Kadaitaccen Tunani: Labarin Rayuwa (5)

A makon jiya, mun jingine labarin nan da nufin bayar da filin don tambihi game da sabuwar shekarar Musulunci. Yau kuma za mu ci gba daga inda muka tsaya a wannan labari mai taken: Sakamakon Hakuri. A can baya dai, mun tsaya inda Dija ta gana da mahaifinta saboda matsalolin da take fuskanta a gidan […]

Kadaitaccen Tunani: Labarin Rayuwa (5)
Kadaitaccen Tunani: Labarin Rayuwa (5)

A makon jiya, mun jingine labarin nan da nufin bayar da filin don tambihi game da sabuwar shekarar Musulunci. Yau kuma za mu ci gba daga inda muka tsaya a wannan labari mai taken: Sakamakon Hakuri. A can baya dai, mun tsaya inda Dija ta gana da mahaifinta saboda matsalolin da take fuskanta a gidan nmijinta. Shi kuwa mahaifin nata, ya ba ta hakuri ne, sannan ya yi mata hudubobi masu ratsa zukata. Yanzu kuma za mu ci gaba:

***
Har yanzu dai Dija ba ta bar kan sallayarta ba, ta sake nutsawa cikin kogin tunani, na yadda rayuwarta ta kasance, musamman yadda ta yi rayuwa cikin gwagwarmaya tsakanin bakin ciki zuwa farin ciki. Ta tuno wata rana da mjinta ya kasance wulakantacce, wanda ya zubar da duk wata kima da daraja da Allah Ya yi masa.
Wata rana ce ma mijin nata ya dauki albashi, amma tun da ya fita da safe, ba ta kara ganinsa ba sai bayan kwana uku. A lokacin da ya bar gida, ta tuno da cewa babu ko kwayar hatsi a gidansu. A lokacin nan, duk gidan, daga ita har ’ya’yanta babu wanda ya karya, alhali da dare ma haka suka kwanta ba tare da sun ci abinci ba. Hana rantsuwa, makwabtansu sun aiko musu da kwano daya na tuwo, wanda ita Dija ta yi loma daya, ta mika wa yaranta sauran, suka cinye, duk da cewa ba su koshi ba. Haka nan suka kwanta har zuwa safiya.
Dija ta tuna da yadda gidansu ya wayi gari, babu abin kari, yara za su tafi makaranta babu ko kwabon da za ta ba su. Haka mijinta ya shura takalminsa ya fice daga gidan, ganin da ba ta kara yi masa ba sai bayan kwanaki uku. Ba wai ganin nasa ne ma ta yi haka nan ba, a’a, ta gamu da bakin ciki da takaici, domin kuwa ba da kafafunsa, kamar yadda ya fita gidansa ya dawo ba, wannan karon, kwaso shi aka yi kamar tsumma, aka dawo da shi gida.
Mijin nata, rai a hannun Allah aka kawo mata shi, kansa a fashe cikin jini, yana nishi daidai. Jikinsa ya yi futu-futu da kura, rigarsa a yage, wandonsa rabi a wangale, sai wari da tsamin giya yake, a yayin da bakinsa ke fitar da wata kumfa mai doyi da hamami.
Kamar yadda Dija ta samu cikakken bayani, bayan mijin nata ya amshi kudin albashinsa, babu inda ya zame sai gidan giya. Ba shi kadai ya tafi ba, sai da ya biya wani gidan karuwai, inda dama ya aje wata karuwa da suke yin dadaro. Tare da karuwar suka tafi gidan giyar nan. A teburin da suka zauna, babu wanda ke sayen giya sai shi. Maza da mata, kusan mutum shida ne a teburin, amma tun da suka zauna da misalin karfe uku na rana, sai da gari ya waye musu suna aiki daya. Shan giya, rawa da kuma surutai da sunan hira, abin da suka yi ta yi ke nan. Jefi-jefi kuma, sun rika yin gardandami, har ta kai ga wasu cikinsu suna fada da juna.
An sake shaida wa Dija cewa, a gidan giyar ne aka lakada wa mijin nata duka, aka yi masa ligi-ligi. ’Yan kwarmato sun bayyana mata cewa, wata karuwa ce ta zo teburin da mijinta ke zaune, ta nuna cewa shi take so, duk da cewa akwai farkarsa zaune kusa da shi. Farkar tasa ce ta fara nuna adawa da kishi, ta zo ta cakume ta, suka rukume da fada. Mijin nata ya shiga tsakani amma farkarsa ta ki amincewa, dalilin da ya sanya shi kuma ya goyi bayan ita bakuwar, har ma ya zaunar da ita, ya saya mata giya suna sha.
Ganin haka ya sanya ita kuma farkarsa ta tashi daga teburin nasa, ta koma wani, inda ita ma ta samu wani manemin na daban. A daren ne al’amura suka cakude, aka samu gagarumin fada a tsakanin teburan biyu. A nan ne fa aka yi wa mijin Dija ligi-ligi, ya kwana a cikin jini, tsakankanin teburan giya.
Ta tuno sarai, irin bakin ciki da takaicin da ta shiga, a lokacin da aka zubar da mijinta a kofar zauren gidansa, yana nishi daidai. Yara kuwa suka baibaye shi a kofar gida, suna ta cewa: “Ya sha kafso, ya yi marisa. Ya sha giya, ya yi marisa!” Da kyar da jibin goshi Dija ta tallabe shi ta shige da shi gida, ta kulle kofar zauren.
A daidai lokacin nan, ba ta da ko sisin kwabo, rishonta babu kananzir, balle ta dafa ruwan da za ta gyara masa jikinsa. ’Ya’yanta kuma ba su dade da dawowa daga makaranta ba, ga shi kuma babu wani abincin da za su ci. Cikin hikima ta tura su gidan kakanninsu domin su samu abin da za su ci. Ita kuma ta zo kan mijinta tana rusa kuka, ta rasa abin da za ta yi.
“Dija, Allah na jaraba kowane mumini ta hanyoyi daban-daban. Idan an jarabi wani ta hanyar talauci, wani ta hanyar dukiya za a jaraba shi. Idan an jarabi wani da samun farin ciki, wani kuma da bakin ciki ake jarabtarsa. Ki dauki rayuwar mijinki a matsayin wata hanya ce da Allah Ya kawo maki domin jarabawa. A matsayinki na mace, wannan babban kalubale ne da ya hau kanki. Ina ba ki shawara da ki maida hankali wajen nemo hikimomi da dabarun yadda za ki shawo kan mijinki domin ya canja halayensa. Ki samu kanki a matsayin malamar jinya, mai koya tarbiyya. Ki sanya wa zuciyarki juriya da hakurin yi wa mijinki huduba da nasiha domin ya dawo kan hanya. Dole sai kin hada da hakuri da addu’a da neman taimakon Allah. Ba aiki ne na rana daya ko biyu ba kuma ba gajiyawa za ki yi ba, sai kin matsa kaimi, ba dare balle rana.”
Wannan huduba ta mahaifinta ce ta fado mata a rai, dalilin da ya sanya ta daina kuka, ta tashi tsaye domin neman yadda za ta kintsa jikin mijinta.
Za mu ci gaba