewa so dai ake yi a yi amfani da batun sace ’yanmatan don a durkusar da gwamnatinsa, har ma ya fito fili, firifalo ya ce a daina kiran sunansa a matsayin wanda ya kasa ceto ‘yanmatan, maimakon haka a tafi can inda aka sace ‘yanmatan a yi ta kururuwa don a maido su.
A takaice dai ana iya cewa Kwarin Najeriya ta yi nasarar hure kunnuwan ’yanuwanta Ibo, wadanda suka amince cewa batun satar ’yanmatan Chibok dai gaibu ce da aka kitsa, musamman don a yi wa mijinta cin-fuska.
Shi ya sa babu wanda ya yi mamaki ganin yadda Kwari Patience ta dukufa wajen gaggauta kafa wata kungiya ta mata zalla don a muzanta ’yanuwa da iyayen ’yanmatan da kuma masu jajanta musu, wadanda ke zanga-zangar lumana don nuna damuwarsu game da halin da ’yanmatan da aka sace ke ciki. A karshe sai da kungiyar Kwari Patience ta yi fito-na-fito da ta wadancan matan, aka fafare su daga inda suka yi dandazo, aka kuma kakkarya musu kayayyaki. Kai, daga karshe ma sai da Kwari Patience ta yi amfani da Kwamishinan ‘yan sandan yankin Abuja, Mista Mbu, wanda ya kasance dan kabilarta don haramta ci gaba da yin zanga-zangar lumana game da ‘yan matan Chibok a garin Abuja, don mijinta ya huta da zargin lusaranci da ake yi masa. Wannan ba farau ba ga Kwari Patience, domin ta yi amfani da wannan dansandan wajen takura wa Gwamna Rotimi na Jihar Ribas, sa’ilin da ya sanya karfar wando daya da mijinta.
To amma al’amarin Kwari Patience da maigida Jonathan tamkar kwaryar sama ce da ta kasa. Zamansa da uwargidansa ya sanya ya koyi manufofi irin na ‘yanuwanta, watau kabilanci da son kai, abubuwan da suka kara tsananta rashawa da cin hanci da kuma haddasa rashin zaman lafiya da lumana a kasar nan. Ai kowa na sane da yadda Ministar Kudi, Misis Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa an kashe Naira miliyan 130 akan harkar tsaro a cikin watanni hudu, baicin wasu dubban daruruwan miliyoyin da aka yi ta warewa a kasafin kudaden shekarun da suka gabata saboda haka, amma ba su biya bukatu ba, ba a kuma binciki wannan al’amarin ba, domin kusan manyan kwamandojin soji na wancan lokacin duk ‘yan kabilar Kwari Patience ne. Shi ya sa Shugaban ke kawar da kai daga dukkan al’amuran da ya shafe su, don gudun bacin ranta. Ai an ce son zuciya bacinta, ga shi nan kuma Shugaba Jonathan na ta gamuwa da abubuwan takaici dangane da haka. To ai shi ma Shugaba
Jonathan ba kanwar lasa ne ba wajen nuna halayyar da ta jibanci kabilanci, domin kuwa ga shi nan a zahiri ya ki daukar matakan tuhumar Ministar albarkatun man fetur, Misis Diezani Allison-Madueke bisa zargin almubazzaranci da wadaka da dukiyar talakawa da take yi. Hasali ma sai kara tarairayarta yake yi kamar kwai, bai son ku kuda ya taba ta balle tashin hankali saboda tonon asiri.
Bisa ga dukkan alamu dai ‘yan uwan Jonathan, a karkashin shugabancin Cif Edwin Clark sun gurgunta shi, bayan sun dora shi bisa turbar kabilanci, ga shi nan kuma yana bin ta tiryan-tiryan, ba kuma zai ankara cewa suna son kai shi ne su baro ba. kabilanci ya ba su damar satar bakin man dasar nan ba kakkautawa, ba kuma wanda ya isa ya hana. Ta ko ina aka duba za a fahimci cewa kabilance ne ummul-haba’isin masifu da matsalolin da ke addabar kasar nan, ‘yan siyasa ne ke kara karfafa shi da gangan. Allah ya sawwake.