kabilun Tibi da Jukun na shirin shiga fagen-daga a Jihar Taraba

’Yan kabilar Tibi da Jukun a Jihar Taraba na shirin shiga fagen-daga sakamakon kisan gillar da kowane bangare ke zargin ana yi wa ’yan kabilarsa.Bayanan da wakilinmu ya samu a yankunan kananan hukumomin Donga da Wukari da Takum a Jihar Taraba da kuma wani sashi na karamar Hukumar Katsina-Ala da ke Jihar Binuwai sun nuna […]

kabilun Tibi da Jukun na shirin shiga fagen-daga a Jihar Taraba
kabilun Tibi da Jukun na shirin shiga fagen-daga a Jihar Taraba

’Yan kabilar Tibi da Jukun a Jihar Taraba na shirin shiga fagen-daga sakamakon kisan gillar da kowane bangare ke zargin ana yi wa ’yan kabilarsa.
Bayanan da wakilinmu ya samu a yankunan kananan hukumomin Donga da Wukari da Takum a Jihar Taraba da kuma wani sashi na karamar Hukumar Katsina-Ala da ke Jihar Binuwai sun nuna cewa a ’yan kwanakin nan an kashe jama’a masu yawa da kabilun biyu ke zargin junansu da wannan aika-aika.
Binciken Aminiya ya nuna cewa, hanyar Takum zuwa garin Katsina-Ala da ke Jihar Binuwai ta zama inda ’ya’yan kabilun biyu ke farautar junansu suna kashewa kusan a kullum wanda hakan ya sa jama’a suka kaurace wa hanyar don tsira da ransu.
A wannan yanki kusan gidan kowa akwai bindiga wanda hakan ya sa kisan kai da rikice-rikice suka zama ruwan dare, wanda hakan ya sa bin daukacin hanyoyin da ke yankin ya zama hadari.
Sakamakon yawan aika-aikar da ke aukuwa a yankin ne, shugaban al’ummar Tibi a Jihar Taraba Mista James Nnungwai ya kira taron manema labarai a garin Jalingo inda ya nuna damawarsa dagane da wannan lamari.
Ya ce abin bacin rai ne ganin yadda kabilun biyu ke ta hallaka junansu, inda ya ce in ba a yi taka-tsantsan ba zai iya haifar da mummunan tashin hankali.
Mista Nnungwai ya ta’allaka matsalar ga matasan bangarorin, inda ya ce su ke gudanar da kashe-kashen da barnata dukiyoyi jama’a a yankunansu.
Sai ya yi kira ga Gwamnan Jihar Taraba Mista Darius Ishaku ya hada kai da Gwamnan Jihar Binuwai Mista Samuel Ortom don shawo kan wannan lamari.
Ya ce zaman lafiya shi ne zai kawo ci gaba da bunkasar jihohin biyu da kasa baki daya, inda ya ce akwai bukatar gwamnatocin jihohin biyu sun tashi tsaye wajen kawo karshen yawan tashin hankalin da ke faruwa a tsakanin kabilan biyu a kan iyakokin jihohin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba, DSP Joseph Kwaji da wakilinmu ya tuntube shi kan wannan batu ya ce ba ya da masaniya amma zai bincika.