Kadaitaccen Tunani: Labarin Rayuwa (7)
A yau ma za mu ci gaba daga inda muka tsaya a wannan labari mai taken: Sakamakon Hakuri. A can baya dai, mun tsaya inda Dija ta kammala kintsa mijinta, bayan da ya farfado har ta ba shi abinci ya koshi. Bayan ya murmure ne ya yi wa matarsa godiya, sannan ya tambaye ta abin […]
A yau ma za mu ci gaba daga inda muka tsaya a wannan labari mai taken: Sakamakon Hakuri. A can baya dai, mun tsaya inda Dija ta kammala kintsa mijinta, bayan da ya farfado har ta ba shi abinci ya koshi. Bayan ya murmure ne ya yi wa matarsa godiya, sannan ya tambaye ta abin da ya faru da shi. Ga ci gaba:
“Dija, na gode, Allah shi maki albarka. Don Allah me ya faru da ni?” Inji shi.
Maimakon ta ba shi amsa, Dija sai ta samu kanta cikin wani bakin ciki marar iyaka. Takaici ya yi ta kai-kawo a ranta, zuciyarta ta yi ta tafarfasa. Kawai sai wani zazzafan hawaye ya rika gudana daga idanuwanta, ta rasa kalmomin da za ta furta wata magana ga mijinta.
“Me ya faru kuma da ke, kike kuka haka? Don Allah ki yi mani magana, na ce me ya faru?”
Ganin yadda ya matsa mata da tambayoyi, tare da la’akari da yanayin da yake ciki sai Dija ta samu karfin halin danne bakin cikin da ke tokare mata zuciya, wanda kuma shi ne ya haddasa mata zubar da hawaye. “Yanzu don Allah Baban Bello haka za mu ci gaba da rayuwa a duniyar nan? Haka za ka ci gaba da zama cikin fajirci da kaskanci a gaban iyalinka da iyaye?” Ta kara barkewa da kuka, wannan karon ba hawaye kadai ba, har da sauti tare da shessheka.
Baban Bello bai kara samun bakin magana ba, sai ya dukar da kai kawai cikin alamar kunya da nadama.
“Ka duba ka ga, Allah Ya yi maka sutura, ka zabi ka zauna cikin tsiraici. Allah Ya ba ka ilimi, na addini da na zamani amma ka zabi ka yi rayuwar jahilci. Allah Ya ba ka iyaye nagari, wadanda suka koya maka tarbiyya takwarai, amma ka zabi ka yi rayuwar fajirci da bata gari. Allah Ya ba ka rufin asiri, kana da aiki mai daraja amma ka zabi ka yi rayuwa irin ta asharari da tambada. Ka duba yadda ka mayar da kanka dan giya, mai neman matan banza. Ka duba yadda ka banzatar da mu iyalanka. Abinci da sutura sun gagare mu. Shin da wane ido kake so ni matarka in rika kallonka da shi? Me kake so ’ya’yanka su dauke ka kuma da wace kama kake son sauran mutanen gari su rika kallon mu?”
“Ni dai ki bar wannan maganar, na tambaye ki cewa me ya faru da ni haka, na samu kaina cikin ciwo da galabaita.”
“Wadannan bayanai da na yi maka, su ne amsar da ta kamace ka. Shin kai ba ka tsinci amsar tambayarka daga wadannan bayanai nawa ba? Me kuma kake so in kara gaya maka?” Dija ta fada masa haka cikin wata zuciya dakakkiya.
Ta ci gaba da bayyana masa labarin abin da ya same shi, kamar yadda ita ma aka ba ta labari. “Nan aka kawo ka hajaran-majaran cikin dattin giya da kai a fashe cikin jini. Ba ka ma san inda kake ba, domin kuwa a some kake. Idan da za a hasko maka hoton yadda yara suka baibaye kofar gidan nan, da takaici ya ishe ka. Yara sun yi dandazo suna yi maka wakar tsokana, cewa kai dan giya ne kuma dan kwaya.”
Ta kara fashewada kuma, a yayin da ta sanya habar zane tana share hawaye. “A daidai lokacin ne fa yaran nan namu suka dawo daga makaranta cikin yunwa. Babu abin da suka iske sai mahaifinsu cikin wulakanci da kaskanci, a yayin da abokansu suna yi masa tijara. Ko abin da za su ci babu a gidan nan, ka kwashe ka kai wa karuwai da masu giya. A dole na tura su gidansu mama, inda can suka samo mana wannan abincin da ka ci da furar da ka gama sha yanzu. Don Allah ka natsu da ranka ka duba irin wannan al’amari – haka kake son mu ci gaba da rayuwa?”
Haka ta tasa shi gaba, ta yi ta ba shi magana da jan hankali, inda shi kuma ya rasa abin da zai gaya mata mai ma’ana.
“Yanzu dai wannan abu duk ya wuce, tun da dai ya faru kuma ba zai dawo ba.” Inji shi. “Ina tabbatar maki da cewa zan gyara. Ni kaina ban san abin da ya same ni ba.”
“Bai yiwuwa ka ce ba ka san abin da ya same ka ba.” Inji Dija cikin harzukakkar murya. “Ai kana da hankali, kana da tunani, kana da ilimi. Ka san baki kuma ka san fari, kamar yadda ka san yunwa kuma ka san koshi. To yaya za a yi ka saka kanka cikin halaka, sannan kuma ka ce ba ka san abin da ya same ka ba? Idan dai za ka canza, dole ne ka canza rayuwarka yanzu, domin babu sauran lokacin tambele a yanzu.”
Da haka dai suka rufe al’amarinsu na ranar nan. Bayan ta gyara masa shimfidarsa, ta tallafa masa ya shiga daki. Bai samu lokaci mai tsawo ba sai barci ya share shi. Ita kuwa Dija sai da ta samu tsawon lokaci ba tare da ta yi barcin ba. Ta tsaya ne tana ta nazarin rayuwarta da yanayin da ta samu kanta a ciki. Ba ta san lokacin da barci ya sace ta ba, sai dai farkawa ta yi ta ga gari ya waye.
Za mu ci gaba