kadangare mai kai biyu da kafafu shida ya bayyana a Thailand

A cikin makon da ya gabata ne mutanen garin Phuket da ke kasarThailand suka ga abin mamaki yayin da suka gano wani kadangare mai kai  biyu da kafafu shida.Bincike ya nuna cewa an gano kadangaren ne a cikin wani gida jim kadan bayan wata kadangaruwa ta haife shi. Wadanda suka ga kadangaren sun bayyana cewa […]

kadangare mai kai biyu da kafafu shida ya bayyana a Thailand

?????????????????????????????????????????????????????????

A cikin makon da ya gabata ne mutanen garin Phuket da ke kasarThailand suka ga abin mamaki yayin da suka gano wani kadangare mai kai  biyu da kafafu shida.
Bincike ya nuna cewa an gano kadangaren ne a cikin wani gida jim kadan bayan wata kadangaruwa ta haife shi. Wadanda suka ga kadangaren sun bayyana cewa sun ga burbushin kwan da ya fito daga ciki a jikinsa kuma ya kai girmai dan yatsan karamin yaro.
Dakta Sansareeya Wangkulangkul, farfesa a bangaren halittu a jami’ar garin Songkhla da ke kasar Thailand ya ce kadangaren yana da wata halitta ta musamman da ta sha bamban da sauran kadangaru irin sa. Ya ce ‘Wannan abin mamaki ne da ba a saba gani ba mafiyawan kadangaru ba sa wuce shekara daya a raye amma shi wannan ba ni da tabbaci a kansa saboda yana da nakasa. Sai dai mai shi ya yi kokarin ciyar da shi da bakar tururuwa ko kuwa da kananan tsutsosi. Ina so jama’a su sani cewa wannan ba shi ne kadangare na farko da aka samu da kai biyu ba an taba samu a wasu kasashe da nahiyoyin duniya daban-daban.’