Kada a dakatar da aikin titin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna

Labarai sun watsu a makon jiya cewa aikin titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, wanda ya yi matukar nisa kuma ake daf da kammalawa akwai yiwuwar ba za a kammala shi a nan kusa ba.Aikin wanda zai ci Naira biliyan 170 an bayar da kwangilarsa ne ga kamfanin gine-gine na kasar China da ake […]

Kada a dakatar da aikin titin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna
Kada a dakatar da aikin titin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna

Labarai sun watsu a makon jiya cewa aikin titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, wanda ya yi matukar nisa kuma ake daf da kammalawa akwai yiwuwar ba za a kammala shi a nan kusa ba.
Aikin wanda zai ci Naira biliyan 170 an bayar da kwangilarsa ne ga kamfanin gine-gine na kasar China da ake kira China Cibil Engineering Construction Corporation (CCECC) domin gina ingantacciyar hanya jirgin kasa mai tsawon kilomita 186 daga Abuja zuwa Kaduna. An shirya za a kammala shi a cikin wata 46, kuma duk da kamfanin CCECC ya tsallake wa’adin kammala aikin a Disamban 2014 da aka diba masa, an kammala kashi 80 cikin 100 na aikin.
 A makon jiya jami’an kamfanin CCECC sun ce aikin yana fuskantar sababbin kalubale sakamakon yadda darajar Naira take faduwa, lamarin da yake kawo tarnaki ga kamfanin ya kammala aikin a kan wa’adin da aka diba masa.
Gwamnatin Jonathan ta karbo bashin kayayyakin aiki na Dala miliyan 900 daga Bankin Edport and Import Bank na kasar China ta hannun Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya don gudanar da wannan aikin. Fasalin bashin ya nuna za a bayar da bashin ne kashi-kashi ta hanyar shigo da kayayyakin aikin ta jiragen ruwa, kamar kwagirin titin jirgin da kayayyakin yin gini da manyan motocin daukar kaya da gadojin kankare da taraktocin China da filolin kankare da sauran kayayyakin shimfida titin jirgin da zai kai kilomita 186.
A karkashin yarjejeniyar, ana sa ran Gwamnatin Tarayya ta samar da kan jiragen kasa na zamani da taragu iri-iri da ma’aikata tare da samar da na’urorin sadarwa na zamani.
Wasu dalilai da aka bayyana na tafiyar hawainiyar da aikin ke yi sun hada da raunin sanya ido daga Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya wadda aikinta ne ta tabbatar da an kammala aikin a kan lokaci sai kuma jan kafa daaga bangaren Hukumar Kula da Sadarwa ta kasa (NCC) wajen amincewa a samar da na’urar sadarwar da za ta bayar da damar sadarwa a tsakanin direbobin jiragen da kuma tashoshin jiragen.
Ministan Sufuri Rotimi Chibuike Amaechi ya yi alkawari lokacin da ya karbi ragamar mulki a bara cewa zai kira taron dukkan bangarorin da suke da hannu a yarjejeniyar domin tabbatar da an kammala aikin a kan lokaci. kalubalen da ke fuskantar aikin ba sababbi ba ne. Abu ne da ya zama ala’adaa kasar nan musamman lokacin da aka samu canjin gwamnati a ga an yi watsi da ayyuka da tsare-tsaren da gwamnatin da ta gabata ta faro, amma wannan aiki bai dace a yi watsi da shi ba, idan aka lura da muhimmancin da yake da shi wajen inganta rayuwa da harkokin tattalin arziki na daukacin yankin arewacin kasar da kuma Abuja.
Faduwar darajar Naira matsala ce da ta zama gama-gari a kwanakin nan, amma lura da irin tasirin da aikin zai yi, ana sa ran kamfanin CCECC zai iya samu canjin Dala a farashin gwamnati ba sai ya je kasuwar bayan fage ba. Shugaban kasa Buhari ya ce dalolin kasar nan da ke ajiye na muhimman al’amura ne, kuma a zahiri wannan aiki na daga cikinsu.
Ba wannan ne karo na farko da ’yan kwangila suke gaza kammala muhimmin aikin titin jirgin kasa a kasar nan ba. A shekarar 2006, Shugaba Olusegun Obasanjo ya sanya hannu kan kwangila da kamfanin CCECC don zamanantar da titin jirgin kasa daga Legas zuwa Kano. Wannan shi ne kashi na farko daga cikin kashe-kashe uku na inganta titin jirgin. An kasa aikin zuwa sassa biyar da suka hada da Legas zuwa Ibadan (kilomita 181) da Ibadan zuwa Ilorin (kilomita 200) da Ilorin zuwa Minna (kilomita 270)  da Minna zuwa Abuja zuwa Kaduna (kilomita 360) da kuma Kaduna zuwa Kano (kilomita 305). Duk da cewa an fara aikin an dakatar da shi a shekarar 2008, sakamakon takaddama kan yarjejeniyar. Gwamnatin Tarayya ta sake sanya hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin Guangdong dinguang International Group domin gina sabon titin jirgin kasa mai gudun fitar hankali (RFR) daga Legas zuwa Abuja da kuma jirgin kasa mai aiki da lantarki daga daga birnin Legas zuwa filin jirgin sama na Murtala Mohammed International Airport da kuma daga birnin Abuja zuwa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport. An kebe Dala biliyan biyu domin fara ayyukan amma ba sake jin komai tun lokacin. Ana ganin Shugaba Buhari zai canja wannan dabi’a bisa lura da ganawar da ya yi a baya-bayan nan a wajen taron kasashen Afirka da China da aka yi a Afirka ta Kudu inda ya tattauna yadda za a gina titin jirgin kasa mai tsawon kilomita 1,402 daga Legas zuwa Kalaba, aikin da ake sa ran za kashe Dala biliyan 12 da China za ta samar a matsayin bashi. Kuma ya sake kulla yarjejeniyar aiki inganta titin jirgin kasa na Dala biilyan 8.3 daga Legas zuwa Kano da aka dakatar.
Aikin titin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna babban aiki ne na kasa, kuma ganin an yi nisa a kansa zai zama abin kunya ne ga kasar nan ta bari ya gaza. Wajibi ne a dauki matakai cikin gaggawa domin a kammala aikin a kaddamar da shi.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno