Kadaitaccen Tunani: Labarin Rayuwa (1)

Ya ku ’yan uwa masu bibiyarmu cikin wannan fili na Sinadarin Rayuwa, ina yi muku sallama, Assalamu alaikum. Kamar yadda muka yi muku alkawari a makon jiya, cewa za mu fara gabatar da sabon littafi mai suna: ‘Kadaitaccen Tunani,’ to da ikon Allah yau za mu fara. Idan ba ku manta ba, maudu’inmu na makon […]

Kadaitaccen Tunani: Labarin Rayuwa (1)
Kadaitaccen Tunani: Labarin Rayuwa (1)

Ya ku ’yan uwa masu bibiyarmu cikin wannan fili na Sinadarin Rayuwa, ina yi muku sallama, Assalamu alaikum. Kamar yadda muka yi muku alkawari a makon jiya, cewa za mu fara gabatar da sabon littafi mai suna: ‘Kadaitaccen Tunani,’ to da ikon Allah yau za mu fara. Idan ba ku manta ba, maudu’inmu na makon jiya, shimfida ce ta warware jigon wannan labari, wanda ya ta’allaka kacokan ga bibiyar al’amuran rayuwarmu na yau da kullum. Idan mun shirya, to bismillah:
Sakamakon Hakuri:
La’asar ce sakaliya, uwargida Dija ta gama Sallah, tana zaune a kan sallayarta daga can kuryar dakinta. Ta gama adadin azkarunta, sai ta samu kanta cikin zuzzrfan tunani. Tunanin nata ya dauke ta zuwa cikin rayuwarta ta can baya da nisa. A bana dai a lissafinta, shekarunta sittin da uku a duniya.
Ta kasance daga lokaci zuwa lokaci, takan samu kanta cikin zuzzurfan tunani irin wannan, musamman idan ta kadaice a natsattsen wuri marar kwaranniya. A irin wadannan lokutan ne take nazari da tariyar abubuwan da suka ratsa cikin rayuwarta. Takan lura da abin da ta samu na natsuwa ko arziki, kamar kuma yadda take lura da abubuwan da suka dugunzuma mata rayuwa, musamman wadanda suka kasance mata kalubale ko jarabawa.
“Alhamdu lillahi!” Abin da ta furta ke nan, bayan ta ja wani gwauron numfashi. Nan ta sake gyara zama bisa dardumarta, domin kuwa yanayin da take ciki a halin yanzu na kadaici, shi ya bijiro mata da wannan tunani, wanda ga dukkan alamu za ta jima ba ta tashi daga shimfidar ba, domin kuwa wannan karon ma ta dauko abin da zurfi.
“Alhamdu lillahi, shukuran kasiran!” Ta kara fadin kalmomin godiya, a yayin da tunaninta ya hasko irin baiwar da Allah Ya yi mata a rayuwa.
“Allah, Ka ba ni zuri’a kuma Ka inganta rayuwarsu. Bello babban dana yana Legas, babban manaja ne shi a babban kamfanin sarrafa roba. Binta kuwa tana Kaduna, baya ga kasancewarta Shugabar Makarantar Sakandaren mata, kuma tana zaune lafiya da mijinta da jikokina. Shi kuwa dan autana, Misbahu, yana Kano, yana aiki a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.
“A kullum ban rasa ci, ban rasa sha, ban rasa suturar daurawa, kamar kuma yadda ga ni a cikin yalwatacce kuma wadataccen muhalli. ’Ya’yana sun tanadar mani da komai, musamman har da barori uku masu yi mani hidima a kullum rana ta lillahi. Sun daukar mani hadima, mai yi mani abinci da share-sharen gida. Ina da mutumin da suka dauka aikin gadi da tsaron al’amuran gidana, kamar kuma yadda suka saya mani mota, tare da daukar direba da ke yi mani kowace zirga-zirga.
“Duk da kasancewar na tsufa, amma ’ya’yana ba su kyale ni haka nan ba, sai da suka daukar mani malamar addinin Musulunci; wacce take zuwa nan har gida tana koya mani karatu, take fayyace mani dalla-dalla na abin da ke ibada. Sun kai ni Makka na sauke farali, baya ga cewa duk shekara sai na je aikin Umrah.
“Na kasance cikin daula, na kasance cikin natsuwa da farin ciki, na kasance cikin zumuncin ’yan uwa da abokan arziki. Gidana ya kasance gidan kowa, domin kuwa daga abin da ’ya’yana suke ba ni, nakan ci na raba wa ’yan uwana na jini, kamar kuma yadda nake raba wa fakirai na nesa da na kusa, wato makwabtana.
“Wannan rayuwa tawa, Alhamdu lillahi!” Dija dai ta ci gaba da nazari, tare da yaba wa yanayin rayuwarta.
“Masu iya magana sun ce, kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba. To ni da na tuna bana, me hakan ke nufi ke nan?” Dija ta tambayi kanta da kanta.
“Babu shakka na ratso yanayin lokaci iri-iri. Na ratso abin da ake kira wulakantaccen yanayi, na ratso rayuwar kunci da talauci; na ratso yanayi na cin mutunci da tozarci.” Idanuwanta sun cika da kwalla. Ta cije lebe lokacin da ta hasko wani duhun wulakanci da ya taba turnuke mata rayuwa, lokacin tana ’yar shekara ashirin a duniya, lokacin ba ta dade da haihuwar fari ba a gidan mijinta.
“A da ni da na kasance bora a gidan duniya, amma yau ni ce ’yar mowa a gaban ’ya’yana da jikokina. A da lokacin da na zama tattaka, marar kima a idon mijina da kishiyoyina, sai ga shi a yau na zama sarauniya abar alfahari ga ’yan uwana da makwabtana. A yayin da shekaru talatin da wani abu da suka wuce na zama tsumma abin share datti, sai ga shi yanzu na zama farin alharini mai kamshin almuski a idanun al’umma.”
“Alhamdu lillahi!” Dija ta kara hasko yadda rayuwarta ta samu gagarumin canji daga baka zuwa fara, daga wahala da kunci zuwa yalwa da sawaba.
“Yanzu ne ma na kara tabbatar da gaskiyar ’yan karin maganar Hausa da suka ce mahakurci mawadaci, kamar kuma yadda suka ce mai hakuri ne ke dafa dutse kuma har ya sha romonsa. Na kuma taba jin masu hikima suna cewa, duk wanda bai ci ribar hakuri ba, to kadan ya yi.” Inji ta cikin alhini, a yayin da hawaye ke kwarara daga idanuwanta. Dija ta sanya habar zane ta share hawayen, sannan ta samu kanta cikin wani sabon tunanin. “Masu magana sun ce, kowa ya ci zomo ya ci gudu. Shin yaya rayuwata ta kasance a baya, kafin in cin ma wannan zango na nasara a rayuwa?” Ta tambayi kanta, a yayin da kuma ta sake nutsa cikin tunanin rayuwarta ta baya.
Za mu ci gaba