Kada ‘yan kasuwa su bari watan azumi ya shude ba su rabauta ba – Shugaban ‘Yan Gwangwan
An yi kira ga ’yan kasuwa da kada su yi sake watan azumi ya shude ba tare da sun rabauta da falalar da ke cikinsa ba wajen saukaka wa bayin Allah da abin da Allah Ya hore masu. Alhaji Ibrahim Abdullahi Soja Sarkin ’yan gwan-gwan na jihohin Yamma ne ya yi kiran a zantawarsa da […]
An yi kira ga ’yan kasuwa da kada su yi sake watan azumi ya shude ba tare da sun rabauta da falalar da ke cikinsa ba wajen saukaka wa bayin Allah da abin da Allah Ya hore masu.
Alhaji Ibrahim Abdullahi Soja Sarkin ’yan gwan-gwan na jihohin Yamma ne ya yi kiran a zantawarsa da Aminiya a offishinsa da ke Gidan Kwali a Ojota a Legas. Ya ce watan azumi lokaci ne na neman kusanci ga Ubangiji mu ’yan kasuwa ya kamata mu tashi tsaye a wannan lokaci mu gode wa Allah da ya nuna mana wannan lokaci mu yi amfani da wannan dama muyi abin da zamu samu yardar Allah domin bunkasar arzikin mu, ba mu dinga neman tauye bayin Allah ba, idan muka saukaka wa talaka muka rage farashin kayayyakin mu, muka yi sadaka muka fidda zakka, muka taimaki mabukata tabbas Allah zai yaukaka arzikin mu ya bamu nutsuwa da kwanciyar hankali.”
Ya ce, akwai ’yan kasuwar da da zarar watan Ramadan ya kama sai su tsawwala farashin kayayyakin su, wannan ba daidai bane, domin duk mai ko yi da Manzon tsira ba zai yi haka ba, ”Mu sani yadda bamu zo da komai duniya ba haka zamu koma ga Allah bamu da komai don haka muyi kokari mu amfana da wannan lokaci kafin ya wuce ya barmu da cizon yatsa“. In ji shi.
Ya ce, matsalar tsaro da ake ci gaba da fuskanta a Arewacin kasar nan lamari ne da ke bukatar kowa ya bada tashi gudunmawar, bai kamata a ce za a sakar wa gwamnati kadai bane aikin tsaro alhakin kowanen mu ne, don haka mu dage da addu’a ganin mun sami saukin al’amura, ”Wannan lokaci na addu’a ne ga mai da hankali wajen yi wa kasar mu addu’ar samun zaman lafiya, yadda Allah ya amsa addu’ar talaka a baya a yanzu ma zai amsa mana muddun mun kasance muna taimakon junan mu, masu karfi suna taimakon mara sa karfi, muddin muka rike wannan zamu rabauta“. In ji shi.
A karshe Alhaji Ibrahim Soja ya yi kira ga Shugaba Buhari da ya lura sosai wajen zaban sabbin ministocinsa wadanda zasu kama masa aiki yadda ya kamata, ya ce akwai bukatar shugaban kasa ya yi nazari sossai ya zabo mutanen da zasu mara masa baya domin talaka ya amfana.