Kadaitaccen Tunani: Labarin Rayuwa (6)
A yau ma za mu ci gba daga inda muka tsaya a wannan labari mai taken: Sakamakon Hakuri. A can baya dai, mun tsaya inda Dija ta kuduri aniyar kintsa mijinta, bayan da aka kawo shi gida cikin mummunan yanayi, rai a hannun Allah: Wannan kyakkyawar huduba da mahaifinta ya taba yi mata, ita ce […]
A yau ma za mu ci gba daga inda muka tsaya a wannan labari mai taken: Sakamakon Hakuri. A can baya dai, mun tsaya inda Dija ta kuduri aniyar kintsa mijinta, bayan da aka kawo shi gida cikin mummunan yanayi, rai a hannun Allah:
Wannan kyakkyawar huduba da mahaifinta ya taba yi mata, ita ce ta sanya Dija ta kori shaidan daga zuciyarta, ta ci damarar kintsa mijinta. Kasancewar babu makamashin da za ta dafa ruwan zafi, sai ta shiga makwabta, ta roke su itacen girki, koda kirare ne.
Dija ta tuno yadda ta samo busasshen kara da wani barbashin gawayi daga gidan makwabta. Da su ne ta takarkara ta dafa ruwan zafi a karamar tukunya, ta tube kayan mijinta, ta yi masa wanka. Duk inda jikinsa ya farfashe ko ya kumbura, ta wanke shi tas. Ta samo man kadanya ta shafe jikin nasa da shi, a yayin da ta samu garin kwalli ta like gurbin da ke zubar jini a kansa. A yayin da ta zo wanke wurin ciwon nan na kansa, sai da ta ci karo da birbishin fasassar kwalba. Alamar da ke nuna cewa kwalbar giya ce aka fasa masa a kai.
A daidai lokacin da ta kawo nan da tunaninta, sai Dija ta samu kanta cikin hawaye. Ba karamin kuka ta yi ba, domin kuwa carbin da ke hannunta sai da ya jike sharkaf da hawaye. Ta tuno yadda mijinta ya zabi ya wulakanta kansa, inda ya mayar da kansa marar gata, duk kuwa da cewa shi mai gata ne. Ta tuno yadda ya kaskantar da kansa, duk kuwa da cewa shi mai muhibba ne. Ta yi la’akari da yadda mijinta ya zama tijararre, fitsararren dan giya, mazinaci, duk kuwa da cewa yana da ilimin addini da na zamani.
Wannan takaici da ta tuno, duk da cewa yanzu abin ya zame mata tarihi, amma bai hana ta zubar da hawaye ba. A kan haka ne ma sai ta samu kanta cikin wani murmushi, wanda ya haskaka fuskarta, ta zama mai annuri. Murmushin nata ya kara bayyana, a yayin da hakoranta suka fito wangalai kamar wani gululun audugar da ke fitar da sabuwar kada. Babban abin da ya bijiro mata da farin ciki, bayan bakin cikin da ta tuno, shi ne yadda ta bi hanyoyin hikima da basira ta canja yanayin mijinta. Daga fandararre zuwa mikakke, daga karkataccen gora mai wuyar fafa zuwa nagartaccen gora mai kyan siffa. Ta tuno yadda, tare da taimakon iyayenta da taimakon Allah, ta samu canja halayen mijinta, inda ya watsar da fajirci ya rungumi aikin Allah, ya watsar da giya da tambele, ya rungumi aikinsa na neman halal.
Dija ta tuno da cewa lallai ba ta samu haka da sauki ba, domin kuwa sai da ta ci bakar wahala. Sai da ta jajirce, ta daure da kaskanci da wulakanci, sannan ta samu sa’ida a gidan mijinta. “Lallai karin maganar Hausawa gaskiya ne.” Abin da ta furta ke nan a lokacin da ta muskuta kugu, ta gyara zama a kan sallayar tata. “Da suka ce, kowa ya ci zomo ya ci gudu.”
A ci gaba da tunaninta, ta hasko yadda mijinta ya murmure daga wannan abin takaici da ya same shi a gidan giya. Lokacin da ya farfado, babu abin da ya fara furtawa sai sunan farkarsa. “Inno, Inno…” Inji shi. “Don kutumar ubanki miko mani kwalbata in tsotsa!”
“Haba Baban Bello, ba ka ganin yanayin da kake ciki kake kunduma ashar haka?” Dija ta fada masa haka cikin takaici. Kuma, nan gidanka ne, ni matarka ce ta sunna, ba Inno ba ce, wacce ta yi sanadiyyar saka ka cikin wannan wulakanci.”
A lokacin ne fa Baban Bello ya yi firgigi zai tashi daga kwance, sai ya samu jikinsa da nauyi. Ya shafa kansa sai ya ji zafin raunin da ke kansa. Haka kuma sai ya ji wata irin yunwa ta murde masa ciki. Kai kuwa rabonsa da hatsi kwana uku ke nan. Duk tsawon kwanakin nan, babu abin da yake kwankwada sai barasa, wadda har ta kai ga ya shiga wannan yanayi na rai-kwakwai-mutu-kwakwai. Ya bude ido sarai sai ya gane cewa ashe a gidansa yake, tare da matarsa Dija.
“Dija, me ya faru da ni ne don Allah?” Tambayar da ya yi wa matarsa ke nan, a lokacin da ya dawo cikin hayyacinsa. “Wash! Wallahi kaina ya yi nauyi, jikina duk ya yi tsami, ga shi ina jin bala’in yunwa. Babu wani abinci nan kusa?”
Dija ta kalle shi, yayin da wani gululun bakin ciki ya cika ta. Ta tuno da cewa babu komai na cimaka a gidan nan, don haka ta rasa ma me za ta fada masa. Ba ta kai ga ba shi amsa ba, sai ta ji sallamar yara sun dawo daga gidan kakanninsu, inda ta tura su dazu, bayan sun dawo daga makaranta. Yaran ne ma suka dawo da kwanon abinci, tuwon dawa miyar kuka. Sannan a daya kwanon kuma da kan dawo mai girma, tare da nono kulle a leda.
Nan da nan Dija ta amshi abincin nan, ta mika wa mijinta. Duk da cewa tana jin yunwa ita ma, amma ba ta koma kan bukatarta ba. Sai da mijinta ya cinye abincin nan, bai rage komai ba sai abin da bai gaza loma uku ba. Daga bisani ta amsa ta cinye, ta sude kwanon.
Ba ta huta ba, sai ta dama furar nan, ta tsiyayi ’yar kadan, ta tura masa sauran. Nan fa ya kafa kai ya kwankwade ta. Bayan ya gama ya yi doguwar ajiyar zuciya, sannan wata gyatsa ta biyo baya.
“Dija, na gode, Allah shi maki albarka. Don Allah me ya faru da ni?” Inji shi.