Kada ku bata ayyukanku (1)
Masallacin Sheikh Bin Baz Riyad, Saudiyya Huduba ta farko: Hamdala da taslimi. Bayan haka, ya ku ’yan uwan imani! dan Adam yakan wahala ya yi aiki, ya yi kokari ya wahalar da ransa, ya tsara ya aiwatar ya shirya ya daidaita, yana neman dukiyarsa yana daddale kasuwancinsa. Hakika ya keta duk wani fage na zato […]
Masallacin Sheikh Bin Baz Riyad, Saudiyya
Huduba ta farko:
Hamdala da taslimi.
Bayan haka, ya ku ’yan uwan imani!
dan Adam yakan wahala ya yi aiki, ya yi kokari ya wahalar da ransa, ya tsara ya aiwatar ya shirya ya daidaita, yana neman dukiyarsa yana daddale kasuwancinsa. Hakika ya keta duk wani fage na zato da mafarkinsa, ya shisshirya ya rurrubuta, sai dai kuma duk da haka kibiyar asara ta auka masa, duk abin da ya tara ya tafi ya bar shi da wahala. Ya kasance kamar kura da ta bi iska ta bar shi da buri da tsammani, ya komo ba ya da komai na dukiya ko abinci face dan abin da ba a rasa ba. Tabbas a bayan aukuwar haka ba sai an tambayi yadda halinsa ya jirkita ba da yadda zuciyarsa ta yi kunci ba da yadda rayuwarsa ta shiga kunci, lafiyarsa ta ragu ko ma ta rikice ba.
Idan wannan dukkansu suna faruwa da wanda ya rasa ’yan kayayyakin duniya masu gushewa da ni’ima mai karewa, don Allah, me za ku ce game da halin asara ta hakika wadda idan ta auku, sai aukuwarta tazo tare da tabewa da bala’i?
Muna neman tsarin Allah daga bacin ayyukan kwarai, don haka babu abin da ya fi dacewa da mu fiye da kula tare da kare ayyukanmu da ladaddakinmu daga yi ayyukan sabo da za su bata su ko su illata su.
Yana da kyau a yi magana a kan tsare ayyukan kwarai da na alheri da bayin Allah suke yi domin su dace da shiriya da abin da yake daidai. Domin haka kiyaye aiki a bayan aiki, shi kansa aiki ne na kwarai, aiki ne na da’a kuma shi ne ke nuna cewa mutum ya tsayu a kan daidai tare da samun kyakkyawar ijaba. “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi da’a ga Allah, kuma ku yi da’a ga ManzonSa, kuma kada ku bata ayyukanku.” (Muhammad: 33).
Hakika taka-tsantan don guje wa aukawa cikin miyagun ayyuka da sharri wadanda suke iya bata ayyuka da lada, sunnah ce da Sahabin nan mai girma Huzaifa bin Yamani (RA) ya sunnanta lokacin da ya ce: “Mutane sun kasance suna tambayar Manzon Allah (SAW) a kan alheri, amma ni sai na rika tambayarsa a kan sharri, saboda tsoron kada ya riske ni.” (Buhari).
Idan aka tambaye ku kan mafi girman mugun aiki da ke rusa kyawawan ayyuka ya sanya su zama kura abar watsarwa me za ku ce? To shi ne mugun aikin nan da Allah Madaukaki Ya ambce shi da zalunci mai girma, wato yin shirka da Allah. Shirka ita ce mafi girman fasadi da take jawo barna a bayan kasa, kuma ba a karbar aikin da’a ko ciyarwa na neman lada daga ma’abucinta. “Lallai ne, Allah ba Ya gafarta a yi shirki game da Shi…” (Nisa’i: 48). Kuma yana daga cikin yin shirki ga Allah bawa ya sarrafa wani nau’i daga cikin nau’o’in ibada ga wanin Allah, duk wanda ya kira wanin Allah, ko ya yi yanka ga wanin Allah ko ya yi bakace da wanin Allah, ko ya yi isti’aza (ya nemi tsari) da wanin Allah, hakika aikinsa ya baci kuma aikinsa ya lalace. “Kuma da sun yi shirki da hakika abin da suka kasance suna aikatawa ya lalace.” (Al-An’am: 88).
Haka yin aiki da riya don a nuna wa ababen halitta ko sum’a, a jiyar da mutane kan kyawawan ayyuka da aikin neman lada, suna sa aiki ya baci a ki karbarsa. Abin da ke tabbatar da haka fadin Allah Madaukaki a cikin Hadisin kudusi sahihi cewa lallai Allah Madaukaki zai ce da masu yin aiki domin a gani (riya) a Ranar kiyama: “Ku je zuwa ga wadanda kuke nuna musu a duniya, ku gani ko za ku samu sakamako a wurinsu.” (Imam Ahmad da wadansu suka ruwaito).
Ba haka ba, hakika riya ba ma aiki kawai take batawa ta lalata ba, har ma takan sanya ma’abucinta ya yi kuka da bakin ciki a Ranar kiyama. Shin akwai wani aiki mafi girma daga aikin mai jihadi ko malami ko mai ciyar da dukiyarsa? Wadancan idan niyyarsu ta baci suka yi nufin nuna wa abin halitta (mutane), za su kasance su ne zubin farko na mutanen da za a kone a wuta, -Allah Ya yi mana tsari- kamar yadda labari ya inganta daga Shugaban Halitta (SAW).
Ya ku bayin Allah! Barin yin umarni da alheri da hana abin ki da kaurace wa yin nasiha da kin masu yin wadannan ayyuka, sabubba ne na jawo fushin Allah a kan daukacin jama’a da kuma la’anar Allah. FushinSa ya sauka a kan Bani Isra’ila ne saboda sun kasance ba su hani daga abin ki da suka aikata shi, kuma tir da abin da suka kasance suna aikatawa. Kuma aikata abin da zai fusata Allah Mabuwayi, sababi ne daga cikin sabuban batawa da lalata aiki. Allah Madaukaki Yana cewa: “Wannan, domin lallai su, sun bi abin da ya fusatar da Allah, kuma sun ki yadarSa, saboda haka Ya bata ayyukansu.” (Muhammad: 29).
A duk lokacin da rayukan mutane suka baci, suka koma son zuciya suka saba wa fidirar Allah, suka ki aiki da hukunce-hukunce shari’a suka juya wa shari’o’in Musulunci baya, ko suka ki wani abu da Manzon Allah (SAW) ya zo da shi daga cikin sunnoninsa na magana ko aiki, to wadannan suna daga cikin mafiya hadari kofofin da suke jawo baci da lalacewar ayyukan kirki. Allah Madaukaki Yana cewa a kan wadanda suke kin shari’a da hukunce-hukuncen da Ya saukar: “Wannan, saboda lallai su, sun ki abin da Allah Ya saukar, domin haka Ya bata ayyukansu.” (Muhammad: 9).
Imani da kuma kin abin da Shugaban ’ya’yan Adam Annabi Muhammad (SAW) ya zo da shi, ba su haduwa a zuciya daya. “Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi imani ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya saba a tsakaninsu, sa’an nan ba su samu wani kunci a cikin zukatansu ba daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamawa.” (Nisa’i: 65).
Ya ku muminai! Yin ridda daga addini tana rusa duk wani aikin kwarai da ya gabace ta, kuma saboda hadarinta da illarta ga mutum shi kadai da al’umma da kuma addini, ya sa malamai suka tsoratar a kanta a cikin littattafan tauhidi da fikhu. Kuma yana daga cikin ridda mutum ya yi inkari (musu ko ya ki) abin da aka sani a cikin addini bisa lalura, kamar ya halatta barin Sallah ko Zakka, ko ya inganta akidojin kafirai ko ya ce ya halatta a bi wani addni ba addinin Musulunci ba. Haka wanda yake ganin wasu tsare-tsare na batattu kamar tsarin Gurguzu da na Jari-Hujja da sauran tsare-tsare na gwamnati da na tattalin arziki sun fi na shari’ar Musulunci wajen inganta rayuwa duk suna jawo ridda.
Har wa yau yana daga cikin ridda tozarta wani hukunci na addini ko tsarin shari’ar Musulunci, ko zaton cewa wannan zamani na ci gaban dan Adam bai dace a dabbaka shari’ar Musulunci a cikinsa ba. Hakika fadin haka wani al’amari ne na cin zarafin Musulunci da tuhumarsa da cewa shi wani tsari ne da yake nakasasshe kuma ya gaza.
Kuma mafi hadarin kofar ridda wadda ta fi saurin jifa mutum ga ridda, ita ce izgili da wata alama ta shari’a ko izgilanci ga hukunce-hukuncen Musulunci. Allah Yana cewa ga masu izgilanci: “Shin da Allah da kuma ayoyinSa da ManzonSa kuka kasance kuna izgili? Kada ku kawo wani uziri, hakika, kun kafirta a bayan imaninku…” (Tauba: 65-66).