‘Kada ’yan Tijjaniya da kadiriyya su bar Shaidan ya shiga tsakaninsu’

Shugaban kungiyar Matasan kadiriyya Nasiriyya reshen Jihar Sakkwato kuma daya daga cikin jikokin Shehu Usman dan Fodiyo Malam Mansur Hallaj ya bukaci mabiya darikun Tijjaniyya da kadiriyya a kasar nan da kada su bar Shaidan ya shiga tsakaninsu kan tuntuben harshen da Sheikh dahiru Usman Bauchi ya yi a kwanakkin baya.Malam Mansur Hallaj ya bayyana […]

‘Kada ’yan Tijjaniya da kadiriyya su bar Shaidan ya shiga tsakaninsu’
‘Kada ’yan Tijjaniya da kadiriyya su bar Shaidan ya shiga tsakaninsu’

Shugaban kungiyar Matasan kadiriyya Nasiriyya reshen Jihar Sakkwato kuma daya daga cikin jikokin Shehu Usman dan Fodiyo Malam Mansur Hallaj ya bukaci mabiya darikun Tijjaniyya da kadiriyya a kasar nan da kada su bar Shaidan ya shiga tsakaninsu kan tuntuben harshen da Sheikh dahiru Usman Bauchi ya yi a kwanakkin baya.
Malam Mansur Hallaj ya bayyana haka ne a tattaunawa da Aminiya a Sakkwato don nuna rashin gamsuwa da matakin da ’yan uwansa mabiya darikar kadiriyya suka dauka na mayar da martani ga Sheikh dahiru Bauchi game da kalaman da ya furta kan Mujaddadi dan Fodiyo.
Ya ce, “Mun tabbata Sheikh dahiru Bauchi masoyin Mujaddadi dan Fodiyo ne, kuma da wuya ya fara majalisi ya rufe ba a ji ya fadi gundumawar da Mujaddadi ya bayar ba, ina da ddmbin kasa-kasansa, hasali ma duk shekara a masallacin dan Fodiyo da ke nan yake gabatar da Mauludin Nabiyi, don haka muke rokon mutane su kauce wa tada fitina ko kokarin fitar da aibin dan uwansu, a rika yi wa juna uzuri.”
Ya ce, kada wani dalili da shari’a ba ta yarda da shi ba ya shiga tsakanin masoya waliyyai, ya ce, “Shaidan ne ke kokarin mantar da mu gudunmawar da Sheikh ya bayar ta hanyar nuna mana kuskurensa, don haka nake son mu farga shi ba ma’asumi ba ne, kada mu bari daddadiyar dangantakarmu da ’yan Tijjaniya ta lalace,” inji Halaj.