Kada a zabi shugaban da zai cusa wa mutane akidar addininsa – Shugaban darikar Angalica

Shugaban cocin darikar Anglica da ke Kalaba Jihar Kuros Riba Rabaran Tunde Adeleye, ya bayyana cewa ko kusa ba za su yarda kasar nan ta yi shugaban da zai tursasa wa mabiya wani addini bin akidodin addininsa, don haka ne ’yan Najeriya su tabbata sun zabi shugaba wanda baruwansa da akida ta wani addini, musamman […]

Kada a zabi shugaban da zai cusa wa mutane akidar addininsa – Shugaban darikar Angalica
Kada a zabi shugaban da zai cusa wa mutane akidar addininsa – Shugaban darikar Angalica

Shugaban cocin darikar Anglica da ke Kalaba Jihar Kuros Riba Rabaran Tunde Adeleye, ya bayyana cewa ko kusa ba za su yarda kasar nan ta yi shugaban da zai tursasa wa mabiya wani addini bin akidodin addininsa, don haka ne ’yan Najeriya su tabbata sun zabi shugaba wanda baruwansa da akida ta wani addini, musamman idan aka yi la’akari da wasu jam’iyyun siyasa an kafa su ne domin cimma wata manufa ta wani addini, lamarin da kasar nan a cewarsa tafi karfin a ce za a cusa wa wasu mabiya akidar da ba ta addinin su ba ce.

Shugaban ya furta haka a hirar da ya yi da manema labarai a harabar majami’arsa da ke Kalaba.
“Ba za mu yarda da duk wani shugaba ba da zai cusa akidar wani addini ga kishiyar addinin Kirista idan aka ce za a tursasa mana kuwa, ni zan jagoranci a nuna masa kyama da kuma yakar lamarin. Ni ba zan yarda ba a ce ’ya ta a matsayina na Kirista a ce sai ta sanya hijabi a makaranta, kamar yadda Gwamna Jihar Ogun ya yi a jiharsa, sanya dokar zuwa makaranta ga ’ya mace da hijabi, inji shi.
Ya ce, duk da bai fito karara ya nuna ga jam’iyyar da yake nufi ba, amma wasu masu fassarar al’amuran yau da kullium na nuni da cewa, da jam’iyyar adawa ta APC yake da ’yan takararta.
Da ya juya kan batun makudan kudin da kwanan baya da ake zargi an dauka a jirgin shugaban kungiyar CAN, Rabaran Adeleye ya ce: “Masu zargi ba su da wata hujja kamata ya yi su fara yin bincike tukuna kafin ma a fara surutu.”
Ya bayyana fargabarsa kan yadda akalar siyasar kasar nan musamman zaben 2015 ke ciki. Lura da yadda ake samun jam’iyyun siyasa wasun ke da manufa ta bangaranci ko addini wajibi ne a yi hattara a zabi shugaban da ba zai raba kan jama’a ba, ko nuna akida ta addini, alhali kasar nan na da kwararrun ’yan siyasa hazikai da za su kai kasar nan ga gaci .
A karshe ya nemi ilahirin kiristoci su fito su kada kuri’a idan zabe ya zo, su zabi shugaban da ba zai cusa musu akidar addininsa ba.