Kachako!

Wani Bafulatini ne ya hau mota daga cikin Kano zuwa wani kauye. Ana cikin tafiya sai yaron mota ya tambaye shi inda zai sauka. Can sai ya ce ya mance sunan garin. To a cikin motar akwai wani mai zako-zakon hakora. Da Bafulatanin ya gan shi, sai ya nuna shi, ya ce: “Wallahi sunan garin […]

Kachako!
Kachako!

Wani Bafulatini ne ya hau mota daga cikin Kano zuwa wani kauye. Ana cikin tafiya sai yaron mota ya tambaye shi inda zai sauka. Can sai ya ce ya mance sunan garin. To a cikin motar akwai wani mai zako-zakon hakora. Da Bafulatanin ya gan shi, sai ya nuna shi, ya ce: “Wallahi sunan garin kamar hakoran wancan. Yaron mota ya ce: “Ko Kachako?” Bafulatani ya ce: “Gaskiyarka, Kashako!”

Daga Nura Suleja Neja, 08107575716