Kadan ne daga cikin malaman addini suke fada wa gwamnati gaskiya
daya daga cikin masu fafutikar tabbatar da adalci a tsakanin al’umma kuma Shugaban kungiyar Masu Maganin Gargajiya a Shiyyar Bauchi ta Kudu Alhaji Gambo Abdullahi Bababa, ya ce nuna damuwa kan yadda wadansu daga cikin malaman addini a Jihar Bauchi suka yi gum da bakinsu ba sa iya fada wa gwamnati gaskiyar halin da jama’a […]
daya daga cikin masu fafutikar tabbatar da adalci a tsakanin al’umma kuma Shugaban kungiyar Masu Maganin Gargajiya a Shiyyar Bauchi ta Kudu Alhaji Gambo Abdullahi Bababa, ya ce nuna damuwa kan yadda wadansu daga cikin malaman addini a Jihar Bauchi suka yi gum da bakinsu ba sa iya fada wa gwamnati gaskiyar halin da jama’a suke ciki, musamman kan rashin biyan albashi da fansho.
Alhaji Gambo Bababa ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Bauchi, inda ya ce ya kamata gwamnatin jihar ta biya ma’aikata da ’yan famsho albashi da hakkokinsu saboda rashin biyan ya gurgunta harkokin kasuwanci da rayuwa a jihar.
“Kowa ya san jihar nan ta dogara da albashi ne kuma duk lokacin da gwamnati ta gaza biyan ma’aikata hakkokinsu matsalar takan shafi kowa. Malaman addini su ne magada annabawa, amma abin kunya wadansu daga cikinsu sun koma ’yan amshin shatan gwamnati ba sa iya fada mata gaskiyar halin da ake ciki. Saboda haka muna ba da shawara gwamnati ta yi maza ta biya ma’aikata hakkokinsu kafin su fara yi mata munanan addu’o’i,” inji shi.
Ya kalubalnci gwamnatin jihar ta fada wa talakawa kudin da take samu daga Asusun Tarayya duk wata da yadda take kashe su.