Kada mu yanke kaunar cin nasara a rayuwa (3)

Ga shi yau ma Allah Ya sake kawo mu wani makon kuma za mu ci gaba da kawo maku tambihi game da sinadaran yaukaka rayuwa. Jama’a, ina yi maku sallama, assalamu alaikum. Za mu ci gaba daga inda muka tsaya, a maudu’in da muka faro makonni biyu. Mun tsaya ne daidai lokacin da muke bayar […]

Kada mu yanke kaunar cin nasara a rayuwa (3)

Ga shi yau ma Allah Ya sake kawo mu wani makon kuma za mu ci gaba da kawo maku tambihi game da sinadaran yaukaka rayuwa. Jama’a, ina yi maku sallama, assalamu alaikum. Za mu ci gaba daga inda muka tsaya, a maudu’in da muka faro makonni biyu. Mun tsaya ne daidai lokacin da muke bayar da misali da zakakurin masanin kimiyya, wato Thomas Edison. Mun ga yadda ya ci nasara saboda jajircewa da mayar da hankali, duk kuwa da cewa an kore shi ne daga makaranta. Ga ci gaba:a

Wannan ya nuna mana cewa ba a sanyin jiki da rayuwa. Idan wannan kofar ta rufe maka, ka kwankwasa wata, za ta iya budewa sannan ka shiga ka samo nasara. Irin wannan ta sha faruwa ga mutane daban-daban na fadin duniyar nan, watau ba ga Thomas Edison kadai ba. Haka ma ta taba faruwa ga shahararren mai kera manhajar (fasahar) na’ura mai kwakwalwa. Saboda nasarar da ya samu a rayuwa, ya taba rike kambin mutumin da ya fi kowa kudi a duniyar wannan zamani.

Ina batun Bill Gates ne, wanda shi ma asalinsa korarre ne daga makaranta, amma da yake bai amince rayuwa ta karya shi ba, sai ya maida hankali da kashin kansa, har Allah Ya ba shi sa’a ya samu nasarar rayuwa. A yau kuwa ga shi sunansa ya kai ko’ina cikin duniya.

Bill Gates ya yi ta bincike har Allah Ya ba shi sa’a ya kirkiro manhajar sarrafa kwamfuta, wanda haka ya ba shi damar kafa kamfani na kashin kansa, wanda ya sanya wa suna Microsoft.

Hazikin ya samu nasarar mallakar fasahar nan, ta yadda duk wanda zai yi wata rawar gaban hantsi dangane da kwamfuta, a kan tasa zai dora ko kuma tasa fasahar ta zame wa mutum abin kwaikwayo ko abin nazari.

A lokacin da ya bar makaranta, bai kammala karatunsa ba. Da a ce ya kasance mai matattar zuciya ne shi, da bai samu wannan babbar nasara ba. Da watakila ya bige ga shaye-shayen kayan maye, da kila ya kasance mai yawon gararamba tare da gungun ’yan daba. Idan da a ce wannan rayuwar ya zaba, da babu yadda za a yi ya kasance mai daukaka, da sai dai ya kasance mai cutar da al’umma, ba mai taimakonsu ba.

Don haka, dan uwa, ’yar uwa, za ku iya samun nasarar rayuwa. Mu mike tsaye, mu sanya azama, mu tunkari al’amuranmu da gaskiya. Mu bi dukkan matakan da suka dace, lallai kam bayan duhu, sai mun cin ma haske!

Ta bangaren mulki ma, muna da misali a nan cikin gida Najeriya. Idan muka dauki abin da ya faru a bana, wato yadda Janar Muhammadu Buhari ya samu nasarar lashe zaben shugabancin kasa, shi kansa babban misali ne na yadda jajircewa da naci da gaskiya da amana kan kai ga mutum zuwa ga cikar burinsa.

Duk da cewa ya taba zama Shugaban Kasar Najeriya, daga 1983 zuwa 1985 a matsayin soja, bayan ya aje kaki, ya shiga fafutuka da gwagwarmayar siyasa, inda ya yi takarar wannan kujera a 2003 kuma bai samu nasara ba.

Janar bai gajiya ba, ya ci gaba da gwagwarmaya, ya ci gaba da jajircewa, inda a 2007 ma ya sake kwatawa. Nan ma Allah bai ba shi nasarar cikar burinsa ba. Duk da cewa an samu tabbacin yi masa magudi, ya shigar da kara amma bai samu nasara ba.

A shekarar 2011 ma, ya sake shiga wannan takara kuma ya bi duk matakan da suka kamata, amma Allah bai kadarta ya samu kujerar ba. Naci damben kuturu! Nan ma bai yi kasa a gwiwa ba, domin kuwa ya bibiyi hakkinsa a kotu, amma Allah bai sa an tabbatar masa da kujerar ba.

Daga bisani, a karo na hudu ke nan, Janar din bai hakura ba. Ya shiga takara kuma ya jajirci, ya yi gwagwarmaya, ya yi aiki tukuru. Daga karshe hakarsa ta cin ma ruwa, ya samu nasarar zama Shugaban Kasar Najeriya kuma aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, 2015. Haka kuma ya kara samun nasara a karo na biyu a 2019.

Don haka, duk abin da muke ciki, duk abin da muke nema, kada mu yanke kauna, kada mu karaya, za mu same shi da ikon Allah. Abin da kawai ya kamata mu yi shi ne, mu nemi abin ta hanyar da ta dace, mu jajirce, mu mayar da hankali sannan mu hada da hakuri da naci.

Allah sa mu dace da nasarar rayuwa, amin.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos