Kabiru Fagge: Ta’aziyyar tsohon ma’aikacin Muryar Amurka

Fitaccen dan jarida kuma tsohon ma’aicin Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) Kabiru Fagge, ya rasu a sakamakon rashin lafiya.

Kabiru Fagge: Ta’aziyyar tsohon ma’aikacin Muryar Amurka

Fitaccen dan jarida kuma tsohon ma’aikacin Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) Kabiru Fagge, ya rasu a sakamakon rashin lafiya.

Kabiru Fagge mai shekaru 77, ya rasu ne ranar Juma’a a kasar Amurka inda ya shafe shekaru 25 a VOA.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba da irin gudunmawar marigayin wajen gina kasa da wayar da kan jama’a da kuma bayar da shawarwarin ilimi ta hanyar fitaccen shirin ilimi na mako-mako da ya kafa.

Kakakin shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya ambato Tinubu na cewa “Kabiru Fagge ya fara sha’awar hidimanta wa bil’adama ta hanyar aikin jarida ne tun a lokacin da yake aikin na wucin gadi.

“Muna godiya da ayyukansa da kuma kasancewarsa jakadan Najeriya nagari a idon duniya.”

Shugaban kasan ya jajanta wa iyalan mamacin, gwamnati, da al’ummar jihar Kano, da kuma ’yan jarida bisa wannan rashi.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe