Kada ya kusa cinye mai kula da shi a gaban ’yan kallo

Da kyar aka ceto ta, amma da karyayyen hannu.

Kada ya kusa cinye mai kula da shi a gaban ’yan kallo

Ma’aikaciyar wani gidan adana namun daji ta tsallake rijiya da baya bayan wani kada da ke gidan ya kai mata farmaki ya kusa hallaka ta a gaban ’yan kallo.

Matar tana cikin yi wa ’yan kallo bayani game da dabbar, kafin a ankara kadan ya kai mata farmaki, ya cafko hannunta da baki, yana kokarin jawo ta zuwa cikin ruwa da aka sanya shi.

Ganin dabbar ta cafko hannun matan yana jan ta zuwa cikin ruwan, sai wani daga cikin ’yan kallo a gidan adana dabbobin na Scale and Tails da ke Utah a kasar Amurka, mai suna Donnie Wiseman, ya yi ta kururuwa cewa, “An samu matsala a nan.”

Daga baya Donnie ya yi ta maza, ya tsallaka ya fada cikin ruwan da dabbar take, sai ma’aikaciyar, wadda dabbar ta rike mata hannu gam tana jan ta, ta rika gaya masa yadda zai yi wa dabbar linzami.

Daga baya wani dan kallo kuma, Todd Christopher, ya rufa wa Donnie baya suka samu suka kwaci mai kula da dabbobin daga bakin kadan bayan ya karairaya mata hannu.

Bayan an fito da ita sai matar Todd mai suna Amy Christopher, wadda ma’aikaciyar jinya ce ta fara ba ta taimakon farko kafin ma’aikatan lafiya su karaso a kai ta asibiti.

Zuwa yanzu dai ma’aikaciyar ta Scales and Tails Utah wadda ba a bayyana sunanta ba “tana samun sauki a asibiti,” inji gidan adana dabbobin.

Hukumar gidan adana dabbobin ta wallafa godiyarta a shafinta na Facebook ga mutanen da suka ceci ma’aikaciyar.

“Muna matukar godiya ga Donnie Wiseman da Todd da kuma Amy Christopher.

“Mun yaba wa jarumtarsu. Tabbasa hulda da irin wadannan dabbobi na da hadari, duk da haka mu ma’aikata muka amince mu yi aikin.”

INEC ta soma tattara sakamakon Zaɓen Gwamnan Edo

Zaɓen Edo: Abin da ya kai ni Ofishin INEC — Obaseki

An kama matan da suka yi yunƙurin sayar da tagwayen jarirai a Legas

Mazauna gaɓar Kogin Benuwe sun soma ƙaurace wa gidajensu