Kachalla Fulani ya kashe mutum 7 bayan an janye sojoji a Matazu

Mazauna sun ce ’yan ta’addan sun kuma tare hanyar Karaduwa zuwa Rimaye kwanan nan da rana tsaka, inda ta yi garkuwa da matafiya tare da dukan wasu

Kachalla Fulani ya kashe mutum 7 bayan an janye sojoji a Matazu

Jana’izar mutum bakwai da ’yan bindiga suka hallaka a yankin Sayaya da ke Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina

Fararen hula bakwai sun mutu a wani hari da ’yan bindiga suka kai jim kaɗan bayan janye sojoji a yankin Sayaya da ke Ƙaramar Hukumar Matazu a Jihar Katsina.

Mutane da dama a ƙaramar hukumar sun tsere zuwa yankin Sayaya domin samun aminci, bayan da hare-haren ’yan bindiga suka addabi yankunansu.

Mazauna yankin sun bayyana cewa jagoran ’yan ta’adda Kachalla Muhammadu Fulani da yaransa ne suka kai sabon harin, kusan nan take bayan ficewar sojojin da suka yi aikin tsaurara matakan tsaro a yankin bayan an yi garkuwa da marigayi Janar Rabe Abubakar (ritaya).

Shaidu sun ce maharan sun mamaye ƙauyen da kafin wayewar garin Alhamis, inda suka riƙa harbe-harbe babu ƙaƙƙautawa, lamarin da ya sa mazauna yankin suka rika tserewa daga gidajensu.

“Muna cikin barci ne sai muka ji ƙarar harbe-harbe masu ƙarfi. Mutane na ihu, yara na kuka, kowa kuma na gudu ta inda domin tsira da ransa.

“Bayan tafiyar maharan mun ƙirga gawarwakin mutanenmu bakwai da suka kashe a harin,” in ji wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro.

Mazauna yankin sun ce waɗanda aka kashe sun haɗa da manoma da ’yan kasuwa da suka yi fatan komawa rayuwarsu ta yau da kullum bayan makonni na samun ɗan kwanciyar hankali.

Sun yi zargin cewa fitaccen shugaban ’yan bindiga mai suna Kachallah Muhammad Fulani ne ya jagoranci harin. An jima ana danganta Kachalla Muhammadu Fulani da hare-hare masu jawo asarar rayuka da kuma sace mutane a Matazu da ƙauyukan da ke kewaye.

“Shi ne mutumin da ya daɗe yana addabar ƙauyukanmu. Shi ne ya sace Manjo-Janar Rabe (ritaya) da matarsa. Duk lokacin da muka ji an ambaci sunansa, mun san matsala na tafe,” in ji wani mazaunin yankin, Alaramma Jibrin.

Sun kuma yi zargin cewa wannan ƙungiya ce ta tare hanyar Karaduwa zuwa Rimaye kwanan nan da rana tsaka, inda ta yi garkuwa da matafiya tare da dukan wasu.

“Sun tare motoci a kan hanya kamar yankinsu ne. An daki mutane, an kuma yi garkuwa da wasu, ba wanda ya iya taimaka musu,” in ji wani matafiyi mai suna Sulaiman Sale Sayaya.

Shekaru da dama ke nan al’ummomin Jihar Katsina ke fama da hare-haren ’yan bindiga da suka haɗa da kashe-kashe, garkuwa da mutane, satar shanu da kuma lalata hanyoyin samun abin abin dogaro da kai na jama’a.

A halin yanzu, manoma na fargabar zuwa gonakinsu, ’yan kasuwa da matafiya kuma na guje wa manyan hanyoyi, yayin da iyalai ke rayuwa cikin ɗar-ɗar.

Ɗaya daga cikin hare-haren baya-bayan nan shi ne sace tsohon Manjo Janar Abubakar Rabe (ritaya) tare da matarsa, Hajiya Amina, a Matazu a ranar 30 ga watan Mayu.

Daga bisani Janar Rabe ya rasu yana hannun masu garkuwa da mutane, yayin da aka ceto matarsa bayan wasu kwanaki. Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce tare da ƙara kira ga gwamnatocin jiha da tarayya da su ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga.

Mazauna yankin sun ce bayan wannan lamari an tura jami’an tsaro zuwa Matazu da ƙauyukan da ke makwabtaka domin ƙarfafa tsaro.

Sai dai sun ce ’yan bindigar sun dawo ne kusan nan take bayan da sojojin suka fice.

“Lokacin da sojoji suke nan muna iya kwanciya cikin kwanciyar hankali. Amma da suka tafi, sai ’yan bindiga suka dawo da ƙarfi fiye da da. Muna jin kamar an yi watsi da mu,” in ji wani dattijo.

Al’ummar yankin sun kuma yi zargin cewa wannan ƙungiya ce ta tare hanyar Karaɗuwa zuwa Rimaye kwanan nan da rana tsaka, inda ta yi garkuwa da matafiya tare da dukan wasu.

“Sun tare motoci a kan hanya kamar yankinsu ne. An daki mutane, an kuma yi garkuwa da wasu, ba wanda ya iya taimaka musu,” in ji wani matafiyi mai suna Sulaiman Sale Sayaya.

Da aka tuntuɓi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce rundunar ba ta kammala tantance rahoton harin ba, yana mai alƙawarin bayar da ƙarin bayani daga baya.

Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a sake samun wata sanarwa daga rundunar ba.

Haka kuma, ƙoƙarin jin ta bakin Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasiru Mu’azu Danmusa, bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran waya ko saƙonnin tes da aka aika masa ba har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto.