Kabiru Gaya ya fadi zabe bayan shekara 16 a Majalisa
Kawu Sumaila na Jam’iyyar NNPP ya lashe 10 daga cikin kananan hukumomi 16 da ke Kano ta Kudu
Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Kabiru Ibrahim Gaya, da ke neman tazarce bayan shekara 16 a Majalisar Dattawa, ya sha kaye a hannun dan Majalisar Wakilai, Kawu Sumaila.
Kawu Sumaila na Jam’iyyar NNPP ya yi nasara ne bayan ya samu nasara a 10 daga cikin kananan hukumomi 16 da ke Kano ta Kudu.
- Yau INEC za ta ci gaba da karbar sakamakon zaben shugaban kasa a Abuja
- Fasinjan jirgin kasan Abuja-Kaduna ya ci zaben Majalisar Tarayya
Kawu Sumaila ya zama gwarzo ne bayan ya samu kuri’u 18,419 a yayin da Sanata Kabiru Gaya na Jam’iyyar APC kuma ya samu kuri’u 10,079.
Wanda ya zo na uku, dan takarar Jam’iyyar PDP, ya samu kuri’a 747.
A shekarar 2007 Kabiru Gaya, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne, ya fara zama Sanata, kuma tun daga lokacin yake Majalisar Dattawa.