Kada da Kifi
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatar ana lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Kada da Kifi.’ Labarin ya yi nuni kan illar rashin bin shawara. A sha karatu lafiya: Akwai wani rafi wanda yake cikin wani daji. A wannan rafi akwai kifi masu yawa a ciki domin mutane ba su san da […]
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatar ana lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Kada da Kifi.’ Labarin ya yi nuni kan illar rashin bin shawara. A sha karatu lafiya:
Akwai wani rafi wanda yake cikin wani daji. A wannan rafi akwai kifi masu yawa a ciki domin mutane ba su san da wannan rafi ba. Kullum kifayen sai su yi ta shawaginsu.
A gefen rafin akwai wani kada wanda a kullum sai ya ba su shawara a kan yadda za su rika tafiyar da al’amurarsu amma kifayen ba su jin maganar. Har suka sa wa wannan kada suna ‘Sarkin bada shawara.’
Ran nan sai wadansu maharba suka fito farautar naman daji kawai sai suka hango rafi. Suka nufi rafi domin shan ruwa sai suka ga kifi makil a ciki. Sai dayansu ya ce sun yi nasara. Daya kuma ya ce su bari zuwa gobe sai su zo da kwandon kamun kifi duk su kame su.
Kada na jin haka ya sake shiga cikin ruwa ya ba kifin shawarar yin hijira amma suka ki. Washegari sai maharban suka dawo suka kwashe kifayen tsab ko daya ba su bari ba. Kifaye suka yi ta da na-sani da sun bi shawarar kada.