Kada dai sabuwar Masana’antar Takin Dangote ta zama inuwar giginya

A ranar 22 ga watan Maris da ya gabata ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci bikin bude katafariyar masana’antar takin zamani mafi girma a Nahiyar Afirka ta Dangote a rukunin Masana’antu na Lekki da ke Legas. Masana’antar da aka gina a kan zunzurutun kudi har Dalar Amurka biliyan biyu da rabi ($2.5biliyan). A matakin […]

Kada dai sabuwar Masana’antar Takin Dangote ta zama inuwar giginya

Lokacin da Buhari ya kaddamar da masana’antar Takin zamani ta Dangote a Legas

A ranar 22 ga watan Maris da ya gabata ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci bikin bude katafariyar masana’antar takin zamani mafi girma a Nahiyar Afirka ta Dangote a rukunin Masana’antu na Lekki da ke Legas.

Masana’antar da aka gina a kan zunzurutun kudi har Dalar Amurka biliyan biyu da rabi ($2.5biliyan). A matakin farko za ta rika samar da tan miliyan uku na samfurin takin Urea duk shekara.

Takin zamani a ’yan shekarun nan ya zama mai kamshin turare dan goma, kasancewar yana wahala, sannan kuma ga shi da dan karen tsada, duk kuwa da irin matukar muhimmancin da yake da shi wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan ta fannin noma, tunda takin gargajiya ya zama mai wahalar samu.

Hakan ta sa duk shekara musamman ga manoman damina, manoma na dari-darin yin shuka, alhali ba su san inda za su samu wadataccen takin zamani ba. Ko shakka babu, wannan ya kara kawo koma baya a kan abin da manoman kasar nan kan noma, baya ga annoba irin ta fari (karancin ruwan sama) da farin dango da makamantan annobar damina da a kan samu.

Ka ga ke nan mai karatu ba sai an fada ba, a duk lokacin da aka ce an samu karin wata masana’antar yin takin zamani a kasar nan, wani babban abin murna ne ga mahukunta da masana tattalin arziki musamman a fannin noma da kiwo, bare kuma uwa uba ga manoman kansu.

An ga Shugaba Buhari lokacin da yake jawabi wajen bude masana’antar yana cike da farin ciki da annashuwa a kan
samuwarta, yana mai cewa ko shakka babu za ta yi matukar bunkasa ayyukan yi da cinikayyar masana’antu da fannin sufuri, wadanda gaba dayansu za su bunkasa arziki da rage talauci da ma kyakkyawar makoma ga kasar nan.

Shugaba Buhari, ya yi fatan samun wannan masana’anta zai haifar da samun wadataccen takin zamani ga manoman kasar nan, ta yadda manoman da suke noma kananan gonaki a kan fargabar rashin taki, yanzu za su rika noma manya-manyan gonaki a zaman noma don riba. Ya yi kuma fatan nan gaba kadan, dukkan dogaron da kasar nan take a kan shigo da kayayyakin gona don sarrafa wa zai zama abin tarihi.

Shi kuwa Gwamnan Babban Bankin kasa, Mista Godwin Emefiele, a nasa jawabin, cewa ya yi zuwan Masana’antar a wannan lokaci, faduwa ce ta zo daidai da zama, idan aka yi la’akari da irin yadda yanzu a kasuwar duniya farashin alkama da man fetur da shi kansa takin zamani suka tashi da kashi 20 cikin 100, a sanadiyar yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine.

Da yake nasa jawabin shugaban masana’antar Alhaji Aliko Dangote hamshakin attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, cewa ya yi aniyarsu ita ce, su samar da ingantaccen takin zamani ga manoman kasar nan, wanda haka zai inganta ayyukan gona da kara kyakkyawar yabanya.

Shi ma tsohon Ministan Ayyukan Gona, yanzu kuma Shugaban Bankin Raya kasashen Afirka, Mista Akinwumi Adesina, da tun kafin bude Masa’antar ya samu ziyartar shi da ’yan Hukumar Daraktocin Banki, ya yi hasashen cewa tan miliyan uku na takin da masana’antar za ta rika yi, zai wadaci kasar nan, har ma ta rika fitar da wani zuwa kasashen waje.

Mista Adesina, ya yi nuni da irin yadda kasar nan a baya take shigo da siminti, amma da jajircewar masana’antun siminti na cikin gida, yanzu kasar nan ta zama mai fitar da siminti zuwa kasashen waje.

Daga karshe ya yi fatarn takin na Dangote zai zama mai rahusa da ingancin da ake bukata. Haka dai aka yi ta jawabin yabo da godiya da tabbacin samun wadataccen taki a kasar nan, wanda su manoman kasar nan manya da kanana suka dade suna fatan samu.

Amma sai dai kash! Akwai fargaba ga manoman a kan yiwuwar samun takin a wadace kuma cikin farashi mai rangwamen da ya kamata, kamar yadda aka ji Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Manoman Najeriya (AFAN), Alhaji Kabir Ibrahim a lokacin bikin bude masana’antar yana bayyana cewa, “takin na Dangote zai kara taimaka mana wajen kara samun hakakar yabanya, don haka abin a yi maraba da shi ne don zai taimaka wajen cikasa gibin karancin takin da ake fama da shi.”

Ya ci gaba da cewa, “rashin taki ba karamar barazana ba ce ga manoma, don haka muna murna da bude wannan masana’anta, da fatan samun saukin farashin takin, bisa ga la’akari da irin karfin saye na manoman kasar nan.” Inji shugaban.

Kamar dai yadda aka bayyana a wajen bikin, tuni masana’antar ta fara fitar da takinta zuwa kasashe irin na Amurka da Indiya da Brazil, har ma ana kiyasin za ta rika samo wa qasar nan kudaden shiga har Dalar Amurka miliyan 62 ($625miliyan), duk shekara.

Dama dai an gina masana’antar ce a rukunin masana’antun da suke da izinin fitar da kayayyakin da suka sarrafa zuwa kowace duniya cikin tsarin biyan kudin fito mai sauki. Ba ma wannan ba, dubi siminti duk da ana cewa muna yin wanda zai wadace mu, amma kuma tsadarsa ta fi karfin talaka. Haka kuwa yana faruwa a kan irin yadda masu masana’antun yin simintin suke ta rige-rigen fitar da shi zuwa kasashen makwabtanmu irinsu Ghana da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi.

Ziyara kan iyakokinmu a kullum zai tabbatar wa da mai karatu hakan. Ko kusa ba laifi ba ne masana’antunmu su yi kayayyakinsu su kai makwabtanmu, don mu ma ana kawo mana nasu, amma inda yake zama laifi ko in ce jari hujja, shi ne yadda kasa ba ta koshi ba amma a rika kwashewa ana kai wa kasashen waje da sunan a ci kazamar ribi. A nan ya kamata mahukuntan kasar nan su rika taka wa masu irin wannan halayya burki ko a rika sama wa talakawan kasa sa’ida. Da fatan kar wannan masana’anta ta zama inuwar giginya ga manoman kasar nan.

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira