Kada a amince da ’yan fashin da suka tuba – Ali kwara
Aminiya: Ka dade kana gwagwarmaya kan yaki da fashi da makami amma sai kamar an yi nasara sai kuma abin ya sake dawowa, wani lokaci za a kama mai laifi anjima kadan sai a ga ya fito, ko me yake jawo haka?Ali kwara: Abubuwan guda biyu ne, bayan kamawa sai kuma a sake su, akwai […]

Aminiya: Ka dade kana gwagwarmaya kan yaki da fashi da makami amma sai kamar an yi nasara sai kuma abin ya sake dawowa, wani lokaci za a kama mai laifi anjima kadan sai a ga ya fito, ko me yake jawo haka?
Ali kwara: Abubuwan guda biyu ne, bayan kamawa sai kuma a sake su, akwai wani lokaci idan gwamnati ta kaddamar da yaki da barayi ko ‘yan sanda suka bude wuta, idan aka kamo barayin sai wani babba ya fito ya ware kamar mutum 50 ya ce sun yi alkawari sun tuba, za su daina fashin, za su mika makamansu, sai a yi musu afuwa. Kuma ya yi musu shinge ke nan gwamnati sai ta barsu ba za ta kara yi musu komai ba, shike nan sai su dinga daukar bindigogin a wata jiha suna fashi, na wata jiha kuma sai su dawo nan su ci gaba da yin wa mutane fashi, idan kuma an samu wani rikicin kabilanci ko addini, wadannan wadanda aka ce sun tuban nan to su ne mayakan kasar nan.Su ne kuma masu satar mutane (kidnapping), don haka bai kamata wani ya zo ya tara mutane ya ce ya tubar da su ba za su kara fashi ba, a yarda a sake masa su.
Aminiya: Ko ka Jawo hankalin gwamnati kan wannan abu?
Ali kwara: A lokacin mulkin PDP duka na fada musu, har na fito na fada a kafofin yada labarai , saboda haka tubar da barayi da wani zai fito ya ce ya yi bai kamata a barshi haka kawai ba, don haka duk wanda ya fito ya ce ya tubar da su shi ma bai kamata a barshi ba. Nan gaba duk wani da ya ware mutum 50 ya ce ya tubar da su bai kamata a barshi ba, don ya sansu ke nan, tunda har ya fitar da su ya kamata hukuma ta kama su, a tambayi ina ya sansu da kuma me ya sa bai ba da rahotonsu ga gwamnati ba.
Aminiya: Me ya sa ‘yan fashin suka yiwo Yamma daga Gabashin Nijeriya?
Ali kwara: Abin da ya sa, ka san barawo a gabas idan ya rika yamma yake yiwowa, to ka san ina kasar Katagum, sai na yanke su a tsakani, sai suka taru a kan iyaka. Ka ga yanzu kasar Borno tsaro ya yi yawa, an yi ta fama d ‘yan fashin a wani gari Balaram da Jibilaram, sun yi ta fada har a cikin ruwa, da kungiyar da ba tasu ba. Kuma a bara, bai kai shekara ba ‘yan fashin sun yi fada a wajen Mafa a kasar Yobe, sun kashe wadansu daga cikin abokan fadansu suka debe bindigogin, ina tsammani bindigogin da sojoji suka karba na abokan fadan barayin ne wadanda ba kungiyarsu guda ba. kasar Borno za fi ya yi yawa, Jiragen sama sun yi yawa, Soja sun yi yawa a kasar Borno, kuma al’adun barayi al’adu ne na masu buya a daji, to a gabas yau tsaro ya yi yawa, ta ko’ina soja sun yi yawa, ka ga ba za su so haka ba, don haka suka yanke shawarar su taho dazuzzukan da ke yamma don su samu hutawa. Sai suka raba kansu, suka fara kawo bindigoginsu suna bi da shanu suna tahowa da mata da yara suna matsowa suna shigowa da bindigogin, tuni bindigogin sun shiga dajin Lame Burra, Wasu kuma sun shiga dajin Yankari, wasu kuma suna kasar Zaki, sai sauran yanzu suke biyowa a hankali da shanu har zuwa cikin dazuzzukan nan namu, wadansu kuma manyan sun daina zaman daji suna cikin Maiduguri. Ka ji dalilin da ya sa suka biyo nan. Kuma duk wajen da suka sauka Fulani sun sansu, tsoro ne kawai suke ji ya sa ba sa iya fada a je a kama su, saboda wani lokaci ko an je shiga dajin yana yi wa Jami’an tsaro wahala, amma duk barawon da ya sauka bafulatani makiyayi yana gane shi, duk su suke ba ni labari. Dole idan za a shawo kansu sai in ana musu hukunci mai tsanani. Ka ga shugaban barayin da aka yi fada da su daya dan Jihar Sakkwato ne, ‘Yan sandan yaki da ‘yan fashi na Jihar Borno sun kama shi bara da bindigogi guda biyu, kuma tsakanin kotu da ‘Yan sandan aka sake shi ya tafi. Don haka su barayi sun gane cewa hukumar Najeriya rariya ce, idan har ana so a zauna lafiya a canja hukunci.
Aminiya: Yaya dangantakar tsakaninku da jami’an tsaro? Kwanakin baya ka yi shiru har ana cewa Ali Kwara Ya kwanta, kome ya faru?
Ali kwara: Alhamdu lillahi. A ko’ina ba inda ba mutumin banza, amma a gaskiya ni kashi 99 cikin 100 jami’an tsaro ba ni da matsala da su, idan ma akwai matsala ‘yar kalilance, saboda sha’anin rayuwa, muna zaman lafiya da su, sun san aiki nake musu kuma addua suke mini, saboda haka ba ni da matsala da su.
Ni aikina kullum shi ne tarko, ni farar hula ne, kuma mutane sun yarda da cewa idan sun ba ni labari ba mai ji, kuma ina kashe dukiyata a duk kasar nan saboda in samu labari, kuma ba na bari kuma ba na hutu. Kuma ka ga ‘yan sandan da muke tare abin da na ci shi za su ci, abin da na sha shi za su sha, kuma tare muke kwana har a daji. Gwamnati ke biyansu albashi, sai dai Ihisani da idan na samu hali nake yi musu.
Ni dai ina nan na sa wa kasar ido ne kawai ina kallonta, shekaru biyu ke nan, ni na yi shiru ne ina kallon kasar. Don wancan gwamnatin da ta shude shekaru 14 na yi ina taimakonta amma sai ta gaza yi da gaske kan sha’anin tsaro, shi ya sa ni ma na tsaya na sa kasar a gaba ina kallonta. ‘Yan siyasa suna so a yi gyara amma ba sa bin salsalar idan aka kama barayin ina ake kai su, kuma wane irin hukunci ake yi musu. Haka har ya sa a cikin barayin wadansu suka dauka na mutu, wasu kuma suka ce sashin jikina ya shanye, wadansu kuma suka ce na koma Abuja ba ruwana da harkar tsaro. Amma a yanzu ina ganin shi shugaban kasa Muhammadu Buhari Jarumi ne, ina ganin yadda yake taba fannonin tsaro idan ya taba fannin fashi da makami da satar mutane za a samu saukinsa, tunda su a fili suke.
Aminiya: An ce Kome anayinsa ne don riba ko mene ne ribarka a kan wannan ?
Ali kwara: Riba iri biyu ne, akwai na duniya, akwai na lahira, ni ban shiga da talauci ba, ina da abin da zan ci, ni dai taimakon alumma na sa a gaba.
Aminiya: A Gombe ba da dadewa ba ‘yan bindiga suka abka wa ‘yan sanda har suka kashe ‘yansanda guda uku, kuma ‘’yan bindigan sukan kai hari ga Jami’an tsaro su tafi da bindigoginsu ko a yi kare jini biri jinni, ko me ke jawo haka a ganinka?
Ali kwara: Ba karancin kwarewa ba ne yake jawo haka, Jamian tsaronmu suna da kwarewa , amma yau da gobe ba ta bar kome ba, za ka rike bindiga, kana da ra,i kana son hutu, shi kuma mayaudari kullum kiwonka yake yi, don haka dole ne sai an samu lokacin da za su hilace ka, ko barci ya dauke ka, ko kana wata sabga, ko kana cin abinci, a nan sai a buge mutum, ba zuwa suke yi lokaci daya suke fada su ba, sai sun hilace su, kuma jiki da jinni. Shi dan ta’adda a kullum ba wanda yake gani zai raina kamar hukuma, kuma duk dan ta’adda idan ya samu bindiga daya so yake ta zama biyu, idan ya samu biyu, so yake su zama uku, kuma sayenta zai yi masa wuya, don bidiga tana da tsada, Naira dubu 400 zuwa dubu 500 suke sayenta yanzu, da su je su saya da tsada gwamma su samu Jami’an tsaro su gwada abka musu, idan suka samu nasara su dauke bindigogin su kara jari.
Aminiya: Me za ka ce a kan kokarin gwamnati ta fiskar tsaro, ko akwai ci gaba?
