Kada gwamnatin Katsina ta dauki nauyin da ba ta iya saukewa – Sarkin Daura
Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Farouk Umar Farouk ya ja hankalin gwamnatin Jihar Katsina cewa kada ta dauki nauyin da zuwa gaba zai gagare ta saukewa. Sarkin ya yi wannan jan hakali ne ga Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Bello Masari lokacin da kwamitin tantance wadanda suka kammala karatu a manyan cibiyoyin ilimi da ba su […]
Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Farouk Umar Farouk ya ja hankalin gwamnatin Jihar Katsina cewa kada ta dauki nauyin da zuwa gaba zai gagare ta saukewa.
Sarkin ya yi wannan jan hakali ne ga Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Bello Masari lokacin da kwamitin tantance wadanda suka kammala karatu a manyan cibiyoyin ilimi da ba su da aikin yi a jihar suka kai masa ziyarar girmamawa a fadarsa a ranar Talatar da ta gabata.
Sarkin wanda ya yaba wa gwamnatin na yunkurin ceto rayuwar matasa. “Gaskiya ba karamin tunani wannan gwamnati ta yi ba, wadda dama mun san gwamnati ce ta taimakon jama’a. Wannan shiri kamar yadda muka ji shi, yana da kyau a koya wa matasa sana’o’i domin dogaro da kansu. Sai dai a nan sai an yi taka-tsantsan musamman batun bashi da aka ce za a rika bayarwa ga wadanda aka tantance, saboda kada nan gaba abin ya gagari gwamnati cika wannan alkawari, saboda yawaitar mabukata ko karancin kudi. Kowa ya san ana fama da matsala a yanzu a kasar nan. A koyar da su yadda za su nemi kudin shi ne mafi alheri. Saboda haka, muna murna da wannan tsari, kuma masarauta a shirye take da bayar da duk wani tallafin da ake bukata,” inji Sarkin.
Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdullmumin Kabir Usman cewa ya yi tuni ya bayar da umarni ga hakimai su kafa kwamitin da ya yi kama da wannan. “Saboda haka ina ganin ni ne gwamnati ta taimakamawa domin ceto rayuwar al’ummata. Mun san rashin aikin yi ne jagaban faruwar duk wata matsala ta tsaro da ake samu a kasar nan. Amma da zarar jama’a musamman matasa na da abin yi za a ga duk wata matsala ta rashin tsaro ta kaura. Sai dai kamar yadda ake kokarin bullo da shirin, yana da kyau a ci gaba da fadakar da jama’a a kan muhimmancin kwamitin da irin aikin da za su yi. Kada a yi zaton wasu ayyuka ne gwamnati za ta ba da, a’a za a koya wa mutane yadda za su dogara da kansu ne,” inji Sarkin Katsina.
Tun farko shugaban kwamitin kuma mai bai wa Gwamna Shawara ta Musamman a kan Samar da Aikin yi, Alhaji Husaini Adamu Karaduwa ya shaida wa sarakunan cewa sun kawo ziyarar ce domin neman shawarwarinsu a kan wannan yunkuri na gwamnati na tallafa wa wadanda suka kammala karatun gaba da sakandare domin dogaro da kansu.
Ya ce, kwamitin zai zagaya sassan jihar domin gano wadanda lamarin ya shafa kuma dole kwamitin ya bi ta hannun sarakuna domin su ne iyayen al’umma.
Aikin kwamitin dai shi ne bincikowa da daddale yawan matasan, domin bullo da hanyar da za a taimaka musu ciki har da ba su rancen kudi domin gudanar da sana’o’i bayan an koya musu ko kara wa masu sana’o’i a cikinsu jari.