‘Kada a nada ’yan adawa a gwamnatin Yobe’

Wani shugaban matasa a Jihar Yobe Malam Umar Gambo ya shawarci Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam da kada ya tsoma ’yan adawar da suka canja sheka zuwa Jam’iyyar APC daga PDP a sabuwar gwamnatin da Yake shirin kafawa don gudun sanya bara-gurbi. Malam Umar Gambo ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya a Damaturu […]

‘Kada a nada ’yan adawa a gwamnatin Yobe’
‘Kada a nada ’yan adawa a gwamnatin Yobe’

Wani shugaban matasa a Jihar Yobe Malam Umar Gambo ya shawarci Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam da kada ya tsoma ’yan adawar da suka canja sheka zuwa Jam’iyyar APC daga PDP a sabuwar gwamnatin da Yake shirin kafawa don gudun sanya bara-gurbi.

Malam Umar Gambo ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya a Damaturu sakamakon yadda ’yan adawar ke tururuwa zuwa APC a matakin jihar da kasa baki daya. Malam Umar ya ce mafi yawan wadanda suka canja sheka daga jam’iyyun adawa a jihar zuwa na da ra’ayoyi da manufofin da suka sha bamban da manufofin Jam’iyyar APC, don haka barna ce a sa su cikin gwamnatin APC. Ya ce ko da za a tsoma ’yan adawar, to, a dan yi jinkiri zuwa wani lokaci.
Ya ce hatta sabon zababben Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran zababbu a sauran jihohin kasar nan a karkashin Jam’iyyar APC ya kamata su yi taka-tsantsan da nada wadanda suka yi canjin sheka daga PDP a kan mukamai.
Ya ce al’ummar kasar nan na sa ran ganin abubuwa masu muhimmanci daga sabon Shugaban kasa musamman abin da ya shafi shawo kan tabarbarewar tsaro a jihohin Yobe da Borno da
Adamawa da kuma kuncin rayuwa da ke addabar al’ummar kasar nan da kawar da cin hanci da rashawa.