Kada sojoji su bari ƙabilanci ya shiga ayyukansu — Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi ya yi wannan roƙo ne a lokacin ƙaddamar da sabon ginin hedikwatar rundunar sojojin Najeriya a Bauchi
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar lll, ya yi kira ga sojojin Nijeriya da kada su bari ƙabilanci ya shiga cikin al’amuransu, yana mai cewa hakan na iya raba kan sojoji da ƙasa baki ɗaya.
Sarkin Musulmi ya yi wannan roƙo ne a lokacin ƙaddamar da sabon ginin hedkwatar rundunar sojojin Najeriya da ke Bauchi a ranar Laraba.
Sarkin Musulmin ya ce, “Yanzu kana aikin soja kuma abubuwa da yawa an tsara su zuwa inda ka fito. Wane ne Musulmi ne? Wane ne Kirista? Wane ne Hausa, Igbo da Bayerabe a ƙasar? Ba mu taɓa sanin waɗannan abubuwa a shekaru da dama da suka gabata ba.
“Ina roƙon kar a bari wannan abu ya kutsa cikin harkokin soja domin hakan zai zama abu ɗaya da zai raba kan sojoji da ma ƙasa.”
Sarkin Musulmi ya kuma gargaɗi ‘yan ƙasar da su daina yi wa jami’an soji mummunan zato wajen gudanar da ayyuka daban-daban domin dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar nan.
Ya ƙara da cewa, “’yan Najeriya na buƙatar bayar da taimako da yi wa sojoji addu’a domin idan babu tsaro ba ma iya barci, ba za mu iya zuwa wurin aikinmu ba har ma da zuwa wuraren ibada.”
A nasa ɓangaren, Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Auwal Mohammed Jatau, ya bayar da tabbacin cewa jihar a shirye take wajen tallafa wa sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.