Ali kwara: Gaskiya akwai barazana ta fuskar tsaro yau a kasar nan, domin a yadda na samu bayani a ‘yan shekarun nan akwai bazuwar bindigogi, sun yi yawa sosai a kasar nan fiye da kowane lokaci. Kuma abin tsoron bindigogin na hannun yara kanane masu shekaru 15 zuwa 17 zuwa 30, wadanda mutuwar ma su ba tsoronta suke yi ba, abun kamar wasannin motsa jiki, yadda yara suke shiga wasan kwallon kafa, haka suke shiga harkar daukar bindiga.
Ka ga makaman nan abin da yake kawo yawansu a kasa shi ne fada irin na kabilanci da na addini, saboda a wani wuri sai ka ga hukuma ta kasa shiga tsakani, idan husuma ta taso sai ka ga wadansu suna da arziki suna so su kare kansu, sai su kafa kungiya su ba da kudade a je a sayo musu makamai don su kare kansu, to makaman nan idan an sayo su wadanda za su bayar ba su san hannun da zai shiga ba, su dai bukatarsu su kare kansu,ko kuma a tare musu wannan masifa. Daga nan bindigogi suka yi ta zama masifa a kasa. Ka ga a da ta kan iyakar kasar Chadi ne ake shigowa da bindigogi cikin kasar nan, yanzu kuma ta kasar Nijar aka fi shigowa da bindigogi. Kuma matsalar saboda fadi ne da kan iyakokin kasarmu ke da shi. Ka duba daga kasar Borno zuwa kasar Sakkwato kwalta nawa ne ta fita a kasar nan? Ba ta fi kilomita 20 ba, sauran kan iyakan duk daji ne, kuma ko’ina mashin da mota da rakuma da dawaki suna shiga. Zancen jami’an tsaro a kan iyaka da sauran aiki, tunda ba katanga ka yi a kasarka ba. Jami’an tsaro suna kan iyaka ne amma miyagun makaman ta daji suke shigowa, wasu a kan rakuma da shanu, aiki ne mai wahala, sai dai a sa sintiri cikin daji ko zai rage, idan zai yiwu.
Aminiya: Wadanne irin bindigogi ne suka bazu cikin kasa?
Ali kwara: Bindigogi na yaki da kowace kasa take yaki da su a duniya sune suke shigowa Nijeriya da RPG da Mashingan da dukkan bindigogi da ka sani manya da kanana, su ne a hannun mutane.
Aminiya: Wace shawara za ka bai wa gwamnati kan wannan sha’ani na tsaro?
Ali kwara: Ya kamata hukuma ta tashi tsaye haikan. Yakamata hukuma ta gane wuraren da ake rikicin ta je ta samu shugabannin ta kare musu rayukansu ta kuma hana su ci gaba da saye, don lokacin da za su tara kudaden a sayo a harzuke suke, so suke a kare su yaki zai ci su. Kuma hukuma ta kula da mutuncin Jami’an tsaron, da jin dadinsu da ciyar da su gaba a kan lokaci, ko idan sun yi bajinta, saboda a shekarun baya dai an samu sakaci a wajen jami’an tsaro, wanda da idan dan sanda ya yi aiki za a ba shi lambar yabo, za a ciyar da shi gaba, amma yanzu an wayi gari idan zai je ya mutu ma baa damu da shi ba. Sai ka ga an bai wa maigadin wani babba mukami ko mai kada gangan ‘yan sanda an ciyar da shi gaba, amma masu fada da miyagu ba a tuna da su ba, hakan ya jawo ‘yan sanda a kasar nan suka gane cewa aikinka da kwazonka bai cika kawo maka ci gaba ba. A yanzu idan hukuma tana so ta yi gyara, ya kamata duk dansandan da ya yi kwazo har ya kwato bindiga ko ya kama ‘yan bindiga, ya kamata a yi masa biki a ba shi lambar yabo da karin girma. Lokacin Tafa Balogun na Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da lokacin Ehindero da zamanin Mike Okiro, duk lokacin da mukayi fada da barayi muka yi kokari za a bai wa dan sanda karin girma. Irinsu muna tare da su, kome dare idan muka ce su tashi a bi masu bindiga za su bi su, akwai bukatar a rika kyautata musu, kuma al’umma ta kara yi wa Jami’an tsaro addu’a, a kuma taimake su da labari.
Aminiya: Gwamnati ta ce ana samun sauki kan sha’anin tsaro?
Lalle su suna wannan maganar wajen fada da ‘yan Boko Haram ne, ni kuma matsalolin da duk nake magana wajen ‘yan fashi da makami ne da masu satar mutane. Nan ba wani ci gaba, a duk fadin kasar nan ba inda ba a satar saniyar bafulatani, kuma za kasamu akwai irin wadannan tubabbun barayin, akwai ‘yan banga, za ka samu har da hannun wadansu sarakuna ma wajen sai da shanun.