Kada gwamnati ta hana shigo da taki daga waje – Bala Jingir
Garkuwar Al’ummar Hausawa da Fulani na yankin Pengana kuma Sarkin Noman Karamar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato Alhaji Ya’u Bala Jingir ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya cewa kada ta hana shigo da takin zamani daga kasashen waje. Alhaji Ya’u Bala Jingir ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya, […]
Garkuwar Al’ummar Hausawa da Fulani na yankin Pengana kuma Sarkin Noman Karamar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato Alhaji Ya’u Bala Jingir ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya cewa kada ta hana shigo da takin zamani daga kasashen waje. Alhaji Ya’u Bala Jingir ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya, inda ya ce, wannan kira ya zama wajibi, saboda rade-radin da ake yi cewa, kamfanonin yin takin zamani na Najeriya suna ta kokarin ganin gwamnati ta hana shigo da taki daga kasashen waje.
Alhaji Ya’u Bala ya ce, “Hana shigo da taki daga waje za ta jawo babbar matsala ga manoman Najeriya. Domin kamfanonin takin da muke da su, ba za su iya wadata manoman da taki ba. Kuma ba sa yin taki ingantatce, suna hada abubuwan da suka ga dama ne kawai a takin da suke yi. Don haka bai kamata gwamnati ta hana shigo da taki daga waje ba.”
“Takin da ake shigowa da shi daga waje ne kawai yake da inganci. Kamfanonin taki na Najeriya ne suke son a hana shigo da taki daga waje. Bayan takin da suke yi ba ya da kyau, babu shakka idan aka dogara da takin da ake yi a Najeriya, noma ba zai inganta ba,’’ inji shi.
a yi kira ga gwamnati ta samar da taraktocin noma da takin zamani ga manoma. Kuma ta sayi amfanin gona daga hannun manoma ta ajiye don bacin rana da rage wa manoma asara, domin yin haka zai dada bunkasa harkokin noma a Najeriya.