Kada dai kilu ta jawo Bau

Tsarin sayar da hannayen jarin masana’antu da hukumomin gwamnati a Nijeriya `ba sabon abu ne ba ne, an dade ana bi ta kansa don a magance matsalolin  da ake cewa suna hana su armashi, ko biyan bukatun da suka sa aka samar da su, amma har yanzu babu wata kwakkwarar nasarar da za a iya […]

Kada dai kilu ta jawo Bau
Kada dai kilu ta jawo Bau

Tsarin sayar da hannayen jarin masana’antu da hukumomin gwamnati a Nijeriya `ba sabon abu ne ba ne, an dade ana bi ta kansa don a magance matsalolin  da ake cewa suna hana su armashi, ko biyan bukatun da suka sa aka samar da su, amma har yanzu babu wata kwakkwarar nasarar da za a iya cewa an cimma game da haka. Daga karshe  sai abin ya zamanto haihuwar guzuma,  da kwance uwa kwance.  
Abin da ke haddasa haka kuwa shi ne rashawar da ta yi katutu a cikin harkar wacce ke hana masu sayen hukumomi ko masana’antun cin moriyarsu, sa’annan kuma dukiyar da gwamnati ta samu wajen sayarwar ta  zame garin banzan da aka yi farau-farau din banza da shi.
Duk da dimbin arzikin da Buwayi Ya huwace wa kasar nan sai ga shi nan ta kasa gudanar da harkokin tattalin arzikinta yadda zai dace da manufofinta na ciyar da kasa gaba da kuma kyautata wa jama’ar cikinta. Maimakon wannan arzikin ya amfani al’ummomin kasar nan sai ya zame masu bala’in da ya haifar da rigngimu da matsalolin da ba su da iyaka, wadanda kuma ba su da magani. Rashin shugabanni nagari ya samar da gwamnatocin da ba su kishin talakawan kasar, sun fi mayar da hankali wajen biyan bukatar iyayen gidansu da ke ketare, wadanda kuma ke shafa masu mai a baki da sunan dimokuradiyya don su dora su bisa tafarkin sace dukiyar kasar nan suna tsibe ta a kasashensu, arzikinsu na kara bunkasa, na wannan kasar kuma na dada bushewa.
Dangane da haka ne Turawa da iyayen gidansu Yahudawa suka dage wajen ganin an gurgunta tattalin arzikin Najeriya, a matsayinta na ‘uwa-ma-ba-da-mama’ ga sauran kasashen Afrikan da ke kiranta ‘Yaya Babba,’ domin kuwa ta haka ne kawai za a iya durkusar da ita, a kuma dakile burinta na ci gaba da jan ragamar Afrika don a share fagen kafa sabon tsarin bautar da al’ummomin nahiyar Afrika. Wannan ne ya sa suka dauki matakai, tare da taimakon lusaran shugabanninmu, wajen ruguza dukkan masana’antun cikin gida da ke samar da irin kayayyakin da ake kerawa a ketare, sa’anan kuma suka bubbude dukkan kofofin antayo kowace irin haja ce daga waje zuwa kasuwannin kasar nan. Ta haka ne jama’ar kasar nan za su kasance cikin bakin talaucin da rashin aikin yi ke haddasawa.
Duk da cewa  hakar Turawa ta cimma ruwa game da haka, ba su hakura ba, sun kwallafa ransu bisa muhimman abubuwa guda biyu wadanda arzikin kasar nan ya dogara kacokan a kansu. Wadanan kuwa su ne ma’aikatar wutar lantarki da kuma matatun man kasar nan. Idan kuma har suka mallaki wadannan gaba daya, to sai abin da Allah Ya yi, domin kuwa sai yadda Turawa suka ga damar yi da kasar. Shi ya sa a ‘yan shekarun baya suka matsa lallai sai an sallama masu rabin dukiyar hukumar wutar lantarki, aka kuma biya masu bukatarsu. Kafin hakan kuwa sai da tsohon Shugaban kasa, Janar Olusegun Obasanjo ya karyar da matatun man kasar nan guda hudu ga Yahudu da Nasara, amma Shugaba Umar ‘Yar’adua da ya gaje shi, ya warware cinikin saboda ganin cewa kwarar da aka yi wa mutanen Najeriya ta yi yawa.
To shi ne kuma a halin yanzu ake son sake sayar da wadannan matatun man,  nan da watanni hudu masu zuwa, kuma  Yahudu da Nasaran da suka danne wa  Gwamnatin Goodluck Jonathan kan maciji, shi da ‘yan koren Amurka na ta wasa da wutsiyar,  za su fi amfana da haka. Idan har aka yi hakan to komai zai tsaya cik a Najeriya, domin kuwa wadannan matatun man ne ke samar da iskar gas da ake sarrafawa a wuraren samar da wutar lantarki da kuma bakin man da ke amfani da shi don juya na’urorin manyan masana’antun kasar nan, wadanda tuni suka kwanta da siradansu. Ashe ke nan danka matatun man kasar nan ga Yahuduwa da manyan ‘yan korensu zai ba su damar tauye  ci gaban masana’antu da sauran sabgogin da suka jibanci habaka tattalin arziki domin kuwa cikin ruwan sanyi suna iya kin samar da iskar gas din da za ta murda wadancan na’urorin samar da wutar lantarkin da kuma bakin man da ake matukar bukata a masana’antu..
A yanzu haka  Yahudu da Nasara na amfani da ‘yan korensu a nan cikin gida wajen sayen masana’antu da kamfanoni wadanda daga baya sukan rufe, ba su yin wani aikin da zai taimaki jama’a. Baicin haka nan kuma a yanzu ‘yan koren Turawa sun zake wajen shigo da tataccen man fetur daga ketare, a sabili da haka ne kuma suka dage wajen hana matatun guda hudu  yin aiki. To wace hujja ce za ta tabbatar cewa idan an sayar da matatun man kasar nan ba za a bari su zame saura ba? Kada dai kilu ta jawo Bau, ko garin gyaran gira a rasa ido.