Kada ka gaya wa kowa
Wani saurayi ne dan kasuwa mai gaskiya da amana, wanda kayansa ma farashi daya yake fadi na gaskiya, kuma duk kasuwar babu mai saukinsa. Ran nan ya kasa kaya, sai ga wani tsoho ya zo ya taya, ya ce masa, “gaskiya nawa wannan, ka fada mini gaskiyar farashinsa na ainihi.” Matashi ya ce: “Gaskiya fa […]
Wani saurayi ne dan kasuwa mai gaskiya da amana, wanda kayansa ma farashi daya yake fadi na gaskiya, kuma duk kasuwar babu mai saukinsa. Ran nan ya kasa kaya, sai ga wani tsoho ya zo ya taya, ya ce masa, “gaskiya nawa wannan, ka fada mini gaskiyar farashinsa na ainihi.” Matashi ya ce: “Gaskiya fa ka ce, idan na gaya maka babu tayi fa, domin gaskiya daya ce.” Tsoho ya ce a gaya masa gaskiyar. Yaro ya ce masa kudinsa Naira 1000. Sai tsohon ya ce: “Kawo kunnenka in gaya maka wani abu.” Yaro ya karkata, sai tsoho ya rada masa cewa Naira 950. Shi kuma saurayi sai ya ce wa tsoho, kawo kunnenka ka ji. Da ya mika masa sai ya rada masa cewa: “Amma dai kai akwai tsohon banza, amma kada ka gaya wa kowa!”
Daga Alhaji danladi China, Kano, 08034463170