Kada matasan Tijjaniyya da kadiriyya su dauki doka a hannunsu – Sheikh Sahihi
Wani fitaccen malamin addinin Musulunci da ke Gusau a Jihar Zamfara, Sheikh Mustafa Sahihi ya bukaci matasan darikun Tijjaniya da kadiriyya da kuma Musulmin kasar nan baki daya da kada su dauki doka a hannunsu, su tsaya su ga matakin hukumomi da shugabanni za su dauka a kan wadanda suka yi batanci ga Manzon Allah […]
Wani fitaccen malamin addinin Musulunci da ke Gusau a Jihar Zamfara, Sheikh Mustafa Sahihi ya bukaci matasan darikun Tijjaniya da kadiriyya da kuma Musulmin kasar nan baki daya da kada su dauki doka a hannunsu, su tsaya su ga matakin hukumomi da shugabanni za su dauka a kan wadanda suka yi batanci ga Manzon Allah (SAW) a Kano.
Shehin Malamin ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wa’azinsa a wajen majalisin da kungiyar Mukaddamai da Halifofi ta Jihar Zamfara ta shirya don bayyana matsayinsu a kan wadanda ake cewa ’yan Tijjaniya ne da suka yi batanci a kan Manzon Allah a wajen maulidin Sheikh Ibrahim Inyas. An gudanar da majalisin ne a ranar Alhamis din makon jiya a garin Gusau babban birnin Jihar Zamfara.
Sheikh Sahihi ya kara da cewa babban abin bakin cikinsu shine yadda ake cewa wai ’yan Tijjaniya ne, ya ce ba ’yan Tijjaniya ba ne domin duk mabiyin Sheikh Ahmadu Tijjani ba zai yi batanci ga Manzon Allah ba, saboda abin da ake nufi da dan Tijjaniyya shi ne almajirin Shehu Ahmadu Tijjani, kuma biyayya ga Shehu shi ne yarda da Alkur’ani da Sunna. Ya kara da cewa Shehu Ahmadu Tijjani ya ce duk wanda ya yi aikin da ya ci karo da Alkur’ani da Hadisi ya yi ridda.
Sheikh Sahihi ya ce bisa ruwayoyin Imamu Malik, tunda mu a nan kasar Malikiyya muke bi duk wanda ya zagi sahabi a zane shi, ma’ana a yi masa bulala, kuma duk wanda ya zagi Manzon Allah jininsa ya halitta, ba tare da wani sassauci ba, kuma koda ba Musulmi ba ne. Ya kara da cewa bisa hujjojin addinin Musulunci na kowace mazhaba wanda duk ya bata ko ya zagi Manzon Allah to, ya halitta a kashe shi. “Bisa wadannan dalilai da wasu muna kira da babban murya ga gwamnatin Jihar Kano da shugabanni da masu ruwa da tsaki na jihar da kuma kasar nan, su dauki matakin da ya dace a kan wadanda suka yi batanci ga Annabi, matakin shi ne yanke wa wadannan mutane hukuncin da ya dace da su wato kisa cikin gaggawa,” inji shi.
Sheikh Mustafa Sahihi ya nemi al’ummar Musulmi musamman matasa da kada su rika daukar doka a hannu, su rika dakatawa don jin abin da hukuma za ta yi, domin a cewarsa idan ba,a bi doka ba, zai zama an aikata abin da ya saba wa karantarwar Sheikh Ahmad Tijjani da Sheikh Ibrahim Inyas da kuma shi kansa addinin baki daya.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne aka wasu da suke kiran kansu ’yan Tijjaniya suka yi munanan maganganu a kan Manzon Allah a Kano, wanda ya yi sanadiyar kone wata kotu a Kano.