Kada ku damu kan batun kafa ’yan sandan jihohi —Sufeto-Janar
Ya ce babu dalilin da zai sa jami’ai fargaba game da makomar aikinsu sakamakon tattaunawar da ake yi kan batun kafa ’yan sandan jihohi.
Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu, ya tabbatar wa jami’ai da ma’aikatan rundunar cewa shirin kafa ’yan sandan jihohi ba zai kawo ƙarshen rundunar ’yan sanda ta ƙasa ba.
Disu ya bayyana haka ne a ziyararsa ta farko a hukumance ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa a ranar Litinin. Ya ce babu dalilin da zai sa jami’ai fargaba game da makomar aikinsu sakamakon tattaunawar da ake yi kan batun kafa ’yan sandan jihohi.
“Na san cewa jami’ai da dama suna da tambayoyi da damuwa, wasu ma suna cikin fargaba dangane da wannan batu. Amma ina tabbatar muku cewa kafa ’yan sandan jihohi ba ya nufin rusa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya. Rundunar za ta ci gaba da kasancewa,” in ji shi.
Ya bayyana cewa a lokuta da dama ana tattauna batutuwan da suka shafi aikin ’yan sanda ba tare da an bai wa rundunar damar bayar da gudunmawa ba, lamarin da ya haifar da matsalolin da ake fuskanta a yanzu.
Disu ya yaba wa jami’an Rundunar ’Yan Sandan Jigawa bisa ƙwazo, sadaukarwa da ƙwarewar da suke nunawa wajen gudanar da aikinsu. Ya ce ya gamsu da irin ƙoƙarin da suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro, musamman a ɓangaren hana laifuka, tattara bayanan sirri da hulɗa da jama’a.
Ya kuma jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar, yana mai cewa hakan alama ce ta yadda ake aiki tare domin tabbatar da tsaro.
Sufeto-Janar din ya ƙara tabbatar wa jami’an cewa shugabancin rundunar na ci gaba da ƙoƙarin inganta walwala, samar da kayan aiki da ƙarfafa ayyukan jami’ai domin su gudanar da aikinsu yadda ya kamata. Ya buƙace su da su ci gaba da kasancewa cikin shiri, nuna ƙwarewa da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ziyarar wani ɓangare ne na rangadin da yake yi a fadin ƙasar nan domin ganawa kai tsaye da jami’an rundunar, tantance ƙalubalen da suke fuskanta da kuma ƙarfafa ƙudurinsa na gina rundunar ’yan sanda mai inganci, kusanci da jama’a da kuma kwarewa.