Kada karatun boko ya zama matsala ga aure -Gimbiya A’isha
Hajiya A’isha Al-amin Ibet Tom Gimbiyar Matan Shuwa Arab a Legas a kwanakin baya ne aka ba ta wannan sarauta saboda gudunmawar da take baiwa ‘yan uwanta mata musamman mazauna Legas. A zantawarta da Aminiya ta bayyana matakan da ya kamata a bi don ganin a samu karkon zamantakewar aure da kulawa da tarbiyar iyali. Tarihina: […]
Hajiya A’isha Al-amin Ibet Tom Gimbiyar Matan Shuwa Arab a Legas a kwanakin baya ne aka ba ta wannan sarauta saboda gudunmawar da take baiwa ‘yan uwanta mata musamman mazauna Legas. A zantawarta da Aminiya ta bayyana matakan da ya kamata a bi don ganin a samu karkon zamantakewar aure da kulawa da tarbiyar iyali.
Tarihina:
Sunana Hajiya A’isha Al’amin Ibet Tom, Ni haiffafiyar Jihar Barno ce, mahaifi na dan Ganborun Gala ne mahaifiyata kuma ’yar asalin Kamaru ce, kuma mu kabilar Shuwa Arab mazauna Dambuwa ne. Ina da kimanin shekaru 9 aka kawo ni Legas yau kimanin shekaru 38 ke nan bayan da iyayena suka dawo da zamansu Legas. Ban yi karatun boko ba amma na dan taba karatun addini domin a wancan lokaci babu makarantun Islamiya a yankin da muke a Legas sai dai iyayenmu kan dauko malamai daga Maiduguri su zo su koyar da mu a gida. Sannan iyayena sun yi mini aure a lokacin da nake da shekaru 14. Kuma a wannan lokacin ni ce ta biyu a wajan maigidana kafin daga bisani ya kara aure mu zama mu 3, Kuma Alhamdulillahi na samu ribar zaman gidan aure da albarkarsa domin kawo yanzu na aurar da ’ya’ya mata 4 da namiji guda sannan ragowar na cigaba da karatun su, wasu a Arewacin kasar nan wasu a kasar Amurka a kwai dana da a yanzu haka ya fara aiki a kasar Amurka domin na haifi ’ya’ya 11 ne maza 5 mata 6. |
Kamar Yadda kika bayyana an yi mi ki aure a lokacin da kike da karancin shekaru ko haka ya janyo kin fuskanci wata matsala?
A Gaskiya ban fuskanci wata matsala ba domin na yi haihuwa ta duka ban fuskanci wata matsala ba sannan ban taba yin yaji ba a tsawon shekaru arba’in da wani abu na aure na ba, to Alhamdulillahi na samu arziki da ake nema a ribar aure.
Babbar matsalar da kan ci wa al’ummar Arewacin kasar nan tuwo a kwarya ta fuskar zamantakewar aure ita ce yawan mace-macen aure ko me kike ganin ya kan janyo hakan?
Sau da yawa mutane na alakanta yawan mutuwar aure da sauyin zamani amma alal hakika mutanen da, da na yanzu kusan duk daya ne ta wannan fuska domin ko a ’ya’ya na akwai ’ya ta da na aurar tana da shekaru 14 ba ta taba kawo min korafi ba. Hakazalika maigidanta bai taba kawo karar ta ba, don haka babu hujjar alakanta yawaitar mutuwar aure da zamani aa wannan abu ya danganta da mutum ne da kuma tarbiyyar da aka yi masa tun a gida, domin shi zaman aure idan ka san halin mutum ne sai ka ci maganin zama da shi, kuma abin ba a karatun boko yake ba, domin akwai wasu matan da suke jin don sun yi karatun boko mai zurfi sai su rika daukar kansu daidai da maza wannan abu ma kan kawo matsala a zamantakewar aure. Shawarar da zan ba mata ’yan uwana da ‘ya’yanmu su sani shi zaman aure hakuri ne in ka ci abinci da hannun dama ka sude dole ne ka hada da na hagu ka cude ka wanke don in ba ka hada da na hagun ba, ba zai wanku ba, abin da nake nufi a nan in ka ce ko wani abu namiji ne zai yi maka kuma dole shi ne zai yi hakuri da ke, ke ba kya yin uziri ba kya hakuri to dole ne a samu matsala, don haka sai mun rungumi hakuri da kawaici da kau da kai kafin mu kai ga cinmma nasara, domin yawanci ana samun laifin ne daga wajanmu mata, saboda duk namijin da ya auro mace yana son ta ne, za ka ga har akwai matan da sukan bukaci namiji ya sake su duk wannan abu ne mara kyau. Su ma mazan a nasu bangaren dole ne su yi hakuri donmin ita mace Allah Ya hallice ta da rauni, akwai lokacin da iyayenta ne ke kulawa da ita da daukar dawainiyarta har ta kai lokacin da za ta zamo a karkashin kulawar maigidanta kafin daga bisani ’ya’yan da ta haifa su ja ragamar kulawa da ita idan ta tsufa don haka mu mata tun daga farkon mu har karshen mu muna karkashin kulawar maza ne don haka dole ne mace ta yi kasa da kanta ta yi biyayya don a zauna lafiya. Kuma maganar yin aure da wuri wannan ba matsala ba ne, hasalima shi ne mafi alkhairi don na gani a kaina da a kan ’ya’yana. Babban abin lura shi ne bada kyakyawar tarbiyya da dacewa da suruki nagari. Kana mafiya yawan abubuwan da kan janyo tashin hankali da fituntunu a iyali musanmman inda ake da mace fiye da daya sakaci ne na maigida. A bangarena ba mu taba fuskantar irin wannan ba kasancewar duka mu ukun kowacce da gidanta daban tare da ’ya’yanta duk da dai ba kowa ba ne Allah Ya hore wa ikon yin haka ba domin tsawon yatsun hannunmu ma ba daya ba ne, amma daidai gwargwado kowa ya kamata ya tafiyar da lamarin sa yadda ya dace.
Wani mataki kike ganin ya kamata a dauka don magance yawan mutuwar aure a kasar Hausa?
Idan ka lura sauran kabilun kasar nan ba sa fuskantar wannan matsalar kamar mu ’yan Arewa, ya kamata a rungumi akidar yin hakuri da juna, matan mu kuma su rika taimakon mazajen auren su don haka yana da kyau mace ta yi sana’a sannan ta rika taimakon mijinta ta wata fuskar ba wai ta tara kudinta a asusuba sai dai kanta kawai ta sani. Wata za ka ga ta kudiri aniya a cikin kudin cefane za ta sayi fili ta yi gini sannnan duk shekara sai ta je aikin Hajji wanda mijinta ya kai ta bai ishe