Kada a kawo mana ’yan China —Likitocin Najeriya

Likitocin Najeriya sun yi Allah-wadai da shirin gwamnatin tarayya na karbar wasu likitoci ’yan China da za su taimaka a yunkurin shawo kan cutar coronavirus. Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA), wadda ta nuna rashin amincewa da shirin, ta ce ba ta ji dadi ba da aka yanke wannan shawara ba a tuntube ta ba, kuma […]

Kada a kawo mana ’yan China —Likitocin Najeriya

Shugaban Kungiyar Likitoci ta Najeriya Francis Faduyile

Likitocin Najeriya sun yi Allah-wadai da shirin gwamnatin tarayya na karbar wasu likitoci ’yan China da za su taimaka a yunkurin shawo kan cutar coronavirus.

Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA), wadda ta nuna rashin amincewa da shirin, ta ce ba ta ji dadi ba da aka yanke wannan shawara ba a tuntube ta ba, kuma ba tare da an yi la’akari da dokokin da suka gindaya sharudda game da likitocin waje su duba ’yan kasa ba.

“Don haka”, a cewar kungiyar a wata sanarwa da shugabanta, Francis Faduyile, ya sanyawa hannu, “mun yi matukar takaici da jin cewa a maimakon [aiki da tanade-tanaden Dokar Aikin Likita] Gwamnatin Tarayya za ta gayyato ’yan China wadanda rahotannin da muke da su suka nuna cewa su ma kasarsu ba ta samu kanta ba tukunna.

“[Sannan wani abin dubawa shi ne yadda] karuwar wadanda suka kamu da cutar a Italiya ta dace da zuwan wasu ’yan China da sunan ba da taimako…”

Sanarwar ta kuma ce ba ta ga dalilin zuwan likitocin China Najeriya ba domin “hatta Majalisar Dinkin Duniya kwanan nan ta yaba da matakan da Najeriya ta dauka zuwa yanzu.

“Muddin gwamnati ta ci gaba da wannan shirin na debo ’yan China to za ta kassara karsashin likitocinmu wadanda suka jima suna sadaukar da rai a sahun farko na wannan yakin…mun kasa fahimtar tasirin da mutum 18 za su yi balle su kawo wani sauyi”.

Ita ma kungiyar kwadago ta TUC, ta bakin shugabanta Quadri Olaleye da babban sakatarenta Musa Lawal-Ozigi, ta yi kira ga gwamnati da kada ta kyale liktocin na china su zo Najeriya.

A cewar shugabannin kwadagon, babu dalilin zuwan ’yan China domin kankantar adadin wadanda suka kamu da karancin wadanda suka mutu sakamakon cutar a Najeriya alama ce da ke nuna cewa likitocin da kasar ke da su sun isa su taka wa matsalar birki.

A karsehn makon jiya ne dai ministan lafiya Dokta Osagie Ohanire ya ce an sanar da shi cewa wata kungiya ta kamfanonin ’yan China da ke Najeriya ta dauki nauyin shigo da wasu kayan aiki da kwararrun likitocin da za su taimaka a yakin da ake yi da cutar coronavirus su 18.

Ministan ya ce likitocin za su taho ne da magunguna da na’urorin numfashi, da kuma kayan gwajin cutar ta COVID-19.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50