Kada mu yanke kaunar cin nasara a rayuwa (2)

Kamar yadda muka saba, yau ma Allah Ya sake kawo mu wani makon, kuma za mu ci gaba da kawo muku tambihi game da sinadaran yaukaka rayuwa. Jama’a, ina yi maku sallama, Assalamu alaikum. Za mu ci gaba daga inda muka tsaya, a maudu’in da muka faro makon jiya: Naci; Hausawa sun ce damben kuturu […]

Kada mu yanke kaunar cin nasara a rayuwa (2)
Kada mu yanke kaunar cin nasara a rayuwa (2)

Kamar yadda muka saba, yau ma Allah Ya sake kawo mu wani makon, kuma za mu ci gaba da kawo muku tambihi game da sinadaran yaukaka rayuwa. Jama’a, ina yi maku sallama, Assalamu alaikum. Za mu ci gaba daga inda muka tsaya, a maudu’in da muka faro makon jiya:

Naci; Hausawa sun ce damben kuturu ne. To, lallai ita rayuwa tana bukatar naci, domin babu wani kalubale da zai kauce daga hanyarka, dole sai ka yi nacin kawar da shi. Muddin kuwa aka sanya naci kan yin duk wani abu, komai wahalarsa, wata rana zai zama labari, za a cim masa. Misali, idan kai dalibi ne, kana koyon wani karatu, za ka fuskanci kalubale da zai kawo maka wahala a zuciya da kwakwalwa, wanda kuma zai kawo maka tarnaki ga koyon wannan karatu. Babu mamaki ma ka ji cewa ba ka kaunar darasin da ake koya maka, ko kuma ka ji cewa ba ka sha’awar malamin. Wannan duk suna daga cikin kalubalen da za su yi maka tarnaki ga cimma burinka na koyon karatun. Me ya kamata ke nan ka yi? A nan, ya zama dole ka wanke zuciyarka, ka maida ita tamkar dutse, yadda za ka tursasa ta, ta fuskanci koyarwar gaba-gadi, sannan ka daure wa duk wani ciwo da rashin jin dadin koyon karatun. Bayan haka, sai ka sanya naci da maida hankali. Idan ka kasance haka, sai mafarkinka ya zama gaskiya, sai nasararka ta zama ta bayyana karara.

Daya daga cikin kalubalen rayuwa, wadanda kuma suke kawo cikas ga mai son samun nasarar wani abu, shi ne maganganun mutane. Mafi yawan lokaci, idan mutum ya tunkari yin wani abu, zai ji maganganun mutane daban-daban, wadanda idan ya biye musu, sai su dankwafar masa da niyya, kila ma daga nan ya ce zai watsar da al’amarin. Ke nan sun yi nasarar hana shi cimma wani burinsa na rayuwa. Misali, kana iya cewa, bari in fara kasuwanci. Jin haka sai abokai su fara yi maka dariya, ko su rika yi maka shegantaka, suna cewa ka fi karfin haka da sauran maganganu na karya gwiwa irin wadannan. Kada ka saurare su, kawai ka ci gaba da bibiyar nufinka, bayan wani lokaci, za ka cimma nasara.

Ita nasara fa babu ruwanta da gado, babu ruwanta da cewa babana kaza ne, innata kaza ce, yayana kaza ne. Kowa na iya samun nasara, muddin dai ya bi matakan da suka dace. Kana gani, dan talakka sai ya zama sarki, idan dai ya bi matakan zama sarkin. Kana gani dan attajiri zai tsiyace, idan bai bi matakan zama attajirin ba. Haka kuma dan malami na iya zama kuntukurmin jahili, muddin bai bi matakan da zai samu ilimi ba. Don haka, rayuwa ’yar tashi a nema ce, kuma neman za a yi shi ne ba da sanyin jiki ba. Za a jajirce, sannan a maida hankali, idan da rabo sai nasara ta kawo jiki da kanta.

Bari mu ba da wani misali da zai yi mana ishara da abin da muka fada a sama. Shekaru aru-aru da suka gabata, an samu wani yaro da aka kai shi makaranta. Bayan lokaci sai malamansa suka kore shi, suka aika wa iyayensa takardar da ke cewa yaron nan dakiki ne, shashasha ne, ba zai iya koyon komai ba a rayuwarsa. Mahaifiyar yaron nan ta ji ciwo sosai da karanta wannan takarda. Sai ta jajirce, ta ce, in Allah Ya yarda, sai na koya wa yarona ilimi, kuma sai ya yi nasara a rayuwa.

Haka kuma abin ya kasance, sai ga shi bayan shekaru, yaron da aka ce wai dakiki ne, ya zama haziki, ya zama zakakuri a fannin kimiyya. Kun san ko wane ne wannan? Ba kowa ba ne sai Mista Thomas Edison, wanda shi ne ya fara kirkiro kwan lantarki. Ba wannan kadai ba ma, shi ne ya kirkiro hoto mai motsi, wato kimiyyar da ake amfani da ita wajen shirya fina-finai da shirye-shiryen talabijin. Kafin ya bar duniya kuwa, tarihi ya nuna cewa, ya kirkiro abubuwa masu tarin yawa, wadanda ke amfanar al’umma har zuwa yau din nan, kuma za su ci gaba da amfanar al’umma har zuwa karshen duniya.

Za mu ci gaba

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos