Kadaitaccen Tunani: Labarin Rayuwa (8)
A yau ma za mu ci gaba daga inda muka tsaya a wannan labari mai taken: Sakamakon Hakuri. A can baya dai, mun tsaya inda Dija da mijinta Baban Bello suka kammala tattaunawa, inda har shi ya yi barci, ya bar ta tana ta tunani; inda daga bisani kuma har barci ya dauke ta ita […]
A yau ma za mu ci gaba daga inda muka tsaya a wannan labari mai taken: Sakamakon Hakuri. A can baya dai, mun tsaya inda Dija da mijinta Baban Bello suka kammala tattaunawa, inda har shi ya yi barci, ya bar ta tana ta tunani; inda daga bisani kuma har barci ya dauke ta ita ma, ba tare da ta sani ba. Ga ci gaba:
Kafin ta kai ga yin barci, Dija da ta ga tunanin nata ya yi nisa, sai ta ga cewa ya kamata ta karanta wani dan labari da ta gani a cikin wani dan karamin littafi da danta ya ce an raba masu a makaranta. Labarin ya daukar mata hankali ne, musamman saboda darussan rayuwa da suke kunshe cikinsa. Ga yadda labarin yake:
Wani Farfesa ne ya amshi bakuncin wasu tsofaffin dalibansa da ya koyar can a baya, a yayin da shi kuma har yanzu yake koyarwa a wannan hamshakiyar jami’a a matsayin babban malami. daliban nan dai sun samu nasara a sassa daban-daban na rayuwa. Wasu sun kasance hamshakan ma’aikata a gwamnati, wasu a bankuna, wasu a manyan kamfanoni. Wasu kuwa sun kasance hamshakan attajirai, a sanadiyyar kasuwancin zamani.
Bayan sun zauna har ma sun fara tattauna al’amura daban-daban, ciki har da abubuwan da suka faru tun can baya suna makaranta, har zuwa al’amuran da ke kan faruwa a kasa yanzu. Daga bisani ma sai suka maida bayaninsu game da al’amarin rayuwa, musamman ma abin da ya danganci mallakar dukiya da tafiyar da rayuwa mai tsada da sauransu.
Ana cikin hira, sai Farfesa ya ce bari ya kawo shayi domin sanyaya makogwaro. Lokacin da aka gabatar da shayin, sai kuma suka ga Farfesan nan ya zo da kofuna iri-iri a cikin kwando. Wasu kofunan na roba ne, wasu na karau, wasu masu tsada ne sosai, wasu kuma masu araha. Wasu kofunan duk sun kode kuma sun tsufa, a yayin da wasu kofunan kuwa sababbi ne, sai sheki suke tare da daukar ido, gwanin ban sha’awa.
Bayan an zuba shayi a dukkan kofunan nan, bayan kowane bako ya dauka, sai Farfesa ya fara magana. Ya ce: “Ina son kowa daga cikinku ya kalli kofin da yake hannunsa. Idan kun lura kowannenku ya yi kokari ya dauki kofi mai kyau kuma mai kyalli, mai tsada. Idan kun duba cikin kwandon da aka aje kofunan, kun bar tsofaffi, wadanda suka kode, kun bar kofunan roba, masu araha, ba ku dauka ba. Idan kun lura, kun dauki kofuna masu kyau da tsada ne, domin kowa yana son ya mallaki abu mai kyau ga kansa. Babu wani mutum da yake son abu mara kyau, babu wanda ke son a ce abinsa bai da kima da daraja. Kun san wani abu? Wannan tunanin kuma shi ne tushen matsalar mutane, shi ne ke haifar mana da cikas a kowane fanni na rayuwa.
“Ku saurare ni ku ji wani abu. Idan kuka kalli kofunan da suke hannuwanku, ko kun san cewa duk da tsadarsu, duk da kyawunsu ba su kara komai ga ruwan shayin da ke cikinsu? Kawai dai su kofunan sun kasance masu tsada, amma abin da muka fi so shi ne ruwan shayin da suke dauke da shi, domin kuwa komai tsada da kyan kofin, ba zai yi mana maganin kishi ba, ba zai biya mana bukata ba, amma ruwan shayin da ke cikinsa, shi ne zai ba mu wannan abu da muke bukata. Amma idan kun lura, a lokacin da kuka je daukar kofi, sai kuka yi ta rububin ku dauki kofi mai tsada kuma wanda ya fi kyau. Kowa na kokari ya dauki wanda ya fi na dan uwansa kyau. Kowa na kallon kofin da dan uwansa ya dauka, don ya ga shin ya kai nasa kyau da tsada, ko kuwa nasa ya fi nasa?”
Ya dan saurara, daliban nan kuwa suka yi ta kai-kawo da tunanin darasin da Farfesansu ke son bayyana masu. Kowa ya maida hankali ga kofin da yake rike da shi, sannan kuma suka koma suna kallon sauran kofunan da ke cikin kwando, wadanda suka rage ba a dauka ba.
“Yanzu sai ku kara saurarawa, domin ku ga tasirin abin da nake son bayyana maku.” Inji Farfesa. Ya ci gaba da bayaninsa da cewa: “Rayuwa dukkanta, ita ce ruwan shayin nan da ke cikin kofunan da kuke rike da su. Kun san wani abu kuma? Wadannan kofunan da kuke rike da su, su ne a matsayin gidajen kwananku, motocin shigarku, kudin da kuke ajewa a bankuna da sauran tarkace daban-daban. Ke nan a rayuwarku, wadannan tarkace, sunansu tarkace kawai, kayan aiki ne kawai na rayuwa. Wato su ne dai kawai suke tallafa wa rayuwa, domin ta gudana. Idan kun lura, ruwan shayin da ke cikin sabon kofi, irinsa ne dai a cikin tsohon kofi. Ruwan shayin da ke cikin kofi mai tsada, irinsa ne dai a cikin kofi mai araha, kuma dandano iri daya zai ba ku, kuma amfani iri daya zai amfana maku. Da kai da ka dauki tsohon kofi, da wancan da ya dauki tsoho; da wacan da ya dauki kodadde, shi kuma wannan da ya dauki mai kyalli, ba kofunan ne za su amfane ku ba, a’a, ruwan shayin ne zai gamsar da ku, kuma dandanonsa ko ingancinsa ba zai canza, don an zuba shi a tsohon kofi ko kodadde ba.
“Idan mun lura da rayuwa, muna ba abubuwa marasa muhimmanci kima, fiye da masu muhimmanci. Lallai ne mu kula da rayuwa, mu gane cewa za ka iya jin dadin rayuwa da abubuwa masu sauki da araha, domin bukatar dara dai kasawa.”
Dija tana gama karanta wannan labari, kafin ka ce wani abu, barci ma ya gama kwashe ta.
Za mu ci gaba