Kada a yi rikici da kowa saboda ni -Janar Buhari
Ganin yadda lokacin manyan zabukan kasar nan ke kara kawo jiki da yadda ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula masu nasaba da yakin neman zabe, jama’a sun fara bayyana fargabarsu bisa tsoron barkewar rikici irin wanda ya biyo bayan zabukan shekarar 2011. An fara fuskantar matsaloli a makon jiya, misali a lokacin bikin kaddamar […]

Ganin yadda lokacin manyan zabukan kasar nan ke kara kawo jiki da yadda ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula masu nasaba da yakin neman zabe, jama’a sun fara bayyana fargabarsu bisa tsoron barkewar rikici irin wanda ya biyo bayan zabukan shekarar 2011.
An fara fuskantar matsaloli a makon jiya, misali a lokacin bikin kaddamar da kamfe din dan takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC wato Janar Muhammadu Buhari, a Jihar Ribas, an kai wa wadansu magoya bayansa hari alokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wurin taron. Har ila yau, a karshen makon jiyan a garin Jos, an kona motocin kamfen din Shugaba Goodluck Jonathan, wato dan takarar Shugabancin kasa na jam’iyyar PDP. Sai harin bam da aka kai ofishin jam’iyyar APC da ke garin Okirka a Jihar Ribas, watao mahaifar Madam Patience Jonathan, uwargidan shugaba Jonathan. Akwai kuma rahoton kai farmaki da aka yi a gidan Shugaban Jam’iyyar APC Cif John Oyegun da ke Abuja, wanda ake zargin wadansu ’yan bindiga sun yi a safiyar ranar Litinin. A Kachiya ma da ke jihar Kaduna an ce wani direba ya sha da kyar lokacin da yake tuka wata mota mai dauke da hoton shugaba Jonathan.
Wannan zaman tankiyar ya sanya Janar Buhari ya nisanta kansa daga tashe-tashen hankulan, inda ya ce babu abin da ya hada magoya bayansa da tashe-tashen hankulan da ake yi masu nasaba da siyasa. Janar din ya bayyana hakan ne lokacin da yake kaddamar da majalisar yakin neman zabensa a Abuja, kuma ya yi kira ga magoya bayansa da kada su dauki doka a hannunsu, komi tsananin tsokanarsu da magoya bayan jam’iyya mai mulki za su yi musu, kuma su guji yin kalaman batanci ga wani dan takara, ko su fadi bakar magana ko kuma ta da hankali a madadinsa. Awata hira da ya yi sashen Hausa na BBC ya yi karin haske game da wannan kiran da ya yi. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Tambaya: Me za ka ce game da tashe-tashen hankulan siyasan da suke faru a halin yanzu?
Janar Buhari: Abin da ya kamata tun da barna ce aka yi, idan ’yan sanda sun kama su, sun tambaye sun ce su yarana ne. To shi ke nan sai ’yan jarida su buga. Ba haka nan ba kurum dan jarida ya yi tsalle ya koma gefe daya, ya ce ga abin da ya abku. Alhali ba a tabbatar da abin ba.
Tambaya: Kwanan nan Farfesa Bolaji Akinyemi ya yi kira ga jam’iyyun APC da PDP kan ku sanya hannu cewa magoya bayanku ba za su tada hankali ba, kan al’amuran da suka shafi zabe. Wasu za su ce watakila saboda ba ku sanya hannu ba shi ya sa aka fara ganin wannan?
Janar Buhari: A’a, ai ba batun sanya hannu ba ne. Tun yaushe mu muke magana muna cewa duk masu goyan bayanmu ko bakar magana kada su yi wa wani. Muna fadin hakan, kuma abin da za mu iya yi ke nan.
Tambaya: Wasu kan ce irin maganganun da kukan yi su ne suke sa mutane suke zuwa suna yin irin wadannan abubuwa?
Janar Buhari: Kamar wadanne cikin maganganun. Ni dai maganar da nake yi a kai shi ne batun sha’anin tsaro, wanda ya damu kowa a kasar nan. Ana kona kauyuka, ana kashe mutane, ana kashe yara a makarantu suna barci, ana zuwa majami’u ana kashe mutane. Ana zuwa masallatai ana kashe mutane, ana zuwa kasuwa da tashar mota ana kashe mutane. To wannan mene ne?
Tambaya: Ko kwanan nan Shugaban kasa ya yi magana cewa saboda sakacin gwamnatocin baya, har ma ya ce lokacin da kake shugaban kasa, ko bindiga guda ba ka saya wa sojoji ba, duk shi ne ya jawo lalacewar tsaro irin wannan?
Janar Buhari: Wannan jahilci ne, wata 20 kawai muka yi a mulki, kamar yadda duk dan Najeriya mai sha’awar tarihin kasar nan ya sani. Cikin wata 20 din nan. Ya je ya tambaya ya gani, jiragen sama, ba ma bindiga ba, guda nawa muka saya. Saboda kusan bai san maganar da yake yi ba. Na kalli lokacin da yake magana a Jihar Legas yana cikin fushi, ko da wa yake fushi ni ban sani ba. Shekara shida ya yi. Ku fa tuna ’yan Najeriya Janar Yakubu Gowon shekara tara ya yi yana shugaban kasa. Wata 30 cikin shekara tara mukai y muna yakin Basasa, amma ko bashin kwabo ba a ciyo ba.
Tambaya: Ita wannan matsala ta tsaro abu ne wanda idan ya lalace yana da wahalar gyarawa, yanzu idan Allah zai kai ka wannan kujerar, wane mataki za ka dauka na ganin cewa ka kawo karshen matsalar?
Janar Buhari: Wannan magana gaskiya ce. Ni a aikin sojan da na sani shekara kusan 23 zuwa 25. Soja bai isa ya yi magana da dan jarida ba a kan aikinsa, amma sai ga shi yanzu sojoji suna fadin an tura su, su fuskanci ’yan ta’adda babu bindigogi ko harsashi. Sojan Najeriya ya fito ya yi wannan maganar, to abin ya baci.
Tambaya: Wasu masana tsaro suna cewa shi kanshi karsashin sojojin ya rigaya ya durkushe shi ya sa ko an ba su makaman ba za su iya zuwa wannan yakin ba, ku kuna tunanin wata kila ku kawo wasu sojojin ne ba wadannan ba?
Janar Buhari: Mu kawo sojoji daga ina. Waye zai tsare mana Najeriyar. Wadanda suka yi wasu dabaru za su iya gudu daga kasar nan da su da iyalansu, suna da gida da kamfanoni a waje, wadannan za su iya gudu. Mu babu inda za mu iya zuwa. Mu nan ne kasarmu. Babu wani waje da za mu je.