Kada ASUU ta yi kuskuren janye yajin aiki gwamnati ba ta cika alkawarinta ba – Solomon Dalong

Fitaccen lauyan nan dan rajin kare hakkin al’umma Barista Solomon Dalong, ya gargadi kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) cewa kada ta yarda ta yi kuskuren janye yajin aikin da ta share fiye da wata uku ba tare da gwamnati ta cika alkawarinta ba. Barista Dalong ya bayyana haka ne a lokacin da ya zantawa […]

Kada ASUU ta yi kuskuren janye yajin aiki gwamnati ba ta cika alkawarinta ba – Solomon Dalong

 Barista Soloman DalongFitaccen lauyan nan dan rajin kare hakkin al’umma Barista Solomon Dalong, ya gargadi kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) cewa kada ta yarda ta yi kuskuren janye yajin aikin da ta share fiye da wata uku ba tare da gwamnati ta cika alkawarinta ba. Barista Dalong ya bayyana haka ne a lokacin da ya zantawa da manema labarai a Gombe ciki kuma har da wakilinmu:  
Aminiya: Barista kasancewarka tsohon malamin jami’a me za kace game da yajin aikin da malaman jami’oin kasar nan ke yi da aka gagara daidaitawa?
Barista Solomon Dalong: Ina kira ga Gwamnatin Tarayya ta shirya da malaman jami’a, ba ma shiryawa ba ne kawai, batu ne na kudi Naira biliyan 97 da idan ba ta da su ya zama dole ta je ko bashi ne ta nemo a Bankin Duniya ko IMF don biya wa malaman bukatunsu a samu a bude jami’o’i yara su koma a ci gaba da karatu. Saboda babu yadda za a yi a samu ilimi mai inganci ko shugabannin da za su jagoranci kasar nan muddin ba su yi karatu ba, don haka ina kira ga gwamnati ta gaggauta zuwa duk inda ta san za ta samu kudi ta nemo ta zuba a harkar ilimi saboda in ba don ilimi ba babu yadda za ayi a samu shugaba a kasa mai digirin-digirgir (Phd) ko a samu mataimakinsa da ke da ilimin fasahar gine-gine, saboda hakan ban ga dalilin da zai sa ayi ta jan wannan yajin aiki na malaman jami’a ba, hakan zai kunyatar da kasar a idon kasashen duniya.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga bangaren ASUU?
Solomon Dalong: Su malaman jami’a ina kira kada su yi kuskure su ce za su janye wannan yajin aiki ba tare da an biya musu bukatunsu ba, idan kuma suka yi kuskuren haka, to wannan shi ne yajin aiki na karshe da za su kira a amsa a kasar nan. idan kuma ba a ba su wannan kudi da suke nema ba daga wajen Gwamnatin Tarayya suka yarda suka janye yajin aikin abin da zai biyo baya nan gaba shi ne idan suka ce a tafi yajin aiki sa ’yan Najeriya za a yi su jefe su don haka su tsaya kada su janye har sai an cika musu alkawarinsu an ba su kudin da suke nema.
Aminiya: Ba ka ganin ASUU sun fiye yawan bukata ne ya sa da sun nemi a ba su kudi aka hana sai su tafi yajin aiki, kana ganin bai kamata su sassauta bukatunsu ba?
Solomon Dalong: Ba gaskiya ba ne a ce ASUU sun fiye yawan bukatu domin matsalar tabarbarewar ilimi a kasar nan ta samo asali ne tun a 1992, inda a dalilin haka aka yi yarjejeniya duk shekara biyu za a rika  waiwayar matsalolin nasu ana ragewa da yake an yarda da hakan shi ya sa a can baya ba za ka ji an samu matsalar da za ta kai ga shiga yajin aiki ba. Amma yanzu da akayi biris da su ka ga al’amarin kullum sai kara tabarbarewa yake yi.  Bisa ga wancan jarjejeniya da gwamnati ta yi da ASUU shi ya sa ta ce ta yi alkwarin sanya Naira biliyan 100 duk shekara a harkar ci gaban ilimi a Najeriya, sannan akwai sharuddan da ake da su na kasa da kasa a harkar ilimi na bayar da kashi 26 cikin 100 na kasafin tarayya. A lokacin marigayi Shugaba ’Yar’aduwa ta samar da kashi 18 ne kawai bayan mulkin ’Yar’aduwa sai ya koma kashi 12 yanzu kuma an dawo ana neman a samu kashi takwas, ai wannan Naira miliyan 100 da ake nema a sanya a harkar ci gaban ilimin ba daga cikin kasafin kudin kasar nan za a cire ba daga Asusun Tallafa wa Ilimi ne (ETF) wanda su ASUU din su suka kafa asusun, batun cewa ASUU suna bukata da yawa maganar banza ce. Suna tambayar abin da ya kamata ne domin a kasar nan akwai kudi  idan kuma gwamnati tana maganar ba kudi, ba za ta iya ba su ba jiragen sama nawa ake da su a fadar Shugaban kasa? Idan ba ku sani ba akwai jirage fiye da goma, Najeriya ta kai Amurka ne? Ai su shugaban kasarsu Barrack Omaba guda biyu kawai yake da su, Firayiministan Birtaniya yana da daya, don haka gwamnati ba ta da hurumin ja-in ja a kan wannan matsala ta yajin aiki. Rokon kawai da zan sake yi wa ASUU shi ne kada ta yarda ta janye wannan yajin aiki har sai an ba su kudin nan. Amma idan suka yi kuskure suka janye ina tabbatar muku nan gaba idan suka kira yajin aiki sanyawa za mu yi ’yan Najeriya su fatattake su, domin ba masu gaskiya ba ne.

TSOKACI

Wasu gurbatattun ’yan Arewa ke sa Dakubo yin bambarma

Daga Manjo Hamza Al-Mustapha

A ranar Asabar da ta gabata ne dogarin marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha wato Manjo Hamza Al-Mustapha ya halarci wani taron matasa a Kaduna, taron ya fara shan suka tare da bayyana shi da wani shirin tazarcen Shugaba Jonathan. Mun so tattaunawa da Manjo Al-Mustapha kan wannan zargi amma ba mu yi nasara ba, to amma wakilinmu Mohammad Yaba, ya ruwaito mana jawabin da ya gabatar a wurin taronkamar haka:
Matan Mujahid Dakubo Asari duk ’yan Arewa ne domin matarsa ta farko Bafulatana ce matarsa ta biyu Shuwa Arab ce. ’Yayansa kuma jikokin Arewa ne, amma na gano cewa wadansu ne gurbatattu daga Arewa suke  saka masa ra’ayin kiyayyar arewa. Kuma shi Asari Dokubo ya yi nadama ya kuma tuba sannan a shirye yake ya bayyana sunan wadannan ’yan Arewan da suke haddasa fitina da ke lalata kasa.
Idan za a yi abubuwa na taimaka wa kasa ba a shakka ana daukar imani ne ga Ubangiji ba a shakka domin bauta ka zo ka yi wa mutane kuma a bautar da kake yi a nan ne Allah zai ba ka lada, wannan ladar kuma ita ce a matsayin taka ladar. Domin da muka je Kudancin Najeriya mun nuna wa sarakunansu cewa Arewa ba sa kin Kudu kuma wadanda ake ingizawa suke zagin Kudu kuskure ne.
Su ma suka yi bayani, mu ma muka yi musu bayani. Muka kuma saka hannu. Babana a nan Dokta Fedreck Fashoun shi Bayarabe ne, a lokacin da aka zartar min da hukunci domin a musguna min a kashe ni, shi ya tsaya tsayin-daka cewa ya gano gaskiya abin da ake bugawa a jaridu da fada a rediyo da talabijin shiri ne na wadansu mutane da suka hada kai da wasu.
Tun daga wannan lokaci ya zama uba a gare ni. Ya ce yau tunda Arewa ta yi taro, ya ce ba za a yi taron nan ba ba tare da shi ba. Muna godiya gare shi. A yau muna gaya muku cewa cikin yarda, mutanen Ibo da mutanen Kudu maso Kudu na Najeriya da mutanen Yarbawa sun yarda mu hada hannu tare da su a kan kare hakkin juna.
A kan tsayawa da taimaka wa juna a kan kawar da da fitintinu a kan girmama manya na kowane bangare. Da muka zauna muka samu wannan yarjejeniya Baban Sarakunan Ibo sai ya ce da ni Allah Ya kawo ku yau kun yake mu ba tare da kun harba bindiga ko daya ba.
Ya kamata ya halarci wannan taro amma saboda yana halartar taron bikin Ranar Ibo ta Duniya shi ya sa ya aiko wakilansa domin su yi bayani a nan. Dukkansu sun amince cewa babu wani abu ko wasu mutane wadanda suka saba amfani da su, su haddasa fitina kamar yadda suka yi a da (da za su yarda su sake ingiza su ga haka), in kuwa sun yi cewa su ’yan Arewa ne, su ’yan Kudu ne wallahi za a kullace su kuma talaka dole ya zauna lafiya.
A wannan lokaci ina fada muku cewa bayan wannan taron matasa na kungiyoyin Arewa za su zauna domin su shimfida abubuwan da za su yi wa Arewa. Bayan haka za a yi taro na matasan Kudu da na Arewa gaba daya kuma a wannan lokaci ne Kudancin Najeriya za su hadu da Arewacin Najeriya domin a hadu a kuma fahimci juna.
A kuma saka hannu a takardun da za su mayar da Najeriya kasa mai kyau domin zaman lafiya da samun ci gaban kasa. Wannan za a yi shi ne bi izinillah, mun dauke shi da sunan nauyi a kafadarmu kuma da yardar Allah za a yi haka, za a kuma samu wannan fahimtar juna.
Ni ba dan kanzagin kowa ba ne, ni ina kishin kasata ce ina kuma kishin talaka ne ina kuma kishin matasa ne. Ina kishin wadanda ake cutarwa ne . Ni daga inda nake idan kuka duba a yau a Jihar Yobe a cikin kashi 100 kashi 30 ne kawai suke zuwa makaranta. Kashi 70 da suka rage suna gararamba ne ko  a hannun wasu mutane.
Yaran nan suna nan babu makaranta kuma ana cinye hakkinsu babu kuma mai tashi ya ce a’a, wannan cuta ce a gare su. Wadannan abubuwa ne na da, kuma dole su canja dole su canja. Hakkin talaka dole ya je ga talaka, hakkin matasa ya je ga matasa hakkin dattawa sai ya je ga dattawa.
Hakki da kariya na shugabanninmu dole ya je ga shugabanninmu. Hakki ga shugabanni abinda aka dora a kafadarsu dole su yi shi. Dole kuma a tilasta su, su yi.
Arewa bi’iznillah ba za ta fadi a kasa babu nauyi ba. Domin Arewa an san ta da nauyi, Arewa tana da nauyi kuma za ta maido da martabarta.
Ina goyon bayanku a kan wannan tafarki da muka sanya a gaba, muna kuma rokonku don Allah da son Annabi a duk lokacin da muka yi kira, ku amince da mu da abin da muka sanya a gaba na yin gyara. Wadanda ba sa son a yi gyara za su yi fada da mu, mun rigaya mun sani. Amma ni a matsayina na Hamza Al-Mustapha idan kana son ka yi fada da mu duk abin da suke son yi, ni na yarda na zama mai shara a kan titi, idan martabar Arewa da martabar talaka za ta dawo. Wannan shi ne matsayina ba abin duniya ba.
A karshe ina godiya ga ciyaman Babana Dokta Lema Jibiril kan halartar taron nan da ya yi, inda ya kuma yi bayanai masu karfi.

 

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50