Kada a rika saurin yanke hukunci

Barkanmu da Sallah Manyan Gobe Da fatan kun sanya kayan sallarku lafiya. A yau na kawo muku labari a kan rashin fai’dar saurin yanke hukunci. Labarin na kunshe da yadda mutane ke yanke hukunci a kan abin da ba su da masaniya a kai. Da fatan Manyan Gobe za su guji yanke hukunci ba tare […]

Kada a rika saurin yanke hukunci
Kada a rika saurin yanke hukunci

Barkanmu da Sallah Manyan Gobe

Da fatan kun sanya kayan sallarku lafiya. A yau na kawo muku labari a kan rashin fai’dar saurin yanke hukunci. Labarin na kunshe da yadda mutane ke yanke hukunci a kan abin da ba su da masaniya a kai. Da fatan Manyan Gobe za su guji yanke hukunci ba tare da bincike ba. A sha karatu lafiya:
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi

Kada a rika saurin yanke hukunci

Akwai wani tsoho yana da da mai shekara 22 da ake kira Haruna. Wata rana sai suka shiga jirgin kasa. A bayan kujerarsu akwai wasu  mutane; mata da miji.
Da jirgi ya fara tafiya, sai Haruna ya sa hanunsa daya a kan tagar jirgi ya ce “Baba! Kalle ni iska na buga ni”. Sai mahaifinsa ya yi murmushi ya ce: “da kyau”. Can sai ya sake cewa: “Baba! Kalli tsuntsaye a kan bishiya” sai tsohon ya sake murmushi ya ce da shi da: “kyau”. Bayan wadansu dakiku sai aka fara yayyafi, sai ya ce: “La! Baba kalli ruwa na taba hannuna.”
 A wannan lokacin, Haruna ya fara ba mutanen jirgin haushi. Ganin cewa shi ba karamin yaro ba ne kuma yana hali irin na yara. Sai daya daga cikinsu ya ce wa mahaifinsa: “Don Allah ka yi wa danka magana domin yana damunmu kuma ba shi kadai ne a jirgin nan ba. In da hali ka kai shi asibitin mahaukata don ba shi da lafiya”. Sai mahaifinsa ya yi murmushi ya ce musu: “Yanzun ma dawowarmu ke nan daga asibiti ai tun da aka haife shi, sai yau ya fara gani da idonsa da makaho ne”. Jin haka, sai jikin mutanen jirgin ya yi sanyi musamman ma wanda ya yi tambayar.
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi daga wannan labarin, kuma ba za su zama masu saurin yanke hukunci ba tare da sun yi bincike ba